← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 146

Sashe 140

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani littafine a hannun Abla gabaki d’aya rabun tunaninta yana kansa sabida yadda ta mayar da hankali akai , bata ankara ba taji an fuske Book d’in, cikin sauri ta d’ago da dara daran eyes dinta tana hararar Fanan ,� Kin fiya rigima fanan , bani book d’ina � cikin tsokana fanan da ke bud’e Book din ta furta � wallahi bazan baki ba , ki bari sai antashi wannan nasan tabbas zan iya baki , amma gabaki d’aya tun d’azu muna magana ke hankalin ki yana kan Book � shiru Abla tayi tana ‘kara hararar ta , kallan yadda ta ‘bata face Eshaal tayi kafin ta kalli fanan itama � kinsan Allah fanan ki fita idan mu, ina ruwanki da littafinta ? Kun bi kun ishemu da surutu salan kusa mana ciwan kai � kallan Baby fanan tayi � kinji fa ! Mu zasu yi wa bariki waisu best friend , ki fad’a musu mu a ‘kawancen namu ma , mu indiyawa ne � gabaki d’ayan su kuma sai suka ‘kyal’kyale da dariya sabida jin abinda fanan tace , � ke dai fanan kin shiga uku da surutu zanga yadda mujin ki zai yi fama dake � cewar Baby, da sauri fanan ta mi’ke tsaye tana toshe kunnuwan ta � Ni bana jin hausa da safe , kunga yanzu time zai wuce , ko kuma a hanyar komawarmu muga an shiga class � cikin tsokana Eshaal ta furta � zakiyi bayani ne ma ! Mu zakiyi wa wayo ? Amma dont worry akwai lokacin da zakiyi bayani� da haka suka mi’ke zasu koma class , kamar ance wa Baby ta juya sai taga flowers suna motsi kamar an bangaje su an wuce ta wajan , gashi gabaki d’aya su kad’ai a wajan flowers d’in � Me kike nema ?� Cewar Abla ganin yadda Baby take zare ido , d’an jijjiga mata kai Baby tayi � No babu komai , mu tafi� kanta Abla ta d’aga mata kafun ta furta � Okay � a haka suka nufi hanyar class kwajin burgewa suna tafiya suna hira abinsu , a karo na biyu Baby ta ‘kara tsayawa jin kamar anta’ba mata hannu, tana kallan side d’in kuma taga babu kowa a wajan � Lapiya ?� Suka had’a baki a wannan karan, waigawa Baby ta soma yi lokaci zuwa lokaci kuma tana kallan hannun ta da kuma wajan flowers d’in da suka bari � ji nake bayan mu akwai wasu anan wajan, sabida anta’ba mun hannu yanzu� d’an murmushi Abla ta saki lokacin da ta matso kusa da Baby � ki kwantar da hankalin ki mana , wane zai ta’baki apart from us ?ki duba kiga a kusa da student meke zaune ba , kawai da kinji irin haka kiyi addua kinji ?� Okay Baby tace mata amma gabaki d’aya ta kasa sakewa sabida bugawa da taji zuciyarta ta soma ,kamar wasu yara suka ri’ke hannun juna , zasu shiga class Baby tayi saurin janye hannun daga na Abla , kallan menene Abla tayi mata suma su fanan gabaki d’aya ido suka zuba mata , hanyar da suka baro Baby ta nuna � sorry nayi mantuwa , ku shiga class nima yanzu zan dawo � da sauri fanan ta furta � okay ni bari na rakaki , inyaso su sai shiga class � da sauri Baby ta girgiza mata kai � No no no ki shiga class d’in kema , karki damu ko 5 minutes bazan ba zan dawo � tana kai ‘karshen maganar ta bata bari sun yi magana ba tayi saurin barin wajan , gabaki d’aya bayanta suka zubawa ido , cikin d’an tantama fanan ta furta � anya lafiyar ta ‘kalau kuwa ?� Ajiyar zuciya Abla tayi kad’an ganin suma sun fara shiga dawuwa da reaction d’in Baby � No karku damu , nasan yanzu zata dawo tunda ta fad’a , mushiga class kawai � toh kawai suka furta , suna shiga ciki kuwa teacher d’in Maths ya shigo class d’in.

Direct Baby wajan flowers d’in da suka baro ta nufa , lokacin gabaki d’aya babu student sabida komawa class da akayi, tunda ta tunkaro wajan take jin ‘kafarta kamar ana tsigarta , amma duk da hakan bata dena tafiya ba ga wani irin zufa da take ji gabaki d’aya jikinta , saura kad’an ta ‘karaso wajan flowers d’in taji ‘kafafuwanta kamar ana zuba mata wani irin abu mara dadin ji , cikin sauri ta saka hannunta ta soma sosa wa , kamar wacce ake ‘karawa abu tana sosawa tana ‘karajin abun yana ‘kara yawa , tun tana d’aukan abun wasa har ta soma hawaye sabida yadda take jin ‘kafarta, da sauri ta juya zata bar wajan taji an hankad’ata , d’ago kan da zatayi kuma ta babu kowa a wajan , cikin sauri ta kuma ‘ko’karin mi’kewa ta ji kamar an ‘kara ta’ba mata ‘kafa , a razane Baby ta furta wayyo Allah na , adduar da Abla ta koya mata take ‘ko’karin yi amma kamar wacce ake sha’kewa ma’koshi , gabaki d’aya sai ta kasa magana, a razane ta mi’ke ta saka gudu zata koma wajansu Abla , tun kafin tayi nisa taga wani irin ba’kin abu na tunkaro ta ,da sauri Baby ta soma ja baya gashi gabaki d’aya bakinta ya kasa bud’uwa balantana ta iya addua, yadda abun yake nufota gadan gadan ne yasaka Baby yanke jiki ta fad’i a wajan su mammiya . Kamar jira abun da tagani yake , yana gani ta sume a wajan ya rikid’e ya koma gizo gizo, a hankali ya zoma zagayeta yana bud’e bakinsa, da ya kai daidai kanta sai ya kasa ta’ba , ya kai sau uku yana ‘ko’karin saka bakinsa a kanta, a karo na hud’u da d’aya daga cikin’kafafun sa suka ta’bata ya saki wani irin gurnani mara dad’in ji , cikin sauri ya soma ja baya , ko second biyar be ‘kara a wajan ba , wasu ba’ka’ken gizo gizo suka ‘kara fitowa kamar wasu aljanu, duk wanda yayi ‘ko’karin ta’bata sai ya kasa , sun dad’e suna abu d’aya kafin su zagayeta gabaki d’ayansu suna binta da ba’ka’ken idanuwansu.

***** Tunda teacher d’in maths yashigo su Abla suke kallan ‘kofa suna jiran shigowar Baby , amma har teacher d’in maths ya gama teaching d’insa Baby bata dawo ba shiyasa gabaki d’aya babu abunda suka fahimta a maths d’in, suna ‘ko’karin mi’kewa teacher d’in geography ya shigo , nan ma gabaki d’aya kasa samun nutsuwa sukai gashi 2 class ne dashi a jere , kusan Allah Allah suke kawai ya fita , time nayi babu wanda ya tsaya jiran books d’insa a cikin su , haka suka nufi wajan flowers d’in da Baby ta ce musu . Adaidai lokacin da su Abla suke tunkaro wajan adaidai lokaci suma gabaki d’aya gizo gizon suka ‘bace , sai Baby dake kwance a wajan a ‘kasa kamar matacciya.

Eshaal ce ta soma hango ta, hannunta har rawa yake lokacin da take kallan Baby , suma gabaki d’aya inda suka ga Eshaal ta kalla suka kalla, cikin sauri suka kwala kiran sunanta tare da nufar Inda take a gwance , Abla kam kasa ta’bata tayi sai binta kawai da take da kallo, Eshaal da Fanan kuwa sai faman jijjigata suke , lokaci d’aya kuma suna kiran suna ta , ganin ta’ki motsa yasaka Fanan barin Wajan a guje, amma ko mintu biyu batayi ba ta dawo d’auke da wani bottle wata, cikin sauri ta bud’e ruwan tare da yayyafawa Baby, wani irin jannufashi Baby tayi sai a lokacin Abla ta iya matsowa wajan ta , a firgice Baby ta bud’e idanuwanta tana bin ko ina da kallo , suma kallan wajan suka soma kama ganin babu komai , a hankali Baby ta saki ajiyar zuciya � Menene ya faru Baby ?� Cewar Abla , Baby ta bud’e baki zatayi musu bayani kamar almara ta manta duk abunda ya faru, hannu kawai ta bud’e tare da furta � Nima bansan me ya faru ba ! Sai yanzu da naganku a Wajan “baki suka saki gabaki d’aya suna kallanta � kudena kallo na ! Ku taso mu tafi � tana kai wa nan ta juya , suka suka bi bayanta suna mamakinta .

Har lokacin tashi yayi basu dena mamakin Baby ba , gashi gabaki d’aya ta ‘kiyi musu bayanin abunda ya faru da itama , musamman Abla da take lura da ita, lokaci zuwa lokaci tana d’an firgita. Ana tashi su Eshaal suka koma hanyar gida , itama Madam sarah time d’in tashi nayi tazo d’aukar Abla suka tafi gida .
Chapter 140 · 0% Book details