← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 146

Sashe 86

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 1 min read

ganinsa tayi ba , kamar zaiyi kuka suka tsaya suna kallan Abla da itama ta tsaya , a hankali ya furta � sister ga abincin simba nan , yaya ya hanamu shiga da mun biki , amma zamu tsaya anan Mujira ki kinji?� Itama Ablan a tsorace ta jinjina masa kai cike da tsoro ta d’auki bucket din ta d’auka Victor zai biyota ganin shima ya tsaya ne yasa ta saki a jiyar zuciya , ‘kofa kawai Victor ya bud’e mata tana shiga ya rufe ‘kofar, Itama Abla ganin d’akin da Haskene yasa bata damu ba mamakinta me d’an uwansu yake yi a waje irin haka take , bata ‘karasa tunanin da take ba Sabida motsin da ta fara ji, fuskarta d’auke da murmushi ta juyo daniyar mi’kawa simba abinci, abinda ta gani ne yasa gabaki d’aya Abla ta ware murya ta kwalla ‘kara, shima simba sabida yadda tayi ihu ne yasa ya bud’e bakinsa tare da sakin wani irin kukan zakuna, Ko motsi Abla bata kumayi a wajan ba ta zube sumammiya .
Chapter 86 · 0% Book details