← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 146

Sashe 93

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Direct d’akin Amma ta wuce lokacin tana zaune daga kan carfet , da sallama ta shigo cikin d’akin , itama Amma fuskar ta d’auke da fara’a ta amsa mata , d’an malelen Eshaal ta ajje mata a gabanta , � Amma ina zuwa yanxu zan dawo �,
Cewar Eshaal, bata jira cewar AMMA ba ta fita cikin d’akin da Sauri . Cikin ‘kan’kanin lokaci kuma ta dawo d’auke da wani tray din da ban , cikinsa lemo ne da ruwa da ta d’akko musu � AMMA yau d’an malele nake sha’awar sha , shiyasa na yi mana shi yanxu , and plx AMMA karkice mun azumi kike dan yau ba Monday bace kuma ba Thursday bane , Dan Allah kisha kinji� murmushi Amma tayi mata ta saka hannu suka soma shan d’an malelen, lokaci zuwa lokaci Eshaal tana bata labari masu dad’i dan tayi dariya , ganin tana ‘ko’kwarin kwarewa ne yasa AMMA dakatar da ita � ya isa haka Eshaal ya kamata ki dena magana idan kina cin abinci kinga yanxu ma kin kusa kwarewa.� Insha Allah AMMA � cewar Eshaal.

Adaidai lokacin da suke tsaka da Shan d’an malelensu a Daidai lokacin su kuma su Baby suka dawo gidan, tacı black abaya da wani ba’kin glass da ta saka akan fuskarta , sai faman ya tsine fuskar take musamman yadda take tauna cin güm d’in bakinta . Bata tsaya d’aukan siyayyar taba tayi wucewarta . Tana shigo cikin falourn ta tarar da bakowa , har wajan kitchen baby ta le’ka amma bata ga Eshaal ko AMMA ba , bakinta ta ta’be zata wuce sai kuma ta dakata tare da nufar d’akin Eshaal , nan ba still bata ciki , cikin Sauri baby ta nufi d’akin AMMA tare da banka ‘kofa , da Sauri Eshaal ta juyo saitin ‘kofar , itama AMMA kofar ta kalla tana cire hannunta daga kan abincin .Wani irin sallallami BABY ta saka da ‘karfi kamar wacce taga wani mugun abu � Mommy , Mommy kina ina ?�, muryar momy sukaji tana cewa menene ya faru baby na ko sun ‘kara yi miki wani saban rashin kunyar ne…� itama dakatawa tayi tana bin su Eshaal da kallo � munafukan Allah abunda kuke yi kenan? Wato idan mun fita zuwa kuke ku satar mana abinci batare da sanin mu ba ? Uban wa ya baku damar ta’ba mana kaya wato har da d’aukar lemo da ruwa tunda ga gidan ubanku ko? Halin matsiyata a jikin ku yake kenan ko ?� Da Sauri Eshaal ta girgiza mata kai � momy babu ruwan AMMA a ciki , hasalima ni ce na dafa na kawo mata babu laifinta a ciki.� A zuciya momy ta shigo cikin d’akin � dan ubanki zaki rufe mun baki ko sai na gurza miki shi da bango? Duk salan iskanci da bari ta koya miki shine har kike da zarar fad’amun babu ruwan ta a ciki?� Sun kuyar da Kai ‘kasa AMMA tayi amma kwata kwata yanayin face d’inta be canza ba , a hankali ta furta “kiyi hakuri � dogon tsaki Momy taja � muna fuka daman kullum abunda kika iya kenan ayi hakuri ayi hakuri , banzaye kawai dangin matsiyata ,� tana kai ‘karshen zancanta ta juya , itama baby cikin ta’be baki ta kalli Eshaal � ki tashi kizo ki jera mun kaya na a cikin kwaba , idan kinga dama kuma ki zauna karkiyi , dan gin matsiyata� tana kai ‘karshen maganarta itama ta juya tana banko musu ‘kofa. Fashewa da kuka Eshaal tayi , wannan cin mutunci har ina dan kawai ta sha d’an malele shine suka cancanci wannan wula’kanci? Lallashinta AMMA ta soma � kar kisaka wannan abun cikin ranki , komai me wucewa ne , kinji ? Ki goge hawayenki ko so kuke su ‘kare kirasa na kuka ranar Auranki?� ‘Boye fuskarta Eshaal tayi tana goge face d’inta , time to time kuma tana murmushi Sabida maganar AMMA ita da bata da ko da saurayi ina taga mijin aure ? Murya a sanyaye itama ta furta � AMMA dan Allah kiyi hakuri akan abunda su Baby suke miki?� Girgiza mata kai AMMA tayi � karki da mu ni babu abunda sukai mun, ya kamata ki tashi ki bita , kar ta sake miki wani abun, ni ki bari zan kwashe kwanukan� da Sauri Eshaal ta girgiza mata kai � No AMMA be kamata ina wajan kice zaki kai ba , kawai kiyi zamanki ki huta Sabida kar ciwan ‘kafarki ya tashi kinji ?� Murmushi AMMA ta sakar mata � Allah ya albarkaci rayuwar ki , ya banı ikon sakaki farinciki kamar yadda kika sani �, da Ameen Eshaal ta amsa lokacin da take kwashe kayan da har taji d’an malelen ya fita a ranta.

Tana kaiwa kitchen d’akin Baby ta wuce gabaki d’aya ta har gitsa d’akin shigowarta dan kafun su dawo saida Amma ta gyara mata , tana kan gado hannu d’auke da wayar ta , ga lemo da take sipping, kunnanta kuma pod ne da alama wa’ka take ji sabida yadda take gyad’a kanta , Eshaal bata ce mata komai ba ta fara kimtsa mata d’akin Sabida kwana biyun nan neman abun fad’a Baby takeyi, tana gama gyara d’akin kayan siyayyar da su baby sukai ta fara jera mata bayan uban tulin kayan Baby da ta ‘kara gyara wa , kana kallansu kasan da gangan kuma baby ta ‘bata su, tun da ta soma gyaran baby take neman hanyar janta da fad’a amma ko kusa Eshaal bata kula taba , tana gamawa tayi wuce wat ta itama batare da ta kula taba.

✨✨✨✨✨✨�

*NEW YORK*

11:45am Abla ta farka daga baccin da ya d’auke ta , bakinta d’auke da adduar bacci ta soma bud’e idanuwanta da Suka d’an kunbura, lokaci d’aya kuma ta lumshe su ta sake bud’ewa tana mikewa zaune � Yah Allah Yaushe barci ya d’auke ni haka ?� Cewar Abla lokacin da Mike tsaye , Daidai gaban mudubin d’akin ta tsaya tana bin fuskarta da kallo , sai a lokacin ta tuno da zafin da d’an yatsan ta yake mata , cikin Sauri ta tsugunna ta shafa wajan , a hankali kamar me rad’a da wani ta ta’bile bakinta � mugu kawai , Allah sai ya sakamun tsabar mugunta harda takan d’an yatsa Sai ya wani dunga d’aure fuska kamar bread, ai ko shi bread yana fara’a tunda yana da dad’i , me fuskar tuwo kawai� ya ‘karasa tana turo bakinta kamar da wani take . Face d’inta ta wanke lokacin da ta kalla Agogo , bata zauna a cikin d’akin ba ta sakko down stairs . Bobo ne zaune kan kujera sai uncle da prince , har ‘kasa Abla ta tsugunna ta gaishe da uncle kafun ta kalli yaya bobo shima cikin fara’a ta gaishesa � har kin tashi daga baccin Kenan ?� Kanta Abla ta jinjina masa tana murmushi kafin ta juya Side d’in prince shima ta gaishesa , da murmushi akan fuskarta ya furta � fine lil sis , kinga tun da wuri little ya saka a miki abinci ya kamata kici yanzu� d’ayan side d’insa ta duba taga little d’in baya wajan fahimtar hakan yasa ya furta � karki damu little yana d’akin yaya big boss yana bacci but nasan any moment from now zaki gansa�, tunda ya ambaci Big boss taji zuciyarta ta buga da ‘karfi daurewa kawai take shiyasa a hankali ta furta � okay �, har zata mi’ke sai kuma ta fasa ta fuskanci su bobo da suka zuba mata ido, kamar zatayi kuka ta furta � Nagode sosai, Allah yasaka da Alkairi, Allah ya saka muku da mafificin Alkairi, Allah ya dauwamar daku cikin farin ciki, Nagode sosai.., � zata cigaba da adduar bobo ya katseta � ki dena wannan godiyar , we’re all family now ! Banaso kinji ? Ko so kike little ya sakko ya saka mana kuka yace mun ta ‘ba masa lil d’insa ?� Ya ‘karasa yana d’an zaro mata ido , murmushi ne ya kwace mata lokaci d’aya ta furta � Ah’ah � shima fuskarsa cike da murmushi ya furta � Good ! Now yaya prince a bawa lil d’in mu abinci � mi’kewa tsaye prince yayi kafun ya furta � Now� tray din abincinta ya dakko mata ya kawo mata har inda take , da kanshi yayi serving d’inta , cikin d’an tsokana ya furta � yaya naga alama lil d’in nan ta fara sabawa da abincin mu�, murmushi kawai Abla ta sakar masa tana kare face d’insa , � don’t mind him daughter , ci abincin ki karyayi sanyi � cewar uncle .

Balaifi ta soma cin abincin su duk da ba sosai ta iya ci ba amma ba kamar dama tunda yanxu bata Amansa , tana cikin ci taji muryar little yana furta � my lil�, at the same time ‘kamshin turaransa ya daki hancinta , jikinta har ya soma rawa kad’an lokacin da ta d’ago face d’inta ta kalli saitin sa , da Sauri kuma ta sun kuyar da kanta ‘kasa tana wasa da spoon d’in hannunta , duk taku d’aya da yake kamar da bugun nunfashinta yake , addua kawai take karanto wa cikin zuciyarta , ganin suna ‘kara kusan to Inda suke � lil sai yanzu kika tashi?�, cewar little yana katse mata rud’anin da ta jefa kanta , da Sauri ta jinjina masa kanta murya na rawa ta furta � ehe..eh mn�, shima kansa little ya jinjina mata � thank god kin fara cin abinci da d’ure zamuyi miki�, kasa magana tayi sai kifkifta idanuwanta da take kamar zatayi kuka , ta kasa d’ago eyes d’inta ko sau d’aya ta kalli direction d’insa gashi ya hana ta zo inda yake.
Chapter 93 · 0% Book details