← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 146

Sashe 50

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Karfe 11:20am ya farka daga baccin da yake , a hankali ya fara bud’e kyawawan eyes dinsa, abunka da me sexy eyes sai idanuwansa suka ‘karayin kyau Sabida baccin da yayi, har yanxu fuskarsa babu fara’a ko murmushi a tattare dashi, side d’in little ya kalla yaga yadda yake baccinsa hankali kwance tsawan 1 minutes yana bin fuskarsa da kallo kafun ya janye eyes d’insa yana mi’kewa zaune sosai, kyawawan long fingers dinsa farare tas dasu ya saka kan lallausan gashin little da yake zuwar masa har wajan idanuwansa sabida irin gyaran askinsa, cikin Cool voice kamar ba tashi ba ya furta � Hey ! Wake up!�, ganin little ya d’an motsa kad’an ne ya kara bud’e muryarsa a hankali � wake up�, yadda little ya fara bud’e eyes dinsa ne bakinsa d’auke da addua yasa big boss had’e ransa kamar bashi ba , da wani irin kallo yabi little dashi � who permitted you , to enter into my room , and even on my bed ?�, hannuwansa biyu little yasaka ya ri’ke kunnuwansa , cikin d’an turo baki ya furta � yaya big boss nayi missing dinkane kuma na dad’e bamu kwana tare ba �, ya ‘karasa yana turo bakinsa kamar wani ‘karamin yaro, be aune ba yaji big boss ya d’alle masa baki da har saida yaji zafi ya furta “ouch! Da zafi�, lumshe eyes dinsa big boss yayi duk da yaji zafin abunda yayi wa little a zuciyarsa amma a fili sai ma kofar fita da ya nuna amsa , fuska ba fara’a ya furta � out of my room!� Little zai ‘kara magana cikin d’age gira big boss ya furta � Now !�, duk da ba cikin d’aga murya ya furta ba , sunkuyar da kansa little yayi kamar me shirin sakin kuka ya nufi ‘kofar barin d’akin , sai da ya tabbata de ya bud’e door din tukunna kafun ya d’ago ya kalli big boss da ya d’ago eyes dinsa shima , hawayen da ya gani akan fuskar little ne yasa ya d’an ware kyawawan eyes dinsa amma be ce masa komai ba sannan be motsa daga yadda yake ba , a shagwa’be little ya furta � yaya ban karya ba Sabida kaima bakaci abinci ba �, yana gama fad’ar hakan yayi saurin rufo masa ‘kofa dama da gangan yayi hawayen , Hakanne kawai zaisa big boss yaci abinci tunda little be cıva . Lumshe eyes dinsa big boss yayi a karo na ba adadi kafun ya saka hannunsa cikin lallausan gashin kansa da ya sakko masa har gadon baya , yadda ya motsa bakinsa kad’anne ya bawa dimples dinsa lotsawa kad’an.
Cikin nutsuwa ya mike tsaye gabaki d’ayansa , sosai yanayin jikin big boss zai baka tsoro da muscle dinsa ba ‘karamun murd’ewa sukai ba alamar yasabu babban horo c bakar singlet dinsa sosai ya fito da ainahin kakkarfar surar jikin da Allah yayi masa , ga baki d’aya murd’ad’d’an bakin gashin kansa ya zubo masa aka fad’unsa, har lokacin kuma sarkar diamond dinsa na wuyansa . Cikin takun sa me cike da izza big boss ya soma taka ‘kafarsa kamar bayasan taka ‘kasa , komai nasa cikin nutsuwa yake yinsa duk da rashin fara’ar da yake fuskarsa direct ‘kofar da ya shiga jiya ya nufa kai tsaye .
Little yana sakkowa main falour ya tarar da uncle , bobo da kuma prince zaune a falour direct kujerar da bobo yake ya nufa kasan tuwar a 3 sitter yake zaune , gabaki d’aya binsa sukai da kallo ganin yadda ya kwanta ya d’ora kansa a cinyar bobo, shima bobo bai ce masa komai ba sai hannunsa d’aya daya saka masa cikin gashi yana d’an masa susa a hankali kafun ya d’aga shi zaune yana binsa da kallo � jekayi wanka tukunna , sai kaci abinci okay !?�, okay kawai little yaje masa yana mikewa cike da tsokana prince ya furta � uhm shiyasa naji gidan mu har ya fara wari Aushe little beyi wanka ba �, kamar zaiyi kuka kuwa little ya mi’ke yana kallan prince lokaci d’aya dariya ta zo masa amma ya danneta yana nufar hanyar elevator , cikin d’aga murya little ya furta � fine ai daga d’akın yaya nake , bari na koma sai kayi masa bayanın yadda nake wari�, bai karasa zancansa Sabida sufar da prince yayi ya nufeshi � Haba mana little dina kai ma kasan wasa fa nake maka, kaga sai kamshin turaran yaya ma kake , let’s go ni da kaina ma zan kai ka d’aki, ya Karasa yana sabar little a baya ko elevator be bari sun hau ba ya nufi stairs, girgiza kansa bobo yayi � bazaku ta’ba girmaba�, shima uncle murmushin drama dinsu yayi “I love it idan fuskarsu tana dauke da murmushi, kullum ina farin cikin hakan..�, ya karasa a sanyaye, murmushin da yafi kuka ciwo bobo ya saki “uncle don’t even start dis please, mistake d’aya sai ya shafi kowa, kasan halinsa, zai iya fitowa any time now “murmushin manya uncle yasaki kafun ya furta � da sannu zuciyar nan tasa sai ansamu me saukar da ita dukda nasan Nima da wuya amma ina fatan Allah ya sanyaya masa wannan zuciyar tasa komai ya wuce , “uhmm � kawai bobo yace dan shima kansa baya san a taso da maganar.
Suna zaune almost 30minutes kafun su prince su ‘kaya sakkowa wannan karan little cikin Riga da wando red colour da sukayi matukar yimasa kyau ya kasa , ga gyaran gashin kansa da yafi komai d’aukar hankali, kamshin turaran jikinsu gabaki d’aya ya cika ko ina na cikin falourn had’e da sanyin Acn . � wow ! Little wannan wanka haka sai kace me shirin zuwa zance , da Sauri ya zaro idanuwansa sai kuma ya shagwa’be face dinsa � plx uncle ka bari kalli fa kallan da yaya bobo yake mun�, pillow din side dinsa bobo ya dauka ya jefa masa � little bakaji ko ? Kaga ina wasa da kai ?� Dariya little ya saki yana karasa wa inda bobo yake yayi hugging Dinsa � Haba yaya bobo ! And nifa yunwa nake ji bari naje na kira yaya � bai ‘karasa zancan saba sabida elevator din da aka bud’e gabaki d’aya maida eyes dinsu sukai suna jiran fitowarsa.
Tun kafin yafito daddad’an kamshin perfume d’insa ya cika ko ina har ba ajin kamshin turaran su little ,ta ko ina kamshin turaransa ne yake yawo sabida Acn falourn yadda ta ‘kara buso da sanyin ta sai hakan ya kara wa kamshin falourn dad’i , gabaki d’ayansu kowa jira yake ya ga fitowarsa , a hankali ya fara taka kafarsa gabaki d’aya sai suka mayar da hankalinsu sosai akansa, sosai kyawu da haduwar big boss ta kara razanani dan ba karamin kyau Allah yayi masa ba , kyakkyawane na ajin karshe da furta yanayin kyansama bata lokaci, iya haduwa da tsari da ko wace mace zata nuna a sa’a big boss ya wuce tunanin hakan . Sosai ya ‘kara d’aure fuskarsa sabida yadda yaji alamar idanuwa akansa amma gabaki d’aya babu alamar zai d’ago ko nuna alamun akwai masu rai a cikin falon,sanye yake cikin ‘kananan kayan Ralph Lauren black colour da Suka fito da hasken fatar jikinsa fari tas dashi sosai kayan suka kar’beyasa musamman daya had’u da gyaran gashin kansa da ke tashin kamshi, sai shinning ba’kin sumarsa da ta tayi mugun had’uwa yake , yadda ya tufke gashin kansa sai ya karayı masa kyau sosai , hatta kyakkyawar face d’insa sai da ta fito fara tas da ita duk da babu fara’a akanta ga sarkar diamond dinsa Siririn sai faman shinning take , ‘kafarsa kuwa sanye yake cikin kyakkyawan bakin takalmin horsebit loafer . Tunda ya fara takunsa cikin nutsuwa bai d’ago ya kalli kowa daga cikin su ba , cikin wata kujera me shegen kyau da babu Wanda ya’ke zama akai sai shi ya nufa, yana crossing legs dinsa prince da little suka yi saurin sauke ‘kafarsu da Sukai crossing , a sanyaye prince ya furta � yaya good afternoon�, shiru be amsa masa ba sai ma lumshe eyes d’insa da yayi kusan 3 minutes har prince ya cire rai da amsawar sa sai kuma ya tsinci daddad’ar muryar sa yana furta � Good afternoon uncle…� yanda yayi maganar a hankali da ace ba shi suke kalla ba da bazasu ta’ba gane cewa yayi magana ba , murmushi uncle ya sakar masa � Afternoon too BUBUBUBU…� da Sauri big boss ya d’ago da eyes dinsa da suka fara kad’awa ya zubawa uncle da ke binshi da kallo shima , da gangan ya furta bubububu Sabida yaga reaction dinsa , amma yadda ya ‘bata raine yasa uncle sakin wani murmushin � Menene na ‘bata rai kuma ?Please banasan wannan reaction din nasa, idanuwan big boss ne ya soma kad’awa har yanxu yana bin uncle da kallo amma bakinsa yayi masa nauyin da ko harshensa bayajin zai iya d’agawa , yadda bobo yaga reaction din big boss ne yasa yayi saurin dakatar da maganar � uncle please…� cewar bobo duk da shima yana kokarin controlling kansane sabida ran big boss da yaga ya soma ‘baci, a zuciye big boss ya d’auke eyes dinsa daga kansu ya lumshe idanuwansa yana sosa girarsa guda d’aya me tsaga da ‘karamin d’an ya tsansa, da ido bobo ya nuna musu dinning alamar su d’auko abincin sa Dan ko giyar wake suka sha yadda suka ga ransa ya ‘baci idan wani yace zai kaimasa abu zai iya balla mutum a wajan , a hankali su Prince suka cika gaban wani center me fad’i sosai da abinci kala kala gwanin burgewa har suka gama be bud’e eyes dinsa ya kallesu ba duk da motsinsu da yake ji cikin kunnuwansa , cikin kujerar gefansa little ya zauna a hankali ya furta � yaya yunwa nake ji�, a hankali ya soma bud’e eyes dinsa kallo d’aya yayiwa little kafun ya d’auke eyes dinsa yana zama sosai abincin ya kalla da kansa kafun ya kalli little , inda suke bobo ya nufa da kansa yayi serving d’insu sabida yasan kalan abunda kowa yake iyaci , da ido big boss ya kalli little sannan ya kalli food din da bobo yayi serving dinsa, yagane me yayan nasa yake nufi shiyasa ya janyo abincin nasa ya faraci a tsanake banda big boss da ko farar ta’ba abincin beyi ba , barin wajan bobo yayi tsawan 5 minutes ya fito hannunsa d’auke da wani unique small cup me d’auke da coffee sai faman turiri yake , har inda big boss yake ya karasa tare da mi’ka masa , a hankali big boss ya saka dausasan hannunsa kamar ba soja ba ya karbi cup din yana lumshe wa bobo ido, bobo ya gane me hakan yake nufi shiyasa ya d’anyi knodding kansa kadan , cikin wani irin unique way ya fara sipping coffee dinsa , little ma sosai ya zage yaji abincinsa ganin yadda big boss yake shan coffee ya tabbata yana gama sha zaici abincin ko kad’an ne , hakan kuwa a kayi Belgian waffles kawai yayi cutting kad’an ya soma ci kamar bayasan taunawa, a nutse yake cin abincin hankali kwance , had’ad’d’iyar wayarsa da ta ‘kara Haske alamar kira na uku kenan Sabida yadda take haske tun d’azu cikin silent amma mamallakin wayar ko gefen inda take be kalla ba , wayar bobo ce ta soma ringing , ganin wanda yake kiran sa ne yasa ya kalli big boss yana sakin wani dan iskan murmushi har Wayan yayi cutting a karo na biyu da aka ‘kara kiransa sai da ta kuşa tsinkewa ne yayi picking , banji me aka ce masa ba sai “okay � da bobo yace yana nufar big boss da phone din hannunsa , tun kafin ya karasa big boss ya dakatar dashi da narkakkun eyes dinsa , a hankali ya zari tissue ya goge bakinsa , phone dinsa kawai ya d’auka ya nufi hanyar fita, sai da Suka ga fitarsa alokacin prince suka saki ajiyar zuciya , murmushi bobo Kawai ya saki daman yasan za’arina ba kowa ne yake kiran big boss ba face president danshi big boss idan rashin mutumcin sa yana kuşa baya ragowa kowa , mayar da wayar sa kunne bobo yayi shima yana bun bayan big boss da ya fita sai a lokacin prince ya Samu damar tanbayar uncle abunda yake san tanbaya � uncle Menene ma’anar Bubububu d’innan da kake yawan fad’awa yaya and naga duk lokacin da ka fad’a Ransa sai ya baci�, a jiyar zuciya uncle ya saki yana kallan prince da little da suke jiran amsarsa � it’s a long time Name! Labarine da ayanxu bakwa bukatar sani har sai lokacin da yayi niyyar kusani�. Amma uncle please kadena fad’a masa to tunda ransa zai ‘baci ni bana jin dad’i Allah , shima fa yaya bobo ranshi ya ‘baci amma yake ‘boye � murmushi me Sauti uncle ya saki batare da ya basa amsa ba suka canza hirarsu zuwa wata davan.
Chapter 50 · 0% Book details