← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 146

Sashe 136

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

9:30am gabaki d’aya suka fito banda Big Boss , a maimakon su jira sai suka nufi dinning abun su , tunda sun san ba yanxune zai fito ba , har aka gama breakfast d’in Abla bata ci wani abinci dayawa ba , ganin idanuwansu ne yasaka take tuttura abincin gudun kar suyi mata magana. A na gamawa ta mi’ke zata tafi Bobo ya dakatar da ita � Lil can you make a cup of coffee ?� A hankali Abla ta furta � yes !� Tana nufar inda coffee maker yake , komai cikin sanyi take yin sa yau, tana gama had’a coffee d’in ta d’akko masa , girgiza mata kai yayi tare da nuna Mata upstairs da hannunsa guda d’aya � Not for me ! Ki Kai masa sama � ta gane abunda yake nufi, � Toh Abla Kawai tace masa ta nufi hanyar part d’insa . Tana hawa kai tsaye falournsa na biyu ta shiga tunda tasan bazata tarar dashi a cikin falourn farko ba , ana biyun ma sai taci rashin sa’a baya falourn , kamar zata ajje masa coffee d’in ta wuce sai taga rashin dacewar hakan , ‘kofar bedroom d’in sa tayi knocking sau d’aya, shurun da taji anyi mata yasa ta ‘kara knocking a karo na biyu , still ba’a amsa mata ba , zata juya taji kamar an bud’e ’kofar kad’an , a hankali ta shiga cikin d’akin bakin ta d’auke da sallama , da Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa ganin sa sanye da Singlet sai dogon ba’kin wandon jikin sa , sau d’aya ya kalleta ya d’auke eyes d’in sa , tun kafin tayi magana ya d’an nuna d’akin da hannun sa , kamar Wanda aka saka dole ya furta � Ki gyara mun�, be jira jin amsar taba ya shige cikin dressing room d’insa , bin bayan sa da kallo Abla tayi tana hararar sa ‘kasa ‘kasa ,ganin bata da wani za’bin yasa ta ajje coffee d’in hannun ta ta soma gyara masa d’akin , mistakenly bata san ganin ya akai ba , sai ganin light d’in d’akin ya d’auke gabaki d’aya , a mugun rikice Abla ta kwalla ihu, lokaci d’aya mafarkin da tayi d’azu yana ‘kara dawo mata cikin kai , ga gudun d’akin da gabaki d’aya ya ‘kara hautsina ta , almost 2 minutes sai faman ihu Abla take gabaki d’aya ta birkita kanta , ita kanta batasan me taneyi ba , ji tayi an finciko ta , lokaci d’aya Big Boss ya kunna light d’in da kashe , wani ihun Abla ta saki tare da sulalewa ‘kasa a sume , Sabida yadda tayi arba da ‘ka’k’kar far damtsen hannun sa ga shi ko riga babu a cikin sa . ‘Karamin tsaki Big Boss ya ja ganin yadda ta sume, a hankali ya soma bin d’akin da kallo gabaki d’aya Abla ta ‘kara binkita shi , hatta saman bed d’insa gabaki d’aya ta cukur kud’asa. Lips d’insa ya taune kad’an tare da komawa cikin dressing room d’in sa , almost 10 minute yayi a ciki kafun ya fito har lokacin Abla tana kwance a ‘kasa , ruwa ya d’akko mana sanyi ya soma zuba mata a fuska , a firgice Abla ta farka sabida ruwan da taji a kanta , har lokacin be dena zuba mata ruwan ba sai da ya juye mata shi gabaki d’aya a jikinta .
� Just 10 minutes na baki ki gyara abunda kika ‘bata , sannan ki d’auki dirty legs d’inki and leave this place immediately � ko kallansa Abla batayi ba Sabida abunda yayi mata , da tayi niyar barin d’akin saidai in kashe ta ne yayi sai kuma ta fasa , ganin ya d’auki system d’insa ya bar cikin d’akin. Cikin hanzari ta soma gyara masa d’akin, hawayen da bata san na mene ne ba suna sakko mata cikin idanu, tana gamawa ta fito daga cikin d’akin sabi sanyin da takeji bakinta har rawa yake . A falour ta tarar dashi yana operating system d’insa , batare da ta kallesa ba ta furta � na gama � har ta wuce ya dakatar da ita , cikin wani black wallet me shegen kyau ya d’auko wani paper note na kud’i guda d’aya ya jefa mata, ko arzi’kin kar’ba da hannun ta bata samu ba , cikin ta’be baki ya furta � For your work�, kallansa tayi tare da kallan kud’in da yake fad’i a ‘kasa , ji tayi hawaye na shirin zubo mata tayi saurin had’iye su , hannu ta saka ta d’auki kudin lokaci d’aya wani murmushin ta kaici ya fito mata , ko uffan bata kuma ce masa ba ta fice daga falourn, kusan saura kad’an suci karo da Bobo da yake ‘ko’karin shigo cikin d’akin, sau d’aya ya kalleta ya girgiza kai , cikin tausasa murya ya furta � ki je ki canza kayan jikin ki , kar mura ya kama ki , nan da 2 hours ki same ni a garden � a sanyaye Abla ta furta masa “Tom � , shi kuma ya wuce falourn Big Boss .
� Na d’auka kayi accepting nata ? Why please Dude? � cewar Bobo Lokacin da yake shigowa cikin falourn , ko sau d’aya Big Boss be d’ago ya kalle saba ya cigaba da abunda yake , sama Bobo yayi yana ‘kara fuskantar Big Boss � magana nake maka fa , why are you treating her like this ? Yaushe zakayi accepting d’in ta as a family of this house ?”da kawa tawa Big Boss yayi cikin ido ya kalli Bobo ,� She will never be !� , d’an murmushi Bobo yayi kafin ya furta � Really ? Nasani Kai ma kasani , da aiko ta akai dan ta cutar da mu da a tun ran farko zamu gane , da bazata ta’ba yin kwana d’aya a cikin gidan nan ba , please ka sassautawa yarinyar nan , duk da bansan labarin taba nasan itama ta sha wahala a rayuwar ta� d’an ta’be bakinsa Big Boss yayi batare da ya sake cewa komai ba , shima Bobo mi’kewa yayi tsaye yana kallan Big Boss , � Bana so kayi abunda zai zamo maka matsala nan gaba , i know you very well , bansan menene ka ke shiryawa ba , but please don’t hurt her �, yana kai ‘karshen maganar sa ya bar falourn , shima Big Boss ba tare da damuwa da abunda Bobo ya fad’a ba ya cigaba da aikinsa.
Kamar yadda Bobo ya umarce ta , wajan ‘karfe 12:10pm ta nufi garden d’in, a zaune ta tarar dashi cikin wata runfa me kyau , ga kujerun zaman sha’katawa suma a wajan , gaban sa wasu drinks d’in da alama sha yake sabida yadda ya nuna a cikin d’aya daga cikin cup d’in wajan , yana ganin Abla ya sakar mata murmushi tare da nuna mata wajan zama . Jiki a sanyaye Abla ta zauna gabaki d’aya ta tsargu sabida batasan akan me yake nemanta ba , shima ya fahimci hakan daga reaction d’in ta , wani murmushi ya ‘kara sakar mata � karki damu baki mun laifin komai ba , � itama Abla murmushi ta saki ganin ya gano ta , book d’in hannun sa ya ajje yana fuskantar ta da kyau � Nasan kin yi mamakin dalilin kiran ki da nayi ko ?� Kanta Abla ta jinjina masa , � karki ‘kullace sa akan abunda yake miki, and karki tunanin tsanar ki yayi , its not like that�, d’an kallan sa Abla tayi dan bata fahimci maganar sa , wani murmushi Bobo ya saki kafun ya furta � Big Boss ! Yeah Big Boss nake magana , ba mugu bane kamar yadda kike tunani zan iya cewa he’s the best soul ever, yana yin rayuwane ya mayar dashi hakan ba wai ke kad’ai ba , kowa ma hakan ne , idan baka san halinsa ba , bazaka ta’ba sanin ya yake ba ,� yana kai ‘karshen maganar da yayi shiru , Abla kuwa tunda ya fara yaban Big Boss ta d’an ta’be baki cikin zuciyar ta � Wannan mugun ne zaka ce yana da kirki mutumin da be san komai ba a rayuwar sa sai mugun ta � katse mata tunanin ya yi tahanyar ci gaba da magana ,� Nasan zaki yi mamaki maganganu na � ya ‘karasa yana kallanta � lokaci kawai zaki basa , he will trust you too! Yana da dalilin da yasa baya yadda da kowa , bawai sabida yana tsoran za’a cutar da shi ba , No ! Yana yin komai ne for his family, Little kamar d’an sa haka yake ,no matter abunda zai masa , ya fishi jin zafin� d’an ‘karamun dariya Bobo yayi , � He’s a bit arrogant sometimes i think, but he’s the best brother i have ever in my life , farin cikin family d’in sa shine na farko a wajan sa � shiru Bobo yayi lokaci d’aya mood d’in sa ya canza , lokaci ya kalla kafun ya sakar mata murmushi kad’an � idan lokaci yayi zaki san komai amma kakki ‘kulla ce sa please “shiru Abla tayi masa sai kallan sa da take , mi’kewa tsaye yayi yana d’aukan wani ‘karamar waya dake kan table d’in wajan � zamu cigaba wata ran yanzu ya kamata ki koma cikin gida okay ?� Itama mi’kewar Abla tayi tana furta � Na gode sosai Yaya Bobo � , kansa ya jinjina mata � its okay � , bata kuma cewa komai ba ta juya , sai da yaga ta ‘bacewa ganin sa tukunna ya saki wani shegen murmushi, cikin dariya dariya ya furta � Dude�, dai dai lokacin da ake kiran sallah , shiyasa ya bar duk abunda yake ya nufi masallacin gidan.
Abla taba komawa cikin d’aki Alwala tayi , tayi sallar azhr d’inta , kud’in da Big Boss ya jefa mata ta d’auka tana ‘kara bin ta da kallo , lokaci d’aya taji ranta ya soma ‘baci, � ‘kazama ! Villager � shine ya ‘kara fad’o mata cikin rai, murmushin ya’ke Abla ta saki tana girgiza kanta kad’an. Ganin tana ‘ko’karin sawa kanta dawu ta ajje tunanin komai a gefe ta fara duba books d’inta na makaranta.
Da daddare ma hakan ne ya faru , suna zaune su hud’u a falourn daga ita sai Little , prince sai kuma Uncle , tare sukai dinner d’in su , su hud’u gwanin burgewa , suna gamawa suka dawo falourn suna hiran su , Abla sai data daidai ci Big Boss ya kusa shigowa gidan ta gud’u d’aki abun ta .
Chapter 136 · 0% Book details