← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 146

Sashe 122

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Me ya faru ? “Cewar Bobo ganin yadda hankalin Little ya tashi lokacin da ya shigo cikin falourn , ga Abla da itama ta wuce ta na kuka , kasa magana Little yayi sai kansa da yake girgiza musu , cikin Sauri ya bi bayan Abla , shima prince da uncle bin bayan sa sukai dan ga baki d’aya little ya tayar musu da hankali, fahimtar kamar da matsala yasa Bobo bin bayansu banda Big Boss da tun bayan kallo d’aya da yayiwa Little be ‘kara kallansa ba, har yanzu yana tsaye a inda yake sai ma folding hannunsa da yayi waje d’aya , face d’insa kamar kullum babu fara’a kwata kwata a kanta.
Little be zame ko ina ba sai d’akin Abla , cikin Sauri ya shiga Bedroom d’inta ganin ‘kofar d’akin abud’e amma gabaki d’aya bata cikin d’akin , ‘karar ruwa da yaji a toilet da kukan ta ne yasa yayi saurin nufar ‘kofar kamar zaiyi kuka yasan har yanzu kuka take, knocking d’in ’kofar ya somayi da d’an ’karfi � Lil ! Lil ! Please open the door let’s talk , please ki kwantar da hankalin ki , komai zai dai dai ta�, shurun da yaji babu amsa ne yasa hankalinsa ‘kara tashi Daidai lokacin da su Bobo suka shigo cikin d’akin suma � Please sister na ro’ke ki , ki bud’e ’kofa zaki iya raunata kanki � ya kasa maganar sa shima yana hawaye dan har cikin zuciyarsa yake jin wani irin d’aci da ba’kin cikin abunda akai wa Lil d’insa , kallan sa Bobo yayi cikin d’an d’aga murya ya furta � I’m asking you kamun bayani , me ya faru ? Wani ne ya ‘bata mata rai ?� Kansa little ya girgiza masa hawayen face d’insa basu dena sakkowa ba , hankali a tashe prince ya furta � Dan Allah little ka fad’a mana ka ta yar mana da hankali , and kaga may be tana using bathroom ne ma ba wani abun bane � kuka little ya fashe musu dashi yana nunawa Bobo ‘kofar toilet d’in� No yaya zan muku bayani daga baya , just please yaya ku bud’e ’kofar nan , zata iya jiwa kanta rauni , d’an Allah yaya � ya ‘karasa yana ‘kara sakin wani kukan dai dai lokacin da suka ji kamar fad’uwar abu a cikin toilet d’in, lokaci d’aya suka soma bugun toilet din suna kiran sunan ta � Sister ? Sister ? Sister ?� amma babu amsa, Shirun da suka jine ya Matu’kar tayar musu da hankali , da iya ‘karfinsa Bobo ya saka ya daki ‘kofar da kafad’unsa , amma kamar Wanda ya daki kataho ko motsi batayi ba, a karo na biyu ya ‘kara da kar ‘kofar da ta d’an motsa kad’an , kafad’unsa ya ta’ba tare da kallan Little da face d’insa tayi ja sosai , cikin ‘yar damuwa Bobo ya furta � called your brother � da sauri Little ya nufi down stairs har lokacin Big Boss na tsaye Inda suka barsa , Little yana ganinsa yaji wani saban kukan na zuwar masa da Sauri yayi hugging d’in Big Boss yana yin kukan sa ‘kasa ‘kasa , lumshe eyes d’insa Big Boss yayi Sabida yadda yaji zuciyar Little ya bugu da Sauri kamar ba zai yi magana ba sai kuma cikin ya mutsa face ya furta � what happen?�
A hankali Little ya sauke ajiyar zuciya , yasani ko be fad’a wa kowa ba dole zai fada wa Big Boss , shiyasa cikin sanyin jiki ya labartawa Big Boss abunda ya faru , tun lokacin da ya ganta tana kuka da bayanin da su Eshaal sukai masa , shiru Big Boss yayi batare da ya tanka ba sai ma d’an ta’be bakinsa da yayi kad’an , kamar wanda aka saka dole ya furta � wannan ya saka kuka ?� Kansa Little ya jinjina masa wasu hawayen na ‘kara taruwa cikin eyes dinsa , Ya bud’e baki zai yi magana sai ya tuno da abunda ya sakko dashi ‘kasa , cikin kwantar da murya Little ya furta � yaya please ‘kofar toilet d’inta aruf…e ta..ke� kallan da Big Boss yayi masa ne ya sa ragowar maganar sa ta rarrabe , cikin rashin damuwa Big Boss ya furta � And ?� Hawayen sa Little ya share ,� Yaya Dan Allah ba danni ba , ka bud’e ’kofar toilet d’inta , zata iya jiwa kanta rauni� kallan diamond watched dinsa Big Boss yayi kafun ya d’an ya mutsa face d’insa kad’an � am going out �, shine kad’ai abunda Big Boss ya iya furtawa , cikin Sauri Little ya haura sama yana goge kwalla har ya wuce d’akin Abla, yana shiga yatarar da har lokacin Bobo na du’kar ’kofar amma ta ki bud’uwa , almost 2 minutes gabaki d’ayansu suka juyo saitin bakin ‘kofa sabida ‘kamshin turaran Wanda basu ta’ba Saran zai shigo d’in ba, Little har da murnarsa ganin Big Boss a bakin ‘kofar Abla amma duk Wanda yaga face d’insa zai ganta a had’e sama da sauran lokuta, babu Wanda ya kalla a cikin su har ya ‘karaso cikin d’akin, gabaki d’aya matsa masa hanya sukai har ya ‘karaso wajan ‘kofar, da iya ‘karfin da Allah yayi musu shida Bobo suka daki ‘kofar da ‘karfin gaske , amma Sabida ‘koface bata wasa ba yasa ta motsa Batare da ta bud’u ba , a karo na biyu suka kara dakar ‘kofar wannan karan sai data d’anyi ’Kara , a karo na uku da Big Boss yayi mata wani irin Wawan bugu ‘kofar ta jijjige gabaki d’ayan ta , rai a ‘bace Big Boss ya hankad’a ‘kofar ciki da har saida Bobo yayi saurin dafe ta , daga inda yake yana iya hango ta cikin jacuzzi, da alama ruwa ta sakar wa kanta , gabaki d’aya bata motsi gashi Jacuzzin ya cika taf da ruwa har yana zuba ga abun side d’in jacuzzin da ya faffashe a ‘kasa , ransa ba ‘karamun ‘baci yayi ba Sabida ‘bata lokacin sa da yayi, d’an ’karamun tsaki ya saki kad’an lokacin da yake ‘karasowa cikin toilet d’in , da hannu d’aya ya d’ago da ita cikin ruwan , Sabida yadda jikin ta ya saki gabaki d’aya baya tayi zata fad’i yayi saurin taro ta da d’ayan hannun nasa , d’aya daga cikin ‘bathrobe d’in cikin toilet d’in ya na d’a mata tare da d’aukar ta gabaki d’aya kamar wata Baby, babu Wanda ya kalla a cikin har ya kwantar da ita kan gadon d’akin, cikin Sauri Little ya ‘karaso wajan gadon ganin Lil d’insa bata motsi, kamar me rad’a ya furta sunan wata allura , Bobo dake bayansu jinjina masa kai kawai yayi ya juya , shima prince da uncle juyawa sukai suka bar d’akin, yayi saura Big Boss da ke tsaye lumshe da idanuwansa sai kuma Little da ya ‘kurawa Abla idanuwa shima kamar zaiyi kuka Sabida yadda eyes d’insa suka fara red . Cikin ‘kan’kanin lokaci Bobo ya dawo d’auke da wani ‘karamun kit ya mi’kawa Big Boss tare da allura da ya fad’a , shima little yana ganin allurar ya fara kulle eyes dinsa dan harga Allah baya san abunda zai ‘kara ta’bata , ganin yadda yake faman kawar da kaine yasaka Bobo kama hannunsa suka bar d’akın. Kusan 2 minutes yana tsaye a wajan be motsa daga inda yake ba , a hankali ya d’auko allurar tare da had’a ta yadda yake so , hannu d’aya ya kai Daidai saitin hancinta, yadda yaji nunfashinta baya fitowa ne yasa ya d’an matsa cikin ta kad’an batare da ya kalle taba , lokaci d’aya Abla ta fara fito da ruwa daga bakin ta tana tari , tun tanayi da ‘karfi ‘karfi har ta fara ajiyar zuciya kafun ta ‘kara fashewa da kuka tuno abunda ya faru, ko uffan be ce mata ba ya d’auko allurar zai mata , sai alokacin Abla ta farga, yadda ta gansa ne ya ‘kara firgita ta ga hawaye sun ‘bata mata face d’inta sosai , cikin muryar kuka ta furta � Ni banaso Dan Allah kar kayi mun allura � ta ‘karasa fad’a tana yarfa hannayen ta , be bi ta kanta ba ya ‘kara d’aga allurar zai yi mata ta ‘kara fashe masa da kuka , a wannan karan sosai ransa ya ‘baci, yadda take kukan ne ya ‘kara harzu’kashi, cikin tsananin ‘bacin rai ya daka mata tsawa , ita kanta bata san lokacin da ta had’iye kukan da take ba , sai idanuwa da take zazzaro wa , har ya gama allurar bata sani ba sai da ya zuba mata rikitattun idanuwansa masu ladaftar da mutane , cikin kausash shiyar murya ya furta � Just 10 minutes na baki ki sakko , idan kin isa ki ‘kara even a minutes �. Yana Kai ‘karshen zancan sa ya bar d’akın. Da kallo Abla ta bishi har ya fice daga cikin d’akin ga hawayen ta har lokacin ya ‘ki tsayuwa , ganin time d’in da ya bata ya fara yasa cikin sanyin jiki ta koma ta watsa ruwa tare da saka wata doguwar riga me kauri Sabida sanyin da take ji a cikinta .
Chapter 122 · 0% Book details