Sashe 76
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
***** 10:10am gabaki d’ayansu suka fito cin abinci kamar had’in baki banda big boss da tunda ya shiga part d’insa be fito ba har yanxu , ko wannansu sanye cikin ‘kananan kaya , James yayi serving d’insu favorite food d’in da suke san ciki, tunda suka soma cin abinci babu Wanda yayi magana , lokaci zuwa lokaci wayar bobo tana haske kusan sau uku batare da ya kalli wayar ba , a karo na hud’une wayarsa ta fara vibrating kamar bazai d’auka ba har uncle yayi magana , “Dr Eli� shine sunan da ya fito kan wayar sa ga uban text d’in da ya gani da sunanta shima , mamakin kiran ne yasa ya d’aga , banji me aka ce masa ba sai mi’kewa tsaye da yayi yana furta � oh shit�. am coming � yana kai karshen zancansa ya kashe called d’in, kallan uncle da yake shirin magana yayi � sorry uncle zanje na duba wata patience� lokaci d’aya prince da little suka had’a baki Wajan furta � patience ?� Shima uncle cike da mamaki ya furta � patience ? Bobo ? Dagaske kake ?� Kansa ya d’anyi knodding kad’an � yes patience�.� Ai be ‘karasa ba little yayi saurin furta � please yaya zan bika� shima prince yayi saurin furta � yes nima yaya please zan bika� tsayawa kallan ikon Allah bobo yayi musamman little da yaga sai faman murmushi yake , shima uncle a d’ayan side d’insa murmushi yake saki shi kad’ai , d’an harararsu bobo yayi zai yi magana little yayi saurin furta � please karka ce no dan Allah�, yadda ya fad’a in a cool voice ne ya saka bobo kara harararsa � let’s go� shine abunda yace , little har da buga wani tsalle kamar ‘karamin yaro , � Hey ba inda zakuje , ku zauna kuci abincin ku� narai narai little yayi masa sai kuma ya kalli direction d’in uncle , prince ma direction d’in uncle ya kalla tare da ‘kif ‘kifta masa ido , wani murmushi uncle ya saki me sauti yana kallan bobo � tunda mara lapiya zaku gani why not ka tafi dasu tunda suna san zuwa� kallan yadda suka sunkuyar da kai bobo yayi kafin ya furta � Okay let’s go� daga nan be ‘karacewa komai ba ya nufi hanyar fita suma cikin sauri su little suka bi bayansa , little har da kashewa uncle ido d’aya , shima uncle d’in ido d’aya ya kashe masa yana sakin murmushi. Babbar farar BMW IX 1 Robert ya d’auko , ga wasu jerun combo cars ba’ka’ke guda bakwai da sojoji suka fito dasu, little back seat ya shiga abunsa shi kad’ai , bobo da prince Suka zauna a tsakiya Sabida kujeru shida ne a cikin motar , biyu a farko , biyu a tsakiya sai guda biyu a baya, tunda suka shiga cikin motar babu Wanda yayi magana kowa phone d’insa yake dan nawa sai time to time suke d’an magana, kusan tafiyar mintuna goma sha biyar sukai kafun su canza kwanar tafiyarsu zuwa wani direction d’in daban, Daidai wani madaidaicin gida motocinsu sukai parking gabaki d’aya sojojin suka fito suka zagaye motar da su little suke cika , Robert ne ya bud’e musu mota suka fiffito, wayar hannunsa bobo kawai ya danna ko mintuna d’aya cikakkiya ba’ai ba aka bud’e ‘kofar gidan da sukai parking, farar baturiyar jiya ce ta fito tare da nuna musu hanyar shigowa ciki, gabaki d’aya sojojin a waje suka tsaya, a maimakon su tsaya waje d’aya sai suka zagaye gidan gabaki d’ayansa , Robert kuma ya bisu cikin gidan , Daidai kofar bakin falour shima ya dakata su bobo suka shiga , madaidaicin falour ne da babu tarkace ko hayaniya a cikinsa gidan shiru kamar babu wani me rai a ciki , amma ko ina tas tas yake babu datti, kan kujerun suka zauna , prince da little sai faman kallan falourn suke a fakaice suna san ganin mara lapiyar , Dr ElI tana ‘ko’karin kiran me aikinta bobo ya dakatar ta ita alamar ta zauna , � where is she?� Cewar bobo, � tana d’aki � dr Eli ta bashi amsa tare da gyara zamanta sosai � But tana cikin wani hali sosai, idan ba’a cire mata damuwar dake zuciyarta ba zata iya kamewa da ciwan zuciya , ko ciwan damuwa, Lokaci zuwa lokaci tana girgita tana fad’in wasu word da ni bana gane yaren da take cewa, gabaki d’aya taki sakin jikinta har magani ta’kisha , habincin da aka kaimata bataci, danai forcing d’inta kuma ta dunga amanshi kamar bata saba cinsa ba , and now fever d’inta ya tashi sosai taki ‘kula kowa balantana ashawo kan problem d’in , seriously tana bu’katar ta kwantar da hankalinta sabida kwakwalwarta tana neman ta’buwa and yes binciken da nayi tana faman da stomach ulcer Sabida rashin cin abinci da batayi�.. tana kaiwa nan Dr Eli ta dakata da bayanan ta , juyawar da bobo zaiyi yaga yadda fuskar Little tayi wani irin mugun ja lokaci d’aya , saurin dake kansa yayi sam ya manta da little yazo da bazai ta’ba bari Dr Eli tayi masa wannan bayanin agaban little ba , dukda yadda gashin sa ya rufe masa ido zaka fahimci kuka yake sanyi , prince ma duk da besan ko wacece ba sosai tausayinta ya fito akan face d’insa , kujerar da bobo yake kai ya Tashi tare da zama akan kujerar little , yadda ya dunkule hannun waje d’aya ne yasa bobo ya kama hannun a hankali ya fara murza masa hannun, Dr Eli bata fahimta ba shiyasa tayi ‘ko’karin cigaba wa Amma bobo yayi saurin dakatar da ita .� Hey calm down! Kwantar da hankalinka!� A hankali little ya d’aga masa kai muryarsa har disashewa take wajan furta � yaya bobo inaso na ganta� shima bobo kansa ya d’aga masa � zaka ganta amma sai ka kwantar da hankalinka ,okay?� Yes please yaya bobo , ina so Nima na ganta , she need our help plx ko sau d’aya ne� cewar prince shima dukda besan akan wa ake magana ba lokaci d’aya yaji yana san yaga yarinyar, kallan Dr Eli bobo yayi kafun ya furta � zaki iya nuna mana inda take ?� Da Sauri ta furta � yes why not � tana mi’kewa tsaye , kai tsaye d’akin da yake cikin falourn ta nuna musu, har yanxu hannun little yana cikin na bobo ya ri’ke masa , a hankali Dr Eli ta tura kofar suka shiga ciki, kwance take a ‘kasa ta juyawa kofar shigowa baya , sosai ta takure jikinta waje d’aya dukda ba’a iya ganinta sai scarp d’in kanta ga ba’kar coat d’in jiya da haryanxu ta ke ri’ke da ita , motsin da taji ne yasa tayi sauri zabura tana juyowa baya , sosai fuskarta ta fad’a kamar wacce tayi shekara tana rashin lapiya ga haskenta da ya sake fitowa sosai , ja dabaya ta somayi fuskarta har d’an kunbura tayi sabida yadda tayi kuka ga idanuwanta da suka kumbura ko bud’esu bata sanyi , yadda taga sun tsats tsareta da ido ne yasa ta ‘kara jin tsoro ya kamata musamman bobo da ta gane shi, suna shigowa cikin d’aki ta ‘kara ja baya sosai tana binsu da kallo, sosai little da prince suke kallanta musamman yadda sukaga tana Jan baya, jikinta sanye yake cikin simple riga me d’an kauri sai cap din kanta da gashin goshinta ya Fito sosai, akan wata kujera bobo ya zauna yana fuskantarta ganin yadda hawaye ke zubo mata sosai a fuska gashi ta takure waje d’aya tana kallansu , bakinta har rawa yake wajan furta � Dan Allah kuyi hakuri� tana kai karshen zancanta ta sunkuyar da kanta tana shashshekar kuka , gabaki d’ayansu babu Wanda be shiga shock ba yadda tayi magana , ‘karin mamakinsu ma yadda tayi Hausa , shiyasa little suka kalli junansu, dan shi little tunda yake a rayuwarsa bai ta’bajin wani yayi Hausa ba , bayan yan gidansu hatta big boss bazaice ga ranar daya ta’bajin Hausa a bakinsa ba tunda yake dashi kuwa , “kinajin Hausa ?� Little ya fad’a mamaki fal ransa , itama da mamakin ta d’ago kunburarrun idanuwanta ta d’orashi akan little haka kawai taji ta yadda bazai cutar da ita ba “gashi kyakkyawa� tafad’a cikin zuciyarta , ita kanta tana mamakin yadda akai ya iya furta Hausa � may be a wani wajan yaji� ta ‘kara nanatawa a zuciyarta , shi little gabaki d’aya sai yaji wani irin farin ciki ya kamashi lokaci d’aya da yaji tana Hausa shiyasa ya ‘karaso Inda take zaune a ‘kasa shima sai ya zauna yana bin fuskarta da kallo , abun mamaki bata ja baya ba ita ma, yadda yake murmushi ne yasa ta tsaya tana kallansa , a hankali ya furta � ya sunanki?�, bobo kam ya kasa motsawa ma , ganin ta saki jikinta da little , har yanxu kuma yana mamakin yadda little yayi mata magana a saninsa little baya ta’ba sakewa da Wanda be sanshi ba shiyasa abun ya d’an basa mamaki, � Ibtissam� cewar Abla tana kallan little , � yar rainin hankali tana magana ni na tanbayeta tamayar dani d’an yankan kai ?� Cewar bobo cikin zuciyarsa , murmushi little ya saki me sauti kafun ya nuna kansa � Ni sunana little� sai kuma ya nuna mata Prince da shima sai murmushi yake sakar mata � wannan sunanshi yaya prince � again ya nuna bobo � wannan kuma sunan shi yaya bobo� kallan bobo tayi kasa kasa kafun ta kalli little da yake mata murmushi, cikin kasa kasa da murya ta furta � bayashan jini?�, lokaci d’aya little da prince suka kyalkyale da dariya � wai yaya bobo ne me shan jini , toh idan taga big boss kuma shugaban ‘kungiyar masu shan jini zata ce kenan cewar prince cikin zuciyarsa , bobo tsaya kallansu kawai yayi ganin farinciki shinfid’e kan fuskarsu musamman little da kullum yake so yaga murmushi akan face d’insa , girgiza mata kai little yayi � Yaya nane fa , bayashan jini�, kanta Abla tayi knodding � kayi hakuri , na d’auka yana shan jini�, shikenan na hakura , amma ne yasa kika ‘kinshan magani? Ko bakyaso ki warke ?� Wasu hawayene suka soma gangarowa Abla