← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 146

Sashe 7

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

3:00am nayi ko munti d’aya be gotaba aka bude kofar shirgin da aka kulle Abla, Zinariyya ce tashigo sai tangad’i take Ganin yanda Abla bata motsine yasa Zinariyya sanar da Uwar karuwai, umarni ta bada Akawo mata ruwa masu sanyi a fridge guda biyar, hakan kuwa akayi cikin d’an karamun roba Zanariyya ta juye ruwan masu bala’in sanyi. Dakin shirgin suka nufa ita da Zinariyya sai wata da ake cewa Yar shila , a yadda zinariyya ta barta a haka sukazo suka sameta, kar’ban ruwan uwar karuwai tayi cikin rashin imani ta juyewa Abla shi a jikinta.A gigice Abla ta farka tana Ambatan sunan Allah , gabaki d’aya jikinta rawa ya d’auka sabida wani irin sanyi dayake ratsa jikinta, kallanta uwar karuwai tayi a wulakance � ku tashi ku fara aikin da kuka saba dan ba Hutu ne ya dace da kuba, matsiyata kawai�, tana kai karshen zancenta ta kalli ‘Yar shila � jeki taso mun ragowar tsinannun yaran, lokaci kankani na baku su kammala ayyukansu, idan ba haka ba ku zanesu suji a jikinsu � tana kai karshen zancanta tayi waje , a duniya idan akwai wacce ‘yar shila ta tsana be wuce Abla ba , shiyasa uwar karuwai na fitowa taja ta kamar kayan wanki , Daidai lokacin da Zinariyya ta fito dasu Anee suma ko wannansu a jike sai rawar sanyi suke . Cikin kuka arwa ta karaso Inda Abla take ,”Abla sanyi nake ji , ga yunwa ina ji, ga bacci da be isar mu, jikina duk ciwo yake mun ga wasu cunnaku dasuka cijeni �, kwallarta Abla tayi saurin gogewa � wata rana sai labari, kafun su dawo ku tashi muyi aikin mu ko zamu samu in lokacin sallah yayi muyi kafun musamu na abincin, kunsan idan bamu kammala ba, bazasu ta’ba bari muyi sallah ba� gyada mata kai sukayi gabaki d’ayansu,Babban falon da ya baci da kwalaben barasa da abubuwan sigari suka fara gyarawa , gabaki d’aya falon wari yake amma duk da haka sai da suka gyara shi tsaf sai faman haki suke sabida galabaitar da sukayi, d’akuna Biyar da suke jere a kasa ko wannansu ya nufi d’aya da niyar gyarawa, d’akin da Abla ta shiga wani irin amaine ya taso mata sabida kazantar da ta dunga cin karo dashi a dakin, gabaki d’aya d’akin a har gitse yake , da kyar ta Samu ta gyara d’akin kafun ta nufi toilet. Tana shiga aman da take rike wa ne ya kwace mata Sabida karo da ta dungaci dasu condom gawani uban Kazan tar dake cikin nan dakin, da kyar ta samu ta wanke ban dakin, tana fitowa sai da ta jira su Husna suka fito Suma , ko wannan su a waji gace sai faman toshe hanci suke, sama suka nufa shima saida suka gyara falon tass da ya fi na kasa baci kafin su gyara rooms din cikin falon, lokacin da suka gama wani irin juwace ta soma kamasu ga kiran sallah da ake faman yi amma badamar suje suyi.Inda kwanukan wanke wanke suke suka nufa, sosai an ‘bata kwanuka haka suka zauna suka fara wankewa, sai wajan 8:30 na safe suka kammala wanke wanken, Dole su gyara kitchen din gidan ga tsakar wajan da zasu gyara shima , ga lokacin sallah na tafiya, murya a dusha she da ‘kyar take magana ta furta � Lokacin sallah na tafiya , ya kamata muyi sallah � a tsorace suka kalleta gabaki d’aya � Abla kinsan hukuncin da zasuyi mana idan suka san munyi sallah ko�, manyan idanuwanta Abla ta saka musu,� kuna nufin mu zauna karmuyi sallah sabida hukunci �, da Sauri duk suka d’aga mata kai kamun ilham tafurta � sai muyi sallar daga baya danni tsoron muguntar su zinariya nake �, same Arwa ma abunda ilham ta fada shi ta maimaita, Anee ce ta kalleta � Abla Nima zanyi sallah , Taho muje �, kallan Husna Abla tayi ko zataje amma ko kallan inda Ablan take batayi ba, a d’arare Suka samu suka fita daga cikin gidan, saida sukai tafiya me Nisan gaske kafun su samu wani masallaci da suka ga butocin ciki da ruwa, Alwala suka samu sukayi kafun Suje bayan masallacin su tayar da sallar su, suna idarwa tsoran hukuncin da za ayi musu ya kamasu. Cikin fargaba suka nufa Gidan, tsallan kwado suka tarar ansaka ilham da arwa , fuskarsu gabaki d’aya ta baci da hawaye, yar shila tana ganin su Abla ta rufe su da duka da wata jungegiyar doruna,kafin suma akasu tsallan kwad’an, tun sunayi da karfin jikinsu har suka somayi a hankali kafun su fadi a kan tiles din suna nun farfashi, yar shila ta daga hannu zata kara zuba musu wani bulalan uwar karuwai ta fito cikin wankanta da kallo d’aya zaka mata kasan cikakkiyar karuwa ce, � ya isa haka yar shila so kike ki kashe mun kasuwa ne , ga kosai can ko wanne ki basa guda bakwai kafun ku basu wankin da aka had’a kunsan yau akwai casu, ko bara banaso suje yau sabida akwai aiki”tana kammala zancanta tasa kai ta bar gidan, kosan yar shila ta dakko amaimakon ta basu kamar yanda aka umarceta sai ta bawa ko wannansu biyar biyar, tana zuwa kan Abla ta Wulla mata guda uku ba kamar sauran ba, Husna ce kawai babu a cikin falon, ayun wace suka fara cin kosan da ko rabin cikinsu be zoba , banda abla da take bun kosan da kallo, tayi wa kanta alkawari bazata kara cin abinda ya fito ta kazamun hanya ba , shiyasa ta rabawa su arwa kowa daddai, harda murnarsu suka amsa kuwa kafun a tulo musu uban wanki me shegen yawa, basu suka kammala ba sai wajan 2:30, anan ma satar hanya ilham da Abla sukai sukaje sukai sallah suka dawo , a wannan karan Allah ya temakesu ba aga dawowarsu ba, har lokacin su Arwa kuwa basuyi ko sallahr asuba ba duk yadda Abla take musu magana har ta gaji . Wata iriyar masifaffiyar yunwa suke ji , Ga uwar karuwai ta hana su zuwa baran da suke nemo abinci, La’asar nayi Abla takara guduwa wannan karan itama ilham bata bita ba. Tana idar da sallah ta ta’be jikin masallaci ko zata Samu sadaka amma har tagama bulayinta bata samu ko biyar ba , shiyasa ta nufi hanyar komawa gida abunta, tana shiga ta tarar da abunda ya tada mata hankali, da sauri ta karasa Wajan su tana tanbayarsu ina zasuje da wannan shigar, Anee na kuka ta soma magana � Abla nagaji, bazan iya rayuwar yunwar nan ba, idan na kara awa d’aya banci abinci ba mutuwa zanyi , shiyasa na yadda da bukatar su Zinariyya, Sunce ba sex zasuyi damu ba, wasa ne kawai zasuyi, kuma zasu dunga biyan mu�, A firgice Abla ta saka salati � Innalillahi wa inna ilaihi raji’un,me kuke kokarin yiwa rayuwar ku,bakusan hakan wata Babbar illace ba arayuwar ku, me zakucewa mahaliccin ku�, a kufule Husna ta kalleta� Ya isheki haka IBTISSAM, ke komai kinfi kowa sani, ko ca’akai miki mu bamu da addinin ne, kullum mutum zai yi abu sai kin kawo naki, idan muka zauna da yunwa zaki bamu abincin da zamu dunga cine,ko zamu zauna kina hanamu abu yunwa ta kashe mu, na dad’e da fahimtar dama ba san cigaban mu kike ba , in baki sani ba ki sani yau bazan kara zama yunwa ta kashe niba , Nima dole na samu kudi, ga hanyar samun kud’i cikin sau’ki , idan ke bakya san rayuwar ki to mu muna so � tana gama maganar ta taja dogon tsaki tayi wucewarta, Arwa da Anee ma bin bayanta sukai, ilham ce kadai ta Matso kusa da Abla � kuncin rayuwar nan ta ishe mu Abla , Bamu da gatan da ya wuce mu samowa kan mu ‘yancin kai, bazan iya rayuwa cikin yunwa ba, duk da bamu dad’e da sanin juna sosai ba amma tabbas ke din Ablan muce me Kaunar mu, kin nuna mana soyayya irin yanda yaya take nuna wa kannanta� itama tana kai karshen zancen ta tabi bayansu Husna , zubewa Abla tayi a kasa tana faman nanata sunayen Allah, babu abunda bakin ta yake furtawa sai � Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un� wannan masifa har ina,batasan lokacin da wani kukan ba’kin ciki ya kwace mata ba.

✨✨✨✨�
✨✨✨✨✨✨

UNITED STATES
Chapter 7 · 0% Book details