← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 146

Sashe 83

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

****karfe 8:30pm gabaki d’aya suna falourn ‘kasa har Abla da little yasaka tafito dan dole , ko wannansu yayi wanka ya canza kayan jikinsa , yau uncle yana d’akinsa daga little sai prince sai kuma Abla da take sakar musu murmushi, yadda suke fara’a sosai kamar a tsakaninsu mutum zaiyi tunanin yan uwane gabaki d’aya musamman yadda suka dage wajan sakata murmushi. Little agaba gaba Wajan bata labarin dariya, sosai ta sake dasu kuwa itama tana basu labari sai faman dariya suke yi abunsu, sallamar bobo ne ya katse musu hirarsu da Sauri little ya ‘karasa wajan da yayi hugging d’insa � welcome back yaya bobo� zaka karya nifa� cewar bobo ganin yadda little ya d’anesa , � welcome back yaya bobo�, shima hannu bobo ya daga musu kafin ya kallesu gabaki d’aya � gaskiya fa kun canza yau bakuyi futunawa� saurin rufe idanuwansa little yayi � Haba yaya bobo� kunnansa bobo yaja � ba gaskiya na fad’a ba?� Da Sauri little ya amsa � gaskiya yaya amma ynxu ai zamu dena tunda muma muna da sister� sai a lokacin bobo ya kalli Abla da take wasa da kyanta , a hankali ta furta � sannu da zuwa� cikin sakin fuska itama bobo ya amsa mata � Yawwa kanwar little� hau wani sautin dariya zakaji little yana yi sabida ya zama ya ya shima, bobo bai zauna a falourn ba ya wuce part d’insa . Sai wajan 10pm bobo ya fito ganin basu kwanta ba,� you guys baku kwanta ba har yanxu ? Babu ruwana idan yayanku ya dawo� little zai shagwa’be masa fuska bobo yayi saurin furta � Nidai babu ruwana, you guys ya kamata ku kwanta especially kai da sister d’inka tunda baku da lapiya , kana yin musu kuma zan kirawosa yanxu�, haba mana yaya just one hour more � cewar little amma ganin bobo na ‘ko’karin daukar phone dinsa little yayi saurin furta � shikenan yaya zamu kwanta yanxu , good night, sister taso na rakaki d’akinki � ba musu kuwa ta bisa , har d’aki ya rakata ganin dare beyi ba sosai yasa kawai ya kunna mata Tv acewarsa idan ta gama kallo sai ka Tashe light din. Shima direct basu kuma zama a falourn ba suka nufi part d’insu shida prince . Bobo yana zaune a falourn yana jiran dawowar Big boss amma har wajan ‘karfe 12 na dare babu big boss babu alamarsa , yau a gajiye ya dawo shiyasa ya nufi d’akin su little dan ya dubasu, lokacin gabaki d’ayansu sunyi bacci , hatta uncle da ya shiga d’akinsa bacci yake shiysa ya rage fitilin falourn ya nufi part d’insa, har wajan karfe 2 na dare na jiran tsammanin dawowar big boss , har bacci ya d’aukesa sabida yadda ya gaji.
3:30am motocin Big boss suka danno kai cikin gidan , a wannan lokacin yasan gabaki d’aya sun kwanta shiyasa be wuce part d’insa ba saida ya duba lapiyarsu dukda shima yau a gajiye ya dawo cikin gidan sabida headache din da yake fama dashi ga idanuwansa da sukayi mugun red sai faman lumshe su yake .

WASHE GARI

Ana kiran sallar asuba gabaki d’aya suka fito falourn , yau abun mamaki kowa ya fito kamar yadda suka saba fitowa amma banda big boss , sun dad’e suna jiran fitowarsa amma basu ganshi ba , little har ya damu yana ‘kokarin zuwa part d’insa bobo ya hanasa sabida sallah da ake ‘ko’karin yi , haka gabaki d’ayansu suka nufi masallacin banda shi , dan kuwa abune me matukar wuyane xai hana sa fitowa kowa kuwa rashin lapiya yake yana fitowa sallah dukda shima rashin lapiyan da wuya su gane bashi da ita . Ana idar da sallah tun kafin kowa ya fito daga masallacin bobo ya nufi part d’in Big Boss dan yasan ba lapiyar sa kalau ba tunda be fitowa sallaba, yana shiga part d’insa ya kulle door din ta ciki ta yadda ko su little sun saka turn print d’insu bazai bud’e ba, gabaki d’aya ko ina da duhu , cikin Sauri bobo ya tura ‘kofar bedroom d’insa da yaga alamar hasken fitula, yadda yaga Big boss a zaune ne yasa yayi saurin ‘karasawa inda yake , yana kokarin ta’basa big boss yayi saurin hankad’asa baya � don’t touch me� shine kadai abunda ya iya furtawa, Bobo bai damu ba yakara yunkurin ta’basa big boss yayi saurin bige masa hannu, Allurar da yagani akan center ne yasa gabaki d’aya mamaki ya kamasa , xai d’auki allurar big boss ya ‘Kara bige masa hannu, wata allura ya janyo xai yiwa kansa bobo yayi saurin ri’ke hannunsa sai alokacin yaji yadda jikin Big boss yayi mugun zafi, zai ta’ba masa goshi big boss ya kara bige masa hannu , cire hannun bobo yayi yana ‘ko’karin yin allurar cikin Tashin hankali bobo ya kai hannu zai fusge amma ina tuni big boss ya yi allurar , cikin Sauri Bobo ya fita daga d’akin, be jima ba ya dawo d’auke da babban ruwan roba me shegen sanyi, gashin big boss gabaki d’aya ya rufe masa fuska a Bobo na kokarin ta’basa big boss ya hanasa hakan , tunda ya sunkuyar da face d’insa kasa be katta dawo da ita ba sabida yadda jijiyoyin wuyansa suka tashi sosia , idanuwansa sunyi jajawurrr ba kad’an ba , lokaci bobo ya kalla da Sauri ya bude ruwan nan duk da yadda yake da mugun sanyi haka ya fara tuttulawa big boss akansa�..

PAY YOUR MONEY INTO 2681892316, Aisha umar zenith bank sai a turo shardar biya ta wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee �

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to the besieged😭😭.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1

SORRY FOR THE TYPING ERROR BANYI EDITING BA!!👏👏�

S____23💞
Chapter 83 · 0% Book details