← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 146

Sashe 31

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Babban farin gidane me shegen kyau da tsaruwa, kowa yasan yadda tsarin gidan turawa yake musamman idan aka shigo fadar shugaban ‘kasa , anan ma hakan ce ta faru sabida tsaruwa da haduwa da White House yayi, ga securities da sojoji ta ko ina musamman da ya kasance His excellency Mr president yananan, ko ina ka waiga zakaga soja Sabida irin had’uwa da tsaran lapiyar sa data ilayinsa da ake baki d’aya .
A cikin ‘kayataccen falourn da zai tabbatar maka da dukiyar da take kuka a ciki, his excellency Vice president ne zaune kan kujera yayi crossing legs d’insa hannun sa d’aya ri’ke da wani had’ad’d’an kofin coffee da yake sha. Bud’e ‘kofar da akai ne yasa vice president yayi saurin ajje kofin hannunsa tare da mi’kewa tsaye lokacin da yaga shigowar mr president, yana shigowa masu tsaransa suka dakata Amma duk da Hakan kana iya hangosu. Farin bature ne kana ganinsa zaka ga haifaffen d’an America, a shekaru kuma bazai haura 60 years ba , bayan sun gaisa sosai sai Vice ya kalli president cikin girmamawa duk da yabada umarnin kar Wanda yashigo tunda tattaunawar sirri zasuyi Amma duk da haka matsu tsaransa suna kallansu ta camera maganar da suke fad’a ne Kawai basaji, � your excellency sir , maganar Nicholas ne �, kasancewar da turanci suke magana ,jinjina masa kai Mr president yayi akan yaci gaba da magana � it’s about Nicholas da ya ‘bata a New Zealand, bawai dagangan ‘batan yayi ba sir , d’aukesa akai intentionally �, yanxu ma cike da wani mulki Mr president ya kallesa, � kayi magana da president d’in New Zealand ? �, yanxu ma cike da girmamawa VC ya cigaba da magana � your excellency basu da hannu aciki, asalima nasan yana hannu wa �, suite d’insa Mr president ya d’an ta’ba � and ?shine kazo kana fad’amun bayan kasan inda yake ?�, your excellency nayi ‘ko’karin hakan but duk ya tashi in vain, maganar kace kad’ai zaisa ya sako su because na Samu complain har da yaran mayor da governor New York ya kama yaransu�, rai a d’an ‘bace mr president ya furta � what’s this nonsense ? Na bada kwana d’aya koma wanene ya kamasu ya gurfana sannan ya dawo da duka yaran �, Mr president na kai ‘karshe Vc ya d’ora da � yana da taurin kai sir na tabbata maganar ka Kawai zaiji �,you as my Vc bazaka iya ba kenan ? Then Menene anfaninka �, sorry sir cewar Vc, Mr president be kuma cewa komai ba tsawan mintuna d’aya kafin ya bud’e bakinsa � ina bu’katar ganin chief nan da 2 d’ays sannan ko wanene inasan a gurfanar mun dashi sannan akarbi mu’kamunsa,� shi Vc ba wannan ne abunda yafi d’aga masa hankali ba , yasan idan his excellency yasan wanene zai iya bin goyan bayansa amma duk da haka ya zama dole ya fad’a masa tunda big boss kamar d’a ya d’aukesa � Big boss ne �, cewar Vc , kallansa mr president yayi lokaci d’aya kuma ya saki murmushi me d’an Sauri da har saida Vc ya kallesa �, kana nufin kace my son shine ya kama Nicholas ? Lefin me sukai ?�, shiru Vc ya kasa basa amsa , ynxu ma murmushi me sauti his excellency ya saka tare da mi’kewa tsaye � nasan ko wanene Son dina , kome zaiyi saida dalili inkaga ya shiga abu toh tabbas ankaisa ‘karshe , zanyi magana dashi , nan da 1 week ina bu’katar tattaunawa ta musamman, bana bu’katar ganin kowa sai iyayen yaran , chief sai masu hannu a case d’in,zanyi wa son magana da kaina �, yana kai ‘karshen maganar sa ya bar falon bayan securities sun bud’e masa door , Vc ma kofar da zata futar dashi ya nufa ba wacce his excellency ya fita ba yasan daman za’a rina , bazai yi wani mistake ba yasan falourn cike take da CC Tv , rai a’bace yabar White House a wannan karan yana ji aransa dole ya karbo d’an sa ko zaiyi anfani da mu’kamun sa na vice president of the United state, dalili d’aya ne yasa yake bin komai a sannu ya tabbata kome zeyi president zai d’aga masa kafa amma ban da abunda zai ta’ba big boss , ya rasan basu da ala’ka Amma yadda yake bun goyan bayan Big Boss da komai da ya shafesa kamar d’an sa yafi komai jijjigasa.

***** His excellency kai tsaye inda zai sadashi da ilayinsa ya nufa , lokacin da ya shiga masu tsaro sai faman gaishesa suke dukda babu me kuskuran d’ago da fuskarta ya kallesa , wata baturiyar matace ta fito daga wani ‘kofa kana ganin fuskarta zaka ga damuwa kwance a kan fuskarta duk da yadda Hutu da jin dadi ya ratsa farar fatarta musamman yadda take sanye da ‘kananan kaya a jikinsa , gashin kanta da ya sha gyara sai faman yawo yake a bayanta ,tana ganin president Sukai hugging junna, shima sai yayi pecking goshinta � me ya faru naga fuskarki ta sauya ?�, cike da damuwa matar ta furta � Alice ce , har yanxu ta saka damuwa a ranta , ko abinci bata san ci, I can’t take it, you’re the president of the whole u.s , you have to keep my daughter in happiness kome take so ayi mata shi ko zai sa ran wasu ya ‘baci, daman momy Alice haka take indai abunda zai ta’ba Mata daughter d’inta kwalli d’aya ne ta gwammace ran kowa ya ‘baci Indai yarta zata Samu abunda take so and bata ta’ba Gaza mata ba sai a wannan karan da ta kasa bata abunda take so, “I will check on her �, cewar sa tare da shiga inda ta fito, nan ma wani kayataccen wajene na gani na fad’a ga masu tsaro burjic a wajan , d’akin Alice ya nufa nan ma sosai d’akin ya gaji da had’uwa , kwance take kan kayataccen gadon ta tayi rubda ciki ba’a iya ganin fuskarta sai santala santalan fararan cinyoyinta da suke sanye cikin wani d’agaggen wando da ko cinya be kai mata ba sai yar fingilar rigar jikinta da bata rufe mata ‘kugunta ba, cikin voice d’inta ta furta � mom , nace kawai ki futa , baba bukatar ganin ki ,just go out �, shiru be amsa mata ba sai ma zama da yayi a gefenta, rai a ‘bace ta d’ago face d’inta ,Wanda ta ganine yasa tayi hugging d’insa � Dad , please ku aura munshi, I can’t leave my life without him dad, nasan zaka iyayin komai ,inaso wannan ma ka mallakamun shi, ina san shi please �, gashin da ya rufe mata fuska ya gara mata, ba mummuna bace , Daidai gwargwadan kyau tana dashi musamman yadda take kashewa skin d’inta kud’i shiysa ta karayin kyau� it’s okay , banasan kina saka damuwa aranki , nasani 1 day one time he will marry you, and kece kad’ai zaki zama matarsa like your mom �, pecking dinsa tayi a goshi � plx dad , kasa ya aureni ina san shi tun lokacin da na fara ganinsa, inaso ni ko yanxu kasa ayi mana aure �, dariya ya saki me Sauti � kinsan wanene Wanda kike so ki aura fa , do you think irin mutanan da ake wa aurene just like that?nan da 1 week zamuyi wani meeting and zansa ku had’u ,just you have to convince him with your love , okay ?�, yes dady ta fad’a tana turo baki � oya ki tashi ki shirya �, yes dady ta fad’a , wani pecking dinsa ta karayi a kuma tu shima hakan yayi mata yana fita ta mi’ke tsaye dogon gashin kanta da yasha gyara ya sakko mata a bayanta, sai yar filgilar rigar ta da ko cibiyarta bata rufeba , ga Santala santalan kafafunta da Suka fito cikin dan mitsitsin wandon jikin ta, Inda jerin beers d’inta suke ta nufa , cikin wani d’an karamin glass cup ta zuba giyar tana sha a hankali cike da yanga , a hankali ta furta � My Big boss , na matsu na ganta, I just want to see you in my arms, ni kad’ai ce matar da akayi maka, and babu wacce ta isa ta zama mallakinka sai ni , idan ba haka ba sai na kasheta,ko ma wacece, I’m Alice , babu Wanda ya isa ya Samu abunda nake so a duniya , ko me nayi niyar samu sai na sameshi, I can’t wait to hug you so tie �.

🍂🍂🍂🍂🍂

KANO
NASARAWA G.R.A
Chapter 31 · 0% Book details