← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 146

Sashe 127

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Da murmushi akan face d’inta ta shigo cikin gidan, gabaki d’aya mi’kewa sukai ganin face d’inta d’auke da annashuwa � Lil kin dena fushin yanzu ?� Cewar Little , kanta Abla ta Jinjina masa tana ‘kara sakar musu murmushi , shima da d’an mamaki Prince ya furta � Da gaske kike ?� Yanzu ma kanta Abla ta jinjina masa , shiru Little yayi kamar me tunani sai kuma ya furta � Amma zaki ci abinci idan muka kawo miki ko?� Kanta ta jinjina masa kafin ta bud’e bakinta � Yunwa nake ji Yaya Little � gabaki d’aya ta d’aure musu kai ganin lokaci d’aya annashuwar ta ya dawo dai dai ko kula da rashin school bag d’in ta basuyi ba . Tana shiga d’aki wanka tayi cikin blue d’in riga da wando palazzo, gashin kanta da yayi tsawo sosai , shima sai da ta gyarasa kafun tayi Rolling da peach d’in mayafi da ya ‘kawata face d’inta , wani half peach shoe ta saka a ‘kafarta , sosai shigar tayi mata kyau kamar ba Itace a cikin damuwa ba jiya . Yunwa take ji sosai shiyasa tana sakkowa suka nufi dinning , har yanzu basu dena mamakin yadda ta sauya ba lokaci guda , ‘dan marairaice musu face Abla tayi � kuzo mu fita yawo please � d’an zaro mata ido little yayi � yawa kuma Lil?� Kanta ta jinjina masa tana langwabar da kanta , � kawai futa zamuyi fa mu dawo, babu Inda zamuje � shiru Little yayi mata kamar ne tunani, prince zai yi magana little yayi saurin furta � shikenan Lil amma baza mufi 20 minutes a waje ba kin yadda ?� Da Sauri Abla ta � Eh na yadda � cikin Sauri prince ya furta � Baku da hankali ne ? Kunsan Yaya Big Boss da Yaya Bobo na nan fa ,� Haba mana Yaya prince bazamu dad’e ba just 20 minutes “cewar Little , girgiza masa kai Prince yayi � babu ruwana , kasan me zai biyo baya ai ko?”Little zai ‘kara masa musu Abla ta dakatar Dashi � Hakane fa! Yaya little karmu ‘bata musu rai kawai muje garden� cikin cool Little ya furta “kin tabbatar ?� Kanta Abla ta jinjina musu � yes kwana biyu ban ga simba ba � da haka Abla ta kashe maganar suka nufi wajan simba gabaki d’ayansu , yanzu ko tsoransa da take ji ma ta dena, sun dad’e a wajan simba kafun su koma garden , sai alokacin Abla tasan da karnukan Bobo, duk yadda Little yayi da ita su je wajan su ta’ki zuwa , ganin tana shirin guduwane ya hakura shima . Suna zaune a Wajan har sai da suka ji kiran sallar La’asar tukunna Abla ta dawo cikin gida , su kuma suka wuce masallaci. Yau gabaki d’aya jinta take kamar a iska , babu kunci , babu damuwa aranta , ko ba komai sun wanke ta daga cikin sharrin da akai mata. Rungume shi data Tuna tayine yasa tayi saurin rintse idanuwanta kamar wani yana ganin ta , a fili ta furta � Na shiga uku na , yanzu ya zanyi ?� Rashin samun mafita yasa Kawai ta ha’kura tayi sallar la’asar d’inta , tana idar wa ta tashi da nufin duba books d’inta, gabaki d’aya ta manta bata d’auko jakar taba sai da ta gama duba ko ina, kamar zatayi kuka ta koma ta zauna sai system d’in ta data kunna , Allah ya te make tama babu teacher d’in da ya shigo class d’in. Abla bata ‘kara fitowa ba sai bayan sallar isha’i, shima yunwa ce ta ishe ta , ga baccin da take ji yau da wuri , cikin d’an guntun kuzarin da ya rage mata ta nufi kitchen lokacin babu kowa , cornflakes ta had’a kad’an cikin cup sai yoghurt da ta d’auka guda d’aya ta dawo falourn, tana ajjewa tayi saurin komawa d’aki ta d’akko system d’inta , Wani Korea da ta fara kallo ta kunna tare da d’ora ta kan center yadda zata fi jin dad’in kallan ta , ta nutsu sosai tana kallan ta dan ba ‘karamun dad’i novel d’in yayi mata ba.
A hankali ya shigo cikin falourn, duk da babu fara’a akan face d’in sa amma ba a had’e take kamar kullum ba , kamar yadda ya saba shigowa tun da ya shigo be d’ago da kansa ba , muryar film d’in da Abla take kallo yana tashi sama sama , gabaki d’aya batasan da shigowar sa falourn ba sabida yadda ta nutsu sosai tana kallan ta , Daidai lokacin da jarumin film din zai yiwa jaruwar kıss Abla tayi saurin kifar da system d’in , jikinta har rawa yake , lokaci d’aya ta dafe saitin zuciyar ta , ta mi’ke da nufun komawa kitchen idanuwansu ya sar’ke cikin na juna , cikin Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa , � sannu da zuwa � cewar Abla, ta’be baki Big Boss yayi cikin husky voice d’in sa ya furta � coffee � daga nan be kuma tanka mata ba ya wuce part d’insa . Kallan hanyar da ya nufa tayi kafin ta ta’be bakinta kad’an � ni ina ruwana tunda dai ka ‘Karo mun hacci na , shine zaka dunga d’auran fuska , coffee , coffee , coffee � cewar Abla tana Kwaikwayar ‘karshen maganar ta , cikin Sauri kuma ta wanke cup din cornflakes d’in ta koma wajan coffee maker, har ta d’auko flavors d’in da Little ya koya mata sai ta idanuwanta suka sauka kan wani strawberry flavor da ginger flavor , da karan baninta ta had’a coffee d’in dasu, lokaci d’aya kuma ‘kamshin su ya ban ban ta da sauran Wanda take yi, da Sauri ta d’auki cup d’in ta nufi part d’insa , zuciyar ta fal fargaban abunda zai yi mata tunda ya hanata shigar masa part , ta fi minti d’aya a wajan gudun kar coffee d’in sa yayi sanyi ne tayi knocking falourn sa na farko shiru babu amsa , still ta ‘kara kwankwasa wa a karo na biyu babu amsa , ‘karfin hali tayi ta bud’e ’kofar tana ganin baya ciki ta nufi d’ayan falourn , shima sau biyu tana knocking ba’a amsa ba , da sallama ta shiga falourn sai kuma tayi saurin Jan burki ganin sa zaune kan d’aya daga cikin kujerun falourn , ga system d’insa da yake operating akai . A nutse ta ‘karaso cikin falourn Daidai Wajan center d’in ta rankwafa kad’an � ga coffee d’in� shiru bai kalleta ba balantana ta saka ran amsawa , a karo na biyu ta ‘kara furta � ga coffee d’in � nan ma shiru yayi mata kamar be san da zuwan ta ba , Yadda ya nuna kamar babu mutum a falourn ne ya ‘kular da ita , juyawa tayi da niyar komawa ya mi’ka hannunsa kad’an ba tare da ya kalle taba � My coffee !� A fakai ce Abla ta d’an harari side din da yake kafun ta juyo ta mi’ka masa coffee d’in, yanzu ma sai da ya gama shan ‘kamshi tukunna ya saka hannu ya kar’ba , ta juya zata tafi ya ‘kara furta � Come back � Abla kamar zatayi kuka haka ta juyo ta tsaya batare da ta kalli side d’in da yake ba , kamar da wasa taga ya kai cup d’in bakin sa , kad’an yayi sipping kamar me tsoran sha , ta d’auka zai mata fad’a sai taga ya ‘kara kai coffee d’in bakinsa a hankali yana sipping. A hankali ta saki a jiyar zuciya ganin yau ta tsira bazai mata punishment ba , ta fi tsawan 7 minutes tana so ya gama shan coffee d’in ko zai barta ta tafi sabida gabaki d’aya ta kasa sakewa , a hankali ya ajje cup d’in batare da ya furta komai ba, itama Abla ganin ya gama sha ne yasa ta d’auka da niyar komawar ta ‘kasa , tana juyawa ta kuma jin saukar muryarta � Coffee �,d’an ya mutsa face d’in ta Abla tayi kad’an kamar zatayi kuka dan yau sosai take jin bacci, cikin Sauri ta ‘karo had’a masa wani coffee d’in har lokacin su Little basa falourn , yanzu ma ta d’auka zai barta ta tafi sai ya ‘kara dakatar da ita , sai da ya mula dan kansa sannan yasha coffee d’in a karo na biyu, duk wannan abun Abla ta tsaye kamar zatayi kuka Sabida yadda ‘kafar ta ya gaji, a karo na uku ya ‘kara sa ta had’a wani coffee d’in , tun tana tunanin d’aukar abun da wasa har ta dena ganin sai da ta koma ta ‘kara had’a masa wasu coffee d’in, kafafuwanta gabaki d’aya ciwo suke mata sabida hawa da saukan da tayi gashi sama da awa d’aya tana tsaye ko zama be barta tayi ba , kamar ta ro’keshi akan ta tafi amma itama taurin kanta ya hanata magana yau sai kawar da face d’in ta da tayi kad’an kwalla har sun tarar mata cikin ido. Sai da ‘kara mintuna 25 a tsaye ga bacci ga cikin kafa amma ko kusa ya hana ta tafiya , Sai da ya tabbatar ya horata da tsayuwa kafun ya furta � get out � ko kallan inda yake yau Abla batayi ba tayi fitowar ta , � mugu kawai� cewar Abla kafun tayi sauri barin Wajan . Tana sakkowa ta tarar da Prince da little sai kuma uncle , � yanzu nake shirin kiranki sai gaki ma kin fito , ina kika je ?� A sanyaye ta furta � coffee na kaiwa Yaya Big Boss � cikin fara’a Little ya furta � sorry Lil nasan kin gaji ko?”Girgiza kanta kad’an Abla tayi duk da ta gaji amma ko kusa bata nuna musu hakan ba � No yaya Little ai ba wani aikin nayi ba , ko kuna bu’katar wani abune ?� Girgiza mata kai sukai � No Lil yaka mata ki huta haka tunda gobe kina da school , okay ?� Cewar uncle , jinjina masa kai tayi kafun ta furta � Tom uncle sai da safe � side d’in su Little ta kalla suma tayi musu sallama kafun ta nufi part d’inta .
Tana shiga d’aki ta fad’a kan gado sabida yadda taji ‘kafafuwanta suka ri’ke, tafi tsawan 10 minutes a kwance kafun ta iya zuwa toilet ta watsa ruwa ajikinta , lokaci d’aya abubuwan da suka faru d’azu suka dunga dawo mata cikin zuciya ta, tasan baya santa , baya ‘kaunar ta , baya san ganin ta a inda yake , amma kano na farko , mutum na farko daya ta’ba kwato mata martabarta ta ‘ya mace, baza ta ta’ba mantawa da hakan ba arayuwarta,tana cikin wannan tunanin bacci ‘barawo ya d’auke ta.
Chapter 127 · 0% Book details