Sashe 90
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kuma ya tufke ga wani irin tsuke face da yayi, sau d’aya ya kallesu gabaki d’aya suka sha jinin jikinsu, musamman kallan da ya jefa wa Abla , lokaci d’aya taji nutsuwarta na neman guduwa , kamar Marasa gaskiya suka shigo cikin falourn, diamond watched dinsa ya kalle dake tsintsiyar kyakkyawan farin hannunsa , a kausashe ya furta � just 15 minutes na baku kuyi sallah, if your dare ku ‘kara 1 minutes � ai be kai ‘karshe ba gabaki d’aya ko wannansu ya nufi part d’insa hatta Abla da hankalinta yayi mugun tashi, ko takan siyayyar da sukayi basu biba, sallah kawai suka idar suka dawo kusan a tare da ko minti d’ayan basu ‘kara ba . Wani irin mugun kallo ya jefa musu da gabaki d’aya sai da ‘ya’yan cikinsu suka kad’a , kamar had’in baki uncle da bobo suka fito Daidai lokacin, kallan babban yayi kafin ya furta � ku zagaye falourn nan sau 5 da gwiwowinku � cikin Sauri bobo ya furta � Haba mana big boss yayi yawa ba , jinjina na masa kai big boss yayi � sau bakwai zakuyi � shima cikin sauri uncle ya furta � plx big boss ka rage musu � rai a ‘bace ya furta � 10^�, bobo zai sake magana uncle yayi saurin dakatar Dashi dan suna ‘kara magana zai ‘kara yawan punishment din nasu , haka suka fara zagaye falourn tun a round 3 suka fara had’a gumi kuma ba daman suyi kuka ,Abla ma sosai ta jigata kamar zata kife daman sai da bobo yace musu karsu dad’e gashi bata Kai wancan aljani simba din abinci ba , yana zaune kan kujera suka cigaba da crolling gashi ba damar su bashi hakuri saida sukayi round 10 d’innan, suna gamawa kuwa suka zube gabaki d’ayansu, hannu d’aya big boss ya mi’kawa little , cikin Sauri ya fara zazzare idanuwa lokacin daya mı’ka masa black card dinsa dan su karan kansu sunsan sunyi masa ‘barna da kud’i, ba fara’a ya furta “Leave this place � da Sauri suka mi’ke kuwa dan har bobo da uncle sun bar falourn Sabida sunsan zasu iya magana kuma big boss bazai gaji ba zai ‘kara ninkawa su little punishment, Abla kam gabaki d’aya kasa tashi tayi sabida yadda ‘kafarta Tayi mugun yi mata tsami, batare da ya kalleta ba ya nuna mata steps � 2 minutes na baki ki hau sama ki sakko� kamar bashi yayi maganar ba , a tsorace Abla ta mi’ke har tana ‘ko’karin fad’uwa kamar zatayi kuma sabida tsahon stairs din kuma tasan bazata iya gudu ba , da’kyar take taka steps dinnan , saida takai har ‘Karshe sannan ta sakko ‘kafarta kamar zata karye dan har ta soma hawaye � again � ya kuma furtawa , haka Abla ta sake komawa sama � kasa ‘kasa tana kuka Sabida karya jita, tun kafin ta sakko ma taji tana ‘ko’karin faduwa amma still sai da big boss ya ‘kara mayar da ita tana yi tana kuka ga fuskarta da tayi mugun ja har zufa ta had’a ta ‘kafafuwanta da suke mata azaba, sai da tayi sau biyar lokacin ko d’aga ‘kafarta Abla bata yi , kamar besan da wanzuwarta ba ya furta � coffee � baiwar Allah duk ta galabaita haka ta daddage taje ta had’a masa coffee kamar yadda su little suka nuna mata , kamar zatayi kuka ta furta � gashi � shima da turanci ta furta masa gudun karya sata wani punishment tunda gashi ya sata hawa step Sabida bata Wana Simba abinci ba , kamar besan da halitta a wajan ba Haka ya share ta gabaki d’aya , a karo na biyu ta ‘kara furta � ga coffee din� nan ma still babu amsa , ga zafin da ‘kafarta ta somayi mata dan har rawa ‘kafarta ta somayi gashi a tsaye take ba daman ta zauna , sau uku tana masa magana amma be motsawa sai ma latsa Wajan sa da yake hankali kwance , ‘kafar Abla sosai ta soma rawa dan ko bakinta ta kasa motsawa , kamar wacce Hajijiya zai fad’ar, tafi ‘karfin 20 minutes ri’ke da coffeee a hannu, shi be kar’ba ba sannan bece mata ta tafiba, sai datayi almost 30 minutes a tsaye sannan ya mike tsaye batare da ya kalli ko inuwartaba yayi wuce warsa part d’insa, fashewa Abla tayi da kuka ganin ko kar’ban coffee din be yi ba gashi ya tsayar da ita, da’kyar ta iya mayar da coffee din ta daddafa ta wuce d’akinta, ko kayan jikinta bata cireba, sai takalmi kawai , yau ko alwalar baccin da ta sabayi batayi ba sabida yadda ‘kafarta tayi mata tsami, cikin ‘kan’kanin lokaci baccin wahala ya d’auketa ko kyakkaywan kwanciya batayi ba Sabida yadda ta gaji. Su little ma suna shiga ko wanka basu yi ba Suka bi lafı yar gado dan dole baccin wahala ya d’aukesu. Fitowar bobo ne ya tarar da kayayyakin da sukai siyayya ya tabbata gabaki d’aya su Adil sunyi bacci shiyasa ya dunga d’aukar siyayyar ya kaisu part d’in Abla , batare da ya shiga ba ya dinga ajje mata su abaki, ices creams din kawai ya cire ya aka a fridge sannan ya duba lafiyarsu little , yadda suke bacci sosai dariya da tausayinsu ya kamasa lokaci guda , ya rasa kan big boss , tun Wanda ya ta’basu ya ta’bo wa kansa rigimar da bashi da maya’ka dan sai yayi mugun sa’bawa mutum, amma shine oga Wajan punishment dukda shima yana musu amma Big boss, Boss d’inne da gasken gaske, be wani jima a falourn ba shima ya nufi part d’insa .