← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 146

Sashe 40

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
KANO
NASARAWA G.R.A
kid’an da yake tashi da sanyin safiyane ya farkar da Eshaal daga baccin data koma tun bayan sallar asuba da tayi ,dogon tsaki taja sabida tasan babu d’an iskan da zaiyi wannan abun sai baby , d’ayan pillow dinta ta d’auka ta toshe kunnuwanta ko zata denaji kid’an amma duk a bazan , wani tsakin ta kuma saki cike da haushin baby data hanata bacci , a hankali ta zuro da santala santalan fararan kafafuwanta da suke sanye cikin kayan baccinta pink colour , dogon gashinta ya soma sukurkucewa Sabida baccin da tayi, half slipper dinta ta saka ta Fito daga cikin bedroom dinta , ita kadai sai faman sakin tsaki take, tana shiga d’akin baby taga fitilar d’akin a kashe sea light masu kaloli data bari a kunne , ita kanta Eshaal bata san Baby na d’akin ba taje ta Kashe kid’an . Tun shigowarta Baby ta ganta tayi mata shiru ne Sabida tana so ta d’anyi wani mistake d’in da zata saka dad momy hukunta ta. Plan d’inta kuwa yayi aiki sabida kashe mata kid’a da Eshaal tayi a harzu’ke baby ta furta � uban wa yace ki shigomun d’aki da har zaki kashe mun kid’a ko kina ba’kincikin ke baki dashi�, kallan sama da kasa Eshaal ta bita dashi � sai akace miki sabida kina da wad’annan banzayan abubuwan zai dameni? Ke kika damu dasu da har kike tunanin kunnasu, dama karatun alkuran kika sa da an fafata a ga me ilimi.baby taji haushin kalaman Eshaal Sabida tasan magana Eshaal ta fad’a mata , “Mtsww bani da lokacinki, ki koma ki kunna mun kid’ana tunda ba uwarkice ta siya mun ba� cewar baby, a tsawa ce Eshaal ta kalleta� na fad’a miki duk lokacin da kika kwaso shararki ki dena sako mun mahaifiyata, ko me zakiyi ya tsaya a iya kaina , amma bakyaji ke kullum abun tashin hankali kika iya ?� A gadarance baby ta furta � An fad’a, idan kinyi zuciya ki tattara ki barmun gida , ko kuma yan uwan matacciyar uwarki su d’aukeki, ko da yake ina ma Suka damu dake ? Daka ke har uwar taki data she’ka�, da karfi Eshaal ta buge mata baki, zafin da tajine yasa ta sha’ko wuyan Eshaal, itama da maganganun Baby suka ‘bata mata rai ta sha’ko Baby take a Wajan Suka soma danbe daman ba wani karfi ne da baby ba sai cika kurin bala’i, da iya karfinta Eshaal ta zage ta dunga luftar Baby, ita kuwa Baby sai faman ihu take wai Eshaal zata kashe ta , a guje momy da Amma suka shigo d’akin, cikin fusata momy ta cafko gashin Eshaal da karfi ta bugata da bango, wata bakar waya da ta gani me kyau ta d’auka ta soma jubgar Eshaal dashi da iya karfin, Eshaal sai ihu take tana bata hakuri amma kamar ‘kara ingiza momy take , Amma sai faman bata hakuri take amma itama tsawan da Momy ta daka mata ne yasa ba yadda ta iya taja bakinta tayi shiru, momy kuwa sai da tayi wa Eshaal shegen duka , kafun ta kalli AMMA � munafuka daman kece kike kitsa mata duk wani abu da zatayi, shine dan muna furta zaki biyo bayanta kiga meke faruwa , da izinin wa ma kika shigo cikin d’akin�, kiyi hakuri hajiya� sai alokacin Baby ta kalleta tare da jan wata ashariya � kutumar uba! Da izinin wa kika shigo mun d’aki da wannan warin jikin naki har ki taka mun carfet? Baki da hankaline ? Ko cuta kikeso kisakamun?�, da Sauri AMMA taja baya tana furta � kiyi hakuri� ta’be baki Baby Tayi� daman ku talakawan nan haka kuka iya , ayi hakuri a yi hakuri, kunsamu an d’auke ku aiki ma sai kunyiwa mutum shish shigi, tukunna ma wai kinyi wanka ? Naji d’akinta ya fara wari gaskiya �, Eshaal bataji dad’in maganganun Baby ba akan AMMA ko ba komai a haihuwa zata haifi kamarta ko wacce ta fita , yanxu tana bud’e bakinta kuma momy zata ‘kara dasa mata wani saban dukan ta Lura baby da gangan take yi Sabida tayi magana yadda momy zata kara dukanta , cike da dattako AMMA ta furta � Eh nayi �, da Sauri baby ta dakatar da ita � a hakan ne kikai wanka sai faman tsami kike ? Plx maza maza ki tattara kinfitar Munda ga d’aki dan harna fara jin amai na taso mun , ga wani bashi bashi da d’akina ya d’auka, yanxu ma � kiyi hakuri � Kawai Amma tace , momy kuwa tana tsaye tana kallan yadda Baby ke wula’kanta AMMA amma ko a jikinta sai dad’in Hakan da take ji ma , kallanta momy tayi up to down kafun ta nuna mata Eshaal da ke nishin wahala � ki kwashe wannan kayan wankin ki fitar da ita daga nan d’akin ,da kalar kazamai tayi kama , sunnan plx ko me zaki taba kisaka leda haka sabida kamar yadda baby ta fad’a Nima na fara jin wari warin nan gaskiya �, gabaki d’aya AMMAHta tsargu shiyasa ta saukar da kanta ‘kasa ta kasa kallansu, � ba magana ake miki ba , kutattara kubarmun d’aki�, rai a ‘bace Eshaal ta mike , har kunyar kallan AMMAH take sabida wulakanci da su momy sukai mata , bata damu da yadda Suka zuba mata idanuwa ba , ta kama hannun AMMAH suka bar d’akin, har cikin d’akinta ta kai AMMA, abun mamaki tsugunnawa Eshaal tayi tana bawa AMMAH hakuri Sabida irin wulakancin da Suka yi mata bakowane xai iya jurewa ba sai me ‘kololuwar hakuri , murmushi akan fuskar AMMAH kamar babu abunda ya faru ta dakatar da ita � Haba mana Menene haka kike ‘ko’karinyi ni wallahi babu Wanda na rike cikin raina , karki damu kinji �, banji dadin abunda sukayi miki bane AMMA , nasan kawai kina ‘boyewa ne amma nasan baki ji dad’in Hakan ba �,yanxu ma wani murmushin Amma ta sakar mata tare da d’akko mata manzafi� ki shafa wannan kada kiyi ciwan jiki, ina da ayyuka � ,toh Kawai Eshaal Tace mata , sai da tayi wanka da ruwan dumi sannan ta shafa man zafin, komai cikin Sauri take yinsa sabida bata san wani wulakanci baby zatayi wa AMMAH ba musamman taga tana had’a musu breakfast, shiyasa gabaki d’aya ta d’auki ragamar yin abincin gidan . Tana fita kitchen ta nufa ta soma kokarin d’aura breakfast, fish pepper soup ta had’a sai chips and plantain da ta had’a musu, ga hot tea da ya sha kayan kamshi, batasan almabuzzuranci shiyasa komai Daidai tayi , and Tasan bata isa taci komai data girka ba Indai ba baby ce tace ta koshi ba .

A wajan cin abinci ma babu irin tujara da Baby batayi ba , iya shegenta kawai take yi momy na biye mata , duk abunda sukai kuma daidai ne dan awajan breakfast dinnan sai da dad ya turawa baby 200k cikin account dinta amma ko gaisuwar Eshaal be amsa ba sai ma hade rai da yayi, baby kuwa dagangan ta’ki Tashi daga wajan dinning sai data tabbatar komaj yayi sanyi lokaci yaja sosai kafun ta tashi tabar Wajan, sai alokacin su Eshaal suka karya wajan around 12. Da rana ma haka tayi musu wannan iskancin bata bari sunci abinci ba sai wajan la’asar , already momy da dad kowa yafita sabgarsa.

9:00pm lokacin da Eshaal take ‘ko’karin kwanciya Baby ta tsuro da zancen wainar fulawa take sha’awa, haka eshaal ta hakura da kwanciyar da zatayi ta je kitchen ta fara kwaba kwainar fulawa , saida ta soya su duka ga bacci da take ji, tana kawo wa baby tace mata ta manta bata fad’a mata ba wainar ta fita ranta bata sha’awa . Eshaal jitayi kamar ta sha’ko wuyan baby ta tsuntsun ka mata mari Amma babu yadda ta iya musamman yadda taga momy na jifanta da kallan tsana . Gabaki d’aya wainar masu gadi ta bawa dan alokacin tasan AMMA tayi bacci, still bataje ta kwanta ba saida baby ta gama yin duk abunda zatayi kafin ta mike ta nufi d’akinta tana cewa Eshaal � ki kashe TVn�. Kashewar kuwa tayi sabida babu yadda zatayi itama gashi baccin take ji, tana shiga d’aki Kayan bacci Kawai ta saka tayi alwala itama tabi lapiyar gado . (Asuba ta gari🚶🏻‍♀�).

🍃🍃🍃🍃🍃
GERMANY
FRANKFURT
Chapter 40 · 0% Book details