← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 146

Sashe 141

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*****Abla tana shiga cikin gidan ta tarar da babu kowa a falourn, a tunaninta su Little suna d’aki shiyasa itama bata zauna a falour ba ta wuce cikin d’akinta tayi wanka ta shirya cikin maroon d’in doguwar riga . Tana sakko wa ‘kasa still bata tarar dasu Little a ciki ba , batayi tunanin komai ba ta wuce dinning zatayi serving kanta , kamar Ance mata ta jiyo taga su Little sunfito daga wata ‘kofa , prince na gaba little na binshi a baya ga hannayensa biyu da ya ‘boye duka a bayansa . Murmushi Abla ta sakar musu � Na dawo gida nan gankuba , na d’auka bakwanan ai � , murmushi a face d’insu suka furta � No Lil mun tsaya wani abune � kallan bayan prince Abla tayi ganin yadda Little yake kakkarewa , cikin ‘yar dariya Abla ta furta � yaya little me kake ‘boyewa a bayanka ?� Kanshi ya girgiza mata ga face d’insa da har yanzu akwai murmushi akanta � No ! No! Babu komai � zatayi magana prince yayi saurin furta � No please karki yi magana � shiru Abla tayi tana Kallansa , da Sauri ya zagayo ta bayanta ya kulle mata ido da wani bakin abu, ita Abla gabaki d’aya dariya suka bata ma yadda suka kulle mata fuskarta , � karki magana � cewar prince , batayın ba kuwa har prince ya kama hannunta suka zaunar da ita kan kujera , tana zauna prince yayi dialing number din uncle da shima ko mintuna 5 beyi ba ya fito face d’insa fal murmushi. Da ido Little ya nunawa prince ya bud’e wa Abla idanuwanta , yana cire kyallan prince da little suka had’a baki wajan furta � Happy Birthday princess �, at the same time kuwa ya fito da wani medium cake da ya ‘boye a bayansa . Lokaci d’aya gabaki d’aya murmushin fuskar Abla ya ‘bace sai ja da fuskarta ya soma yi , da Sauri ta sunkuyar da kanta ‘kasa tana taunar le’ben ’kasan bakinta ,� Lil ?� Tun bai ce sister d’in ba Abla ta kulle idanuwanta tare da fashewa da kuka , cikin Sauri little ya ajje cake d’in tare da zama a side d’in ta , � Lil me akai miki? Waya ta’ba ki ? Ni ne ? Yaya prince ne ? Me akai miki?� Shine tanbayoyin da Little ya soma yi wa Abla ganin yadda take kuka sosai , uncle kuwa waje ya samu ya zauna yana kallan Abla ganin yadda take kukan ta da gasken gasken, Little zai sake magana Uncle yayi saurin dakatar Dashi � it’s okay Little � da Sauri little da prince Suka kallesa , da kai kawai ya amsa masa yana ‘kara Kallan yadda Abla take kuka . Suma shirun sukai suna ‘kara binta da idanuwa , musamman little da shima yake ji kamar yayi kukan.ta d’auka kusan 5 minutes tana kuka ganin kukan nata bame ‘karewa bane yasa uncle dakatar da ita � it’s okay Daughter, kukan ya isa haka , tunda birthday d’in ne bakyaso bazasu sake miki ba , kinji ?� Sai kuma ya ‘karasa yana kallan su Little � karku ‘karayı mata tunda bata kunji ?� Cikin Sauri Abla ta girgiza masa kai , muryarta kamar me kuka ta furta � Ah.. ah ni basuyi mun komai ba uncle , abune ya shiga cikin ido na , babu abunda ya sameni � , shiru sukai mata suna kallanta ,kafun prince ya furta � kuka kikai magana , bamusan hakan zai ‘bata miki ba , we’re all sorry � wani kukan Abla yaji yana san sake zuwar ta , murmushi me ciwo ta saki sosai kafin ta furta � Dagaske nake yaya prince ni bakuyi mun komai ba , ku dena bani hakuri � then me yasaka ki kuka ?� Cewar little yana tsareta da ido, shiru Abla tayi masa tana bin cake d’in gabanta da kallo , shima prince murmushi ya d’an saki kad’ai kafun ya furta “we’re not family ? Da bazaki fad’amun abunda yake damun ki ba ? I thought we’re family ! We can share our issues ! Amma it’s okay tunda bakya san kowa ya sani � ya ‘karasa yana ‘ko’karin mi’kewa , da Sauri Abla ta ri’ko hannunsa � No please ka zauna “zaunawar yayi kuwa yana kallanta , wani murmushin Abla ta ‘kara saki � ba yau ne birthday d’ina ba , bansan Yaushe bane , bansan ranar ba Nima � cikin Sauri prince ya furta � Sister � kanta ta jinjina masa � yes ! Yaya prince bani da family, bani da kowa , bansan su wanene suka haifeni ba ,bansan mamana ba , bansan babana ba , sun mutu ko suna raye duka bansani ba �, hawayen da suka zubo mata Abla ta share tana sakar musu murmushi ganin yadda reaction d’in face d’insu ya canza gabaki d’aya , a jiyar zuciya ta dauke ahankali kafun ta cigaba � cikakken sunana shine Ibtissam amma cikin wad’an da na rayu dasu suna kira da Abla, kullum cikin godewa Allah nake da irin rayuwar da na tashi , kuma bazan daina gode masa ba , kamar yadda na fad’a muku bansan su wanene suka haifeni ba , nasan kawai na taso cikin ‘kunci da ba’kin cikin rayuwane,da farko na taso cikin gidan haka , matar da ta d’auke ni ta shaidamun batasan su wanene suka haifeni ba , ta tsinceni ne cikin wata ‘kauye a daji cikin cijayawa duk Jini a jiki na , ga ruwa anayi lokacin wannan ne babban dalilin da yasa ta tausaya mun ta d’auke ni, nayi rayuwa da Ita cikin bautawa , kamar baiwar ta haka ta mayar dani dukda nafijin dadin sosai akan inda na rayu , ko ba komai tayi mun hallaci,ita ta sakani makaranta, take boyamın kudin makaranta , abinci na , komai ita take yi mun shi , hatta sunan da na mahaifinta nake anfani a makaranta Sabida bansan wanene nawa uban ba.� Sai da ta saki a jiyar zuciya kad’an kafun ta cigaba , � rayuwata ta soma gur’bacewane tun bayan rasuwar ta , Sabida tsangwama da mutane suke nuna muna , suna Kirana da yar karuwa , bani da yadda zanyi , babu Wanda zai tai maki rayuwa ta , da farko na soma kwana a cikin kwango amma Sabida yadda mutane ke ‘ko’karin lalatamin rayuwa tsoran hakan ya kamani, Tuna’nı na kullum ya zanyi na tsira , kwatsam wata hajiya ta so temaka mun duk na so na ‘ki amince mata amma sabida ba yadda zanyi dole na amince mata , haushe ‘ko’karin fad’awa rami nake, a ranar farko da naje gidan ta , ta kula dani sosai kamar yar data haifa har na soma sha’kuwa da ita Sabida Itama ta fad’a mun ita kadai take rayuwa bata da yan uwa, shiyasa Nima na sake sosai da ita , a cikin kwana na biyar da nayi a cikin gidan ta wasu mutane suka d’auke ni daga wajan ta, Aushe siyar dani tayi , ta siyar dani ga macen da ta fi kowa san lalata dani , karuwa, mara tsoran Allah , mara ‘kaunar addinin Allah, nasha wahala sosai , bana bacci sai cikin dare sai ayyukan da nake yi , ga kiran da ake saka wa cikin dare , hakan baya hana ‘karfe 3 na dare a tashe ni daga bacci ni da ‘yan matan da aka siyar dasu , ka zame mun tamkar yan uwana na Jini , Arwa, ilham, Aneesa, muna shan wahala sosai , basa bamu abinci, kullum burin su , su sami Wanda zaiyi lalata damu ,� gabaki d’aya sai da Abla ta zaiyane musu irin rayuwar Da tayi cikin gidan uwar karuwai da ‘kalubalen data fuskanta har kashe mata Arwa da sukai da yadda suka siyar da ita har zuwa lokacin da su Bobo suka tsinceta, tana kaiwa nan ta fashe da kuka tana kulle fuskarta, cikin Sauri Little ya goge hawayen fuskarsa � waya ce miki baki da family ? Ku kuma fa ? We’re all family! Na miki al’kawari I will always be by your side , kin manta ni yayan kine ?� Kanta Abla ta jin jina masa tana murmushi kad’an , shima prince hannunta ya ri’ke � we’re family ki dena cewa baki da family , duk Wanda ya ta’baki just karki manta Prince and Little will always be there for you , kinji?� Yanzu ma kanta Abla ta jinjina masa gabaki d’aya sai sukayi hugging d’in juna . Uncle kuwa tun da ta soma basu labarin ta be motsaba sabida zurfin Tuna’nın da ya fad’a , ganin yadda mood d’insu ya canzane suma Abla ta furta � Nifa yunwa nake ji ! Let’s eat the cake � kasa magana sukai gabaki d’ayansu, da kanta Abla ta yanka cake d’in , ta basu, zasu magana Abla tayi saurin furta � let’s enjoyed our life komai da sanin Allah ! Okay ?� Kansa little ya jinjina mata, gefe d’aya kuma yana jin badad’i ko kad’an, zuciyarsa yaji ta soma zafi shiyasa ya kawar da komai amma duk da hakan yana ‘ko’karin dannewa sabida bayasan tayar musu da hankali .A ‘bangaran Abla ma dannewa kawai take sabıda kar suga rauninta, shiyasa Ta kawar da duk wata damuwar ta Sabida tana san ganin farin cikinsu , suna zaune a falourn har lokacin kuma babu abunda uncle yace sai binta da kallo da yake. Lokacin sallah nayi suka wuce masallaci itama kuma Abla ta wuce d’akın ta . Cikin Sauri ta kulle ‘kofa tare da tsugunnawa a Wajan , kukan da take ‘boyewa yana ‘kwace mata .
Chapter 141 · 0% Book details