← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 146

Sashe 92

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana tsaye yayi folding hannunsa ya na kallan ikon Allah , dan shi gabaki d’aya yadda ya ga tana magana ita ka d’ai ya d’auka aljanu ne a kanta , ran sa a ‘bace yake je fa mata wani mugun kallo dayasa tayi saurin had’iye yawun ba kin ta, a hankali ya soma ta kowa cikin falourn, itama Abla a tsorace ta fara ja baya ganin yana nufo in da take , hannunta d’aya ta fara yarfewa kamar za ta yi kuka ta furta � Dan Allah kayi ha’kuri ni badakai nake ba,� sai kuma tayi saurin toshe bakinta ganin ta ‘karayin wani lefin tunda ya hanata magana da Hausa , yadda take ja baya bata san lokacin da ta ‘karasa wajan kujera ba , shima still be dena nufo hanyar ba , tanagani yazo daf da kujerun ta hantsila baya kanta yana bigewa , cikin kuka kuka ta furta � Wayyo Allah na�, kafarsa d’aya big boss yasa ya taka mata ‘karamin d’an yasan ‘kafarta , cikin azaba Abla ta saki ‘kara ta soma bashi hakuri sabida zafin da taji a d’an ya tsan naka , amma ko gezau big boss beyi ba sai ma ‘kara taka shin da yayi sosai yadda zata ji zafin ,cikin husky voice d’insa ya daka mata tsawa , lokaci d’aya jikin Abla ya soma rawa , cikin kallan tsanan da yake jefa mata ya soma magana � just because na barki ki zauna ba shike nufin ke ahalin gidannan bace , ko wanene ya baki plan d’in shigowa cikin gidan nan , just wait and see , and this is my last warning , idan kika Kuskura na sake ganin face d’inki a inda nake sai na mugun sa’bamiki , stupid !”a hankali cikin shashshekar kuka Abla ta soma bashi hakuri , rai a ‘bace ya daka mata tsawa � Get lost�, cikin kuka sosai Abla ta ruga stairs inda d’akinta yake , tana gudu tana share hawa yan da suke zubo mata .

***** Tana shiga d’aki kan bed ta fad’a tare da fashewa da saban kuka , kuka kawai takeyi abunta ,duk da irin abunda yayi mata yanzu kwata kwata bata ji zafinsa ko d’aya a cikin zuciyarta ba, sai ‘kara tuno face d’insa da tayi da yadda dogon murd’ad’d’en gashinsa yake motsawa , a hankali face d’insa ta soma yi mata gizo kamar yanxu ne yake mata fad’an shiyasa ta ‘kara fashewa da wani saban kukan, tun tanayi da ‘karfi har ta somayi a hankali sabida muryarta data d’an dishashe, lokaci d’aya kuma ta soma sakin a jiyar zuciya alamar bacci ne ya d’auketa, ga d’an mitsitsin bakinta da ta turo lokacin da take baccin.

****Big Boss
Tana wucewa sama ya ja siririn tsaki , cikin ‘kasa ‘kasan ma’koshi ya furta � stubborn rat�, doguwar maganar da yayi yanxu har kansa ya soma yi masa ciwo, ga face d’insa da ya ‘kara had’ewa kamar har yanzu tana gabansa, diamond watches d’insa ya kalla da fararan idanuwansa a karo na biyu ya ‘Karajan wani siririn tsaki tare da nufar part d’insa .

************
10:00am Little , Bobo , prince da uncle suka shigo cikin falourn , babu kowa a ciki shiyasa ko wannansu ya nufi part d’insa sabida su canza kaya, Prince sai mita yake wa little lokacin da yace zai je part d’in yaya , da kyar ya samu little ya hakura sabida shi yunwa yake ji, da Zaije d’akin Abla ma saida prince ya ro’ke shi akan ya dawo da wuri, cikin rashin sa’a yana shiga ya tarar da Abla tana bacci shiyasa ya dawo falourn , lokacin gabaki d’aya suna kan dinning suka jiran fitowar su , ganin babu Abla a bayansa yasa bobo tanbayar sa � ina little sis d’in taka ?�, d’an kalar tausayi little yayi � yaya tayi bacci sai dai kafun ta farka ayi mata wani breakfast d’in ita da yaya � kansa bobo ya jinjina masa � it’s okay ! Let’s eat�, daga haka gabaki d’aya Suka zauna James yayi serving d’insu tunda Abla bata wajan . Suna gama cin abinci little be jira kowa ba ya nufi part d’in Big boss , kusan kullum light d’in part d’insa a dum yake shiyasa basa damuwa da hakan , direct bedroom d’insa ya nufa bayan yayi knocking sau uku ganin big boss be amsa masa bane yasa ya shiga cikin d’akin, nan ma still dum light ne a wajan , a hankali little ya furta � yaya ?!� Shiru yaya be amsa masa ba , a karo na biyu ya ‘kara ambatan sunansa amma still be amsa masa ba duk da yana jin lokacin da little ya shigo cikin d’akin amma ya sharesa , cikin turo baki little ya hau kan gadon tare da fara yaye masa white blanket d’insa , be bud’e eyes dinsa ba sai cikin cool voice d’insa ya furta � little what do you want?�, muryar little d’auke da murmushi ya furta � yaya ni fa maganar sister nazo nayi maka ya kamata ta fara zuwa school please and naga kana bacci fa� shiru big boss yayi masa ba tare da ya amsa masa ba , a shagwa’be little ya furta � please yaya kaji?am your little ka manta , ina so sister ta fara zuwa makaranta please�, shiru big boss ya ‘kara masa har saida yace masa � please� , yanxu ma cikin cool voice kamar bashi ba ya furta � bani da kudi� wani irin dariya little ya saka da har saida big boss ya bud’e lumshash shun eyes d’insa � haba yaya taya zaka cemun baka da kudi? Please just for my sake kaji?� ‘Dan ta’be baki big boss yayi lokacin da ya zubawa little idanuwansa � kana da kudi sai ka sata mana , ni na hana ka ?� Girgixa masa kai little yayi � but yaya kace fa ko me nakeso na fara tanbayar ka !� Dakatar Dashi big boss yayi ta hanyar furta � jiya da kuka kashemun kud’i shima kun tanbayeni?� No yaya , cewar little � okay fine ! Allowed me to sleep�, yana kai ‘Karshen zancansa yaja duvet dinsa , d’an turo baki little yayi tare da kwanciya a side d’insa ba tare da ya ‘kara furta komai ba shi a dole yayi fushi.

✨✨✨✨✨✨�

NIGERIA
KANO STATE

Tun lokacin da dady ya furta komawarsu Eshaal U.s baby take fushi dashi sabida batasan komawa da Eshaal ta fisan ta yi tafiyarta makaranta ita kad’ai shiyasa tace wa dady ya samo mata wani school a cikin Garin Kano. Sosai ta tada bala’i cikin gidan daga momy har dady babu Wanda ta ragawa dan sai da tayi kwana uku bata kula kowannansu, kullum cikin rarrashinta suke yi dady har kyautar mota yayi mata dan ta wuce shiyasa ta d’an sassauta fushinta, amma duk lokacin da taga Eshaal ko AMMA ta fara ci musu mutumci kenan musamman Amma da take gani Itace ta Shirya ko wani makirci na komawar Eshaal U.S. Duk da ta ha’kura ta d’au Al’kawarin sai ta musgunawa Eshaal har sai taji tafisan zamanta a Nigeria , kullum cikin kawowa dady da momy ‘karar Eshaal take , musamman momy da tafi kowa tsanar Eshaal haka zata kamata tayi ta dukanta kamar wata jaka , sau biyu momy tana tsinkawa AMMA mari lokaci na farko da Baby taji babu dad’i cikin zuciyar ta Sabida Momy bata ta’ba Marin ta agabanta ba , bata kawo komai aranta ba ta share tunanin duk da lokaci zuwa lokaci hakan na fad’o mata arai .
Yau ya kama saturday, ranar da yayi Daidai da saura kwana biyu su Baby su koma U.s karatu, tun safe Baby ta fita ita da momy da dady sabida siyayyar da suka fita da baby ta za’bi duk abunda take san siya amma ko kusa dady be bawa Eshaal 5k ba ta siyayya kuma ba kowa ne ya hana hakan ba face momy, a cewarta idan baby ta dawo zata bata tsofaffin kayanta sai tayi anfani dasu . Eshaal ko ajikinta inda sabo ta saba da irin halin momy da take nuna mata tsana a fili , shiyasa tana gama abincin rana kayan sawarta ta zauna ta goge duk da yadda Amma ta so ta bata amma Eshaal ta’ki bata sai ma zuwa da tayi ta kwantar da Amma akan ta huta . Tun tana yar ‘karamarta bata da uwa kamar Amma Sabida dukda yadda AMMA take aiki a karkashinsu ta fisan ta fiye da kowa na gidan har Dadyn ta. Sabida yadda ada ya nuna mata soyayya amma tun bayan mutuwar mahaifiyarta soyayyarsa ta koma kiyayya baya san ganinta , bayasan ta ra’beshi bayasan komai da ya dangan ce ta shiyasa itama take jan jikinta, yanxu a rayuwa bayan Amma bata sakewa da kowa Sabida ita kad’ai ce sırrın ta .

**** Ana idar da sallar la’asar Eshaal ta shiga cikin kitchen Sabida sha’awar d’an malelen da take , cikin d’an ’karamin tukunya ta d’ora musu ruwan d’an malelensu , gabaki d’aya saida ta yanka tomato, cucumber ,albasa da zasuci d’an malelensu , ruwan da ta d’ora yana tafasa ta saka tsakinta da ta wanke tare da barbad’a masa gishiri kad’an, tun kafun ya dafu ta soya musu manja . Tana gamawa har wani murmushi take saki , cikin wani medium tray ta juye musu d’an malelen , ta saka manja , tumatur , cucumber , da albasa , sai tabi kansu da wani irin yaji me shegen dad’i da AMMA ta daka , tun kafun ta faraci har ta fara had’i yar miyau ita kadai.
Chapter 92 · 0% Book details