← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 146

Sashe 69

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

9:30pm motocin su Big boss suka shigo cikin gidan , cikin sauri sojojin su sukai layi har motocin su big boss suka shigo cikin compound d’in gidan , da Sauri Victor da Anthony suka fito daga cikin mota suka tsaya a Daidai kofar motar su big boss, lokacin gabaki d’aya ragowar sojojin sun fito suna jiran fitowar Oga big boss , kusan mintuna 5 kafun Victor da Anthony su bud’e musu mota, ko minti 2 bobo beyiba yafito daga cikin motar banda big boss da idanuwansa suke a kulle bashi da alamar fitowa daga cikin motar , kusan mintuna 10 big boss yana cikin motar har lokacin bobo be tafi ba shima yana jiran fitowar sa, sai da ya mula yasha İska (har ya bushe inji mss Lee 😹😂) sannan ya fito da kyakykyawar farar balarabiyar ‘kafarsa, still sai da ya ‘kara d’aukan 2 minutes kafin ya fito gabaki d’ayansa , babu Wanda ya kalla hatta bobo da ke jiransa bai jira saba yayi wucewarsa , girgiza kansa bobo yayi kawai tare da bin bayan big boss suka jera a tare . Suna shigowa gabaki d’aya su little suna zaune a falourn suna jiran dawowarsu, bobo kai tsaye inda suke ya nufa banda big boss da yayi wucewarsa ko nuna alamar da mutane a falourn beyi ba . Kan little bobo ya shafa lokacin da yake ce masa welcomed back , shima be zauna ba sai kallan uncle da yake sakar masa murmushi yayi � uncle barka !� Sai kuma ya kalli prince da little � kuma yadda naga kun nitsunnan nasan kunyi rashin ji ,� kallan juna prince da little sukai tare da girgiza kai lokaci guda d’aya , gabaki d’ayansu rangwashi ya kai musu kafun ya nufi part d’insa suna furta � kukai wa big boss coffee d’insa da fruit� , da ‘karfi little ya furta � okay sir�, cikin sauri suka nufi wani waje da coffee maker yake ga wasu abubuwa masu kaloli daban daban , a Wajan , sosai cikin kwarewa little ya had’awa big boss coffee sai faman turiri yake , prince kuwa da kansa ya yanka fruit d’insa , sukayi arranging cikin tray fari tass Dashi suka nufi part d’insa , rabansu da su shigo d’akin tun d’azu da suka gyara masa shiyasa amaimakon suji kamshin turaran d’akın sai kamshin turaran big boss suke ji ta ko ina , kai tsaye ‘kofar bedroom d’insa sukai knocking shiru ba’a amsa ba , sau biyu suna knocking ba’a amsa ba sai a na ukun sukai shahada suka shiga. Kamar yadda sukabar d’akin d’azu haka yake yanxu ma sabida duhun d’akin da suka gani, batare da tsoro ba little ya ‘karasa wajan center ya kunna wani abu take hasken d’akin ya kunnu tako ina ga sanyin da d’akin ya d’auka kamar zai shiga cikin ‘kashin mutum. Babu kowa a cikin d’akin sai kamshin turaran big boss , akan center d’in d’akin suka ajje masa tray d’in tare da barin d’akin. Kusan mintuna 2 da fitarsu shikuma big boss ya fito ba’kin gashin kansa sai faman tsiyayar ruwa yake kad’an kad’an , jikinsa sanye yake cikin wata ba’kar t-shirt da ta matse masa hannu, sosai muscle d’in hannunsa suka fito kamar zasu fasa hannun rigarsa ga farar fatar jikinsa da ta ‘kara haska ba’kar rigar jikinsa , Wanda jikinsa bari tass dashi me laushin gaske sai white half shoe da yake ‘kafarsa, dogayen ‘yan yatsunsa sosai suka fito cikin ta kalmin ‘kafarsa. A kan sofa d’insa ya zauna tare da d’aukar coffeee d’in da su little suka ajje masa , ya d’au mintuna a hannunsa kafun ya fara shipping d’insa a hankali , sai a lokacin ya janyo system d’in gabansa , sosai yake operating a kan da alama wani aiki yake me muhimmanci sosai , har ya shanye coffee d’in hannunsa ya ‘kara zuba wani be gama aikin da yake ba dan ko fruit d’in da aka ajje masa be soma cıba , saida yasha 4 cup of coffee tukunna ya ajje cup d’in , wasu short number ya danna cikin dan’kareriyar wayar sa cikin ‘yan seconds aka d’aga wayar be jira jin abinda za a ceba ya furta � operate on it� sai kitt ya kashe kiran batare da ya jira jin amsar wanda ya kira ba .

✨✨✨✨�
CANADA

HALIFAX..

Saida Abla tayi kusan 3 hours tukunna ta bud’e idanuwanta a hankali sai faman sakin ajiyar zuciya take tana bun d’akin da take ciki da kallo , da Sauri ta mi’ke zaune tana ‘ko’karin tashi tsaye EMMA da ta ‘karaso Wajan tayi saurin dakatar da ita , bangajeta Abla tayi da Sauri ganin matar da bata ta’ba gani ba , “cike da tsoro ta furta wacece ke? Me nayi muku� bakinta har rawa yake ta soma jin jikinta , kallan kallo suka fara tsakanin ta da Emma ganin bata fuskantar abunda take cewa da French EMMA ta furta � babu abunda zan miki ki kwantar da hankalinki� binta da ido kawai Abla tayi jikinta sai faman rawa yake ganin bata fuskantar abunda EMMA take cewa , itama Emma fahimtar hakan hakan yasa ta dakata da hannu ta soma mata alama kafun cikin turanci ta furta � babu abunda zan miki� sai a lokacin Abla ta saki jikinta dukda hakan bata bari Emma ta ta’ba taba , tray din gabanta emma ta ajje mata da Sauri ta saka hannu ta d’ibi abincin ko loma d’aya batayi ba ta amayar dashi ganin gabaki d’aya babu test cikin abincin ga ‘karnı da d’anyen abinci da taji abakinta kamar zata kwayar da ruwan cikinta amma babu abunda ya fita daga cikin ta , sosai hakan ya bawa Emma tausayi shiyasa ta janyo plate d’in fruit ta mi’ka mata , yanxu kam da sauri Abla ta karba tare da komawa nesa da Emma sosai ko tsayawa batayi ta dunga tura fruit din cikin bakinta , sai data cinye duk yawan fruit d’in dake cikin plate sannan ta soma ajiyar zuciya , ganin tasha fruit din sosai yasa Emma kwashe tray din tare da nuna mata bed yanxu ma da turanci tace mata ta kwanta , tana kai karshen zancanta ta kunna mata Ac tare da ‘ko’karin kashe light , cike da tsoro Abla bata san lokacin da ta furta “No�, murmushi Emma ta sakar mata kafin ta furta � okay goodnight� . Tana barin d’akin Abla ta takure jikinta sabida yadda ta fara jin sanyi na ratsa mata jiki , ita kadai sai Faman bin d’akin take da kallo ganin a rayuwar ta bata ta’ba shigowa cikin d’aki irin haka ba , yadda taji sanyi na ratsatane yasa ‘kara bin dakin da kallo ko akwai wani aciki ganin babu kowa a ciki yasa tayi saurin Jan ‘karamin blanket d’in gadon ta takure jikinta dashi a’kasa sabida jin wani irin sanyi da bata ta’ba Jiba ko a gidan uwar karuwai. Sosai sanyin d’akin ya soma sakata lumshe idanuwa Sabida yadda hakan ya fara yi mata dad’i , tun batasan lumshe idanuwanta har take lumshe su , cikin kankanin lokaci baccin da ta dad’e batayi irin saba ya d’auketa ga sanyin Ac da yake ratsata sosai .

WASHE GARI

Wajan 11amm su Mila gabaki d’aya suka shigo cikin d’akin har da Mom , yadda suka ga Abla ta takure a ‘kasa yasaka gabaki d’aya Jan burki , ita kad’ai sai faman jujjuya kanta take , tray d’in fruit din hannunta Emma ta ajje tare da karasawa inda Abla take , tana ta’bata Abla ta farka a firgice , lokaci d’aya ta soma bige bige da Sauri Mila ta bar d’akin itama Emma ta soma ‘ko’karin riketa ganin lokaci d’aya ta ‘kara bir kice musu kamar zasu shid’e mila tana dawowa bata tsaya bin shawararsuba ta yiwa Abla allurar bacci, cikin kankanin lokaci jikin Abla ya ‘kara saki , rai a’bace Emma ta furta � me kikai mata�, d’an kallanta Mila tayi kafun ta furta � wannan shi kad’ai ne best solution idan ba haka ba ranta yana cikin hatsari� dakatar dasu mom tayi � wannan ba wani abu bane , yanxu abunda nake so daku just ku wanke mata kanta ku gyara masa nails d’inta naga sai ku saka mata wancan gown zuwa anjima� ta ‘karasa tana nuna musu red gown d’in da bata da tsaho sosai. Hakan ce kuwa ta faru mom na fita suka d’auko d’auki Abla suka shigar da ita toilet , sosai suka wanke mata kanta da yayi mugun datti , dukda haka basu wanke shi ya futaba, sama sama suka wanke shi dan suma basu saba yi ba yi musu ake , Clara tana ‘ko’karin taba zip din Abla , Emma ta dakatar dasu akan babu Wanda zai cire mata kaya, haka suka gyara mata nails d’inta sosai yan yatsun ‘kafarta sukai mata kyau ba kad’an ba , ga gashin kanta da bakinsa ya ‘kara fitowa dukda dattin sa be tafi duka ba . Suna gamawa mai kawai Emma ta shafa maka akai tare da taje mata uban tukun gashin Abla ganin lokaci d’aya cikowarsa ya fito sosai Sabida babu murd’ewar da yayi ba tare da sun tufke mata ba suka kwantar da ita suka bar d’akin gabaki d’aya .
Chapter 69 · 0% Book details