← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 146

Sashe 3

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

har na kasa banbance wanane yafi kyau a tsakaninsu duk da fuskar little ma rabi ce a bude amma kana ganinsu zaka ga kamannin da suke da juna har ya kwayar idanuwansa light gray ya zuba musu , “YAYA BOBO� little ya fada da niyar nufar sa, wani gigitaccen kallo ya jefa masa kuskarsa kwata kwata ba fara’a � if you dare ka kara one step kaga yanda zan karya kasusuwanku �, narai narai little yayi da ido, shikansa Prince tsoran magana yake kar lefin ya dawo kansa baki d’aya ,kallansu mutumin yayi kafun ya nuna musu 5 fingers dinshi � just 5 minutes na baku , ku tabbatar falon nan ya dawo yanda yake kafun ku karbi punishment dinku�, be karasa maganar ta saba suka fara gyara pillows din , jiya d’auke kansa yayi daga kansu kafun ya dakko wata roughly mobile phone army dake jikin 3quarter dinsa , number 3 kawai ya danna ko mintuna biyu ba aiba , su captain Suka shiga cikin babban parlourn, gabaki d’aya sara masa sukai ko kallan inda suke beyi ba, cikin kwarewa captain ya kara sarawa tun kafin BOBO yayi magana, Cikin yaran turanci Captain ya furta � reporting !!! Tukin ganganci a harabar gida hukuncin bulala dari tare da zagayen gida sau dari shine hukuncin mu�, ga baki d’aya sauran soldiers din suka hada baki wajan furta “salute�, hada ido Prince da adil sukai, cikin zuciyar sa prince yake furta “shikenan little ka kashe ni da raina, yanxu idan me kirar samu dawan nan ya dawo kan mu ai mummutu, “su captain suna fita Prince be karasa maganar zucin saba Bobo ya maida kallansa akansu, gabaki d’aya sunkuyar da kai kasa sukai, kan one sitter ya zauna kafun yayi crossing legs dinsa yana duba a gogo � zagaye dari!!! Starts � kamar zasuyi kuka suka fara zagaye falon gashi ba damar su bashi hakuri ya kara nunka musu wani wahalar, a zagaye na 20 suka fara layi kamar zasu fadi, a hankali suka fara tafiya yanxu, mikewa bobo yayi daga kan kujeran tuni suka manta da gajiyar tasu suka ci gaba da zagaye falon, da sunyi kokarin tsayawa zasu ga bobo na binsu da kallo, a 80 adil ya fadi kasa tare da fashewa da kuka � yaya bobo please kayi hakuri, kamanta little dinka ne ni kuma yau graduation dina fa, � shima Prince zubewa yayi a kasa cikin pleading ya furta � yaya bobo we’re sorry �, babu Wanda ya kula acikinsu, � zagaye hamshin!!! Starts�, sakin baki Prince yayi � wani lokaci har tunanin tsakanin big boss da yaya bobo wanane yafi wani iya mugunta dan hukuncin big boss ya fi na kowa tsauri, ba karamin aikin sa bane yasa a jefaka caged din zakinsa kuma babu Wanda ya isa ya futar da kai sai ta Allah. Zasu mike wani mutumi ya shiga black American da shi, jikinsa sanye da kananan kaya shima, little na ganinsa ya kara fashewa da kuka � Uncle iron man , please ka bawa yaya bobo hakuri kafata ciwo take mun�,kallan bobo mutumin yayi yaga ya dauke kansa, murmushi ya saki kafun ya karasa inda little yake � kunyi lefi kenan, ku bashi hakuri idan ya ki hakura ku kira masa big boss sai ayi ya’ki kowa ma ya huta�, yanda suka zaro idanuwane yaso bashi shi dariya , zasu kara magana bobo ya nuna musu hanya dan hayaniyar su har ta cika masa kunne � leave this place now�, ai be karasa ba ko wannansu ya arta a guje, yanxu kam kasa rike dariyarsa mutumin yayi saida ya dara kafun ya kalli bobo � why are you punishing yourself, kai da big boss kunfi kowa jin zafin punishment din da kuke sasu amma hakan baya hana gobe insunyi lefi ku hukuntasu, ynxu da dan gwarzane sukai sai kunfi kowa jin ciwo, in wani kuma yayi gigin koda mintsuninsune tsaf zaku harbe mutum,please ku sassauta wannan zuciyar taku�.shafa keyarsa bobo yayi kafun ya furta “ok uncle�, girgiza Kai uncle din yayi kafun ya nufi wata kofa , shima bobo wajan elevator ya nufa da zea kaishi sama. A bangaren Prince da little kuwa suna shiga dakin su kowa ya haye kan gadonsa yana maida ajiyar zuciya Dan ba karamun horuwa sukai ba, babu Wanda ya kula junan su ,musamman little da yake fushi, ko wannansu wanka yayi cikin kayan shan iska, duk yanda Prince yayi da little su sakko kasa yaki, ya ma ki yi masa magana kwata kwata sai ma Hayewa kan bed dinsa da yayi yana lullube kansa. Kusan tsawan 30 minutes yaji an bude door din, a tunaninsa Prince ne yace � yaya Prince just leave me alone�, shirun da yaji ne yasashi kara furta � please yaya Prince ka tafi, yaya bobo baya sona yanxu”yaye blanket din da akai ne yasashi waro ido ganin bobo tsaye hannunsa dauke da babban tray, akaran farko da kyakkyawar fuskar little ta fito, a shekaru bazai wuce shekara 21 ba dukda kyansa be gama fitowa ba kamar yan uwansa amma shima kyakkyawa ne na karshen karshe, dauke blue eyes dinsa yayi daga kan bobo zai koma ya kwanta � stay still� cewar bobo, sunkuyar da kai little yayi kamar zeyi kuka , ajje tray din bobo yayi kan wani table me zaman mutum 3,kafun ya karasa inda little yake , a gefensa ya zauna shima kafun ya kama hannun little � yaya bobo yayi lefi, am sorry kar a fada wa big boss ya harbeni �, dariya ce ta kwace wa little besan lokacin da ya rungume bobo ba, shima bobo rungumesa yayi kafun ya mikar dashi tsaye, dakansa ya dunga feeding ADEEL abincin da ya kawo masa shima ADEEL din na bashi abaki, saida suka kammala cin abincinsu kafin little ya kalli bobo� yaya bobo , big boss ya dena sona har yanxu ya ki dawowa fa�, bobo be ce masa komai ba sai wata karamar phone da ya dauko wasu number guda Hutu ya danna take a wajan aka dauka, little dake binsa da kallo, tsawan mintuna biyar Ba’ace komai ba kuma babu alamun za ayi magana ,”yaya� shiru yaji ba ayi magana ba � Assalamu Alaikum � ya kara fada kusan mintuna biyu kafun wata ratsatstsiyar murya ta daki dodon kunnansu � Wa’alaykumussalm �, daga nan ba a kuma cewa komai ba � Yaya� little ya fada kamar me rada � little I will called you back!� � kafun yayi kokarin yin magana aka kashe kiran gabaki d’aya ,� karbar wayar bobo yayi � kaga yayan naka yana meeting and zai kiraka , so don’t worry, and ya bani gift dinta , and if you guys need anything ku duba dakina ko na big boss, but ba fa kyauta na baka ba , kana fara aiki zaka biyani kudi na � rungumeshi little yayi cikin yaran larabci ya furta � Ina sanka yaya bobo na ,� love you too � yana gama maganar sa ya bar dakin. Shima tittle wani choco ya dakko cikin sauri ya sakko downstairs, “yaya Prince � yake kwallawa kira ,”Menene kake faman kirana ka gama fushi�, amaimakon ya amsa masa sai kashe masa ido daya da yayi � yaya Prince wajan simba zaka rakani , yau kwata kwata banganshiba �,kallan tara saura kwata Prince ya bishi dashi � dan iska ne Ance maka da zanje wajan wancan zagin, Kai da ka ga zaka iya ai sai kai tayi �, shima kallansa Adil yayi � shikenan Allah sai na fada wa yaya bobo , shima big boss sai na fada masa � da Sauri Prince ya riko hannunsa � Haba auta, wasa fa nake maka zo muje wajan simba din�, fitowa sukai cikin babban mansion kafun su nufi wata kofa, duk inda suka wuce sojoji suna sara musu, cikin wani babban cage suka shiga , Prince da ya shiga karshe sai be kulle kofar cage din ba, “Simba!!! Simba !!!� AdIL yake kira,wani gurnanin zaki ne ya fara tashi me tsoratarwa, inda gurnanin yake fitowa adil ya nufa ba ko tsoro tattare dashi,”Simba � ya kara kiran sunansa , wani katon zaki ne ya fito , yanda naga girmanshi nikaina sai da na razana, bakinsa ya bude kafun yayi wani kuka amaimaikon su gudu sai nufar kusan tosa da sukai kai, kansa Adil ya shafa “Simba yau duk ban gankaba � Abun mamakin shima Zakin da aka kira da simba, gashin kansa ya karkada masa kafun ya daga hannayensa ya dora ajikin Adil, wani irin farinciki ne ya kama adil kamar Wanda ya samu mage haka yake wa zakin wasa, Prince na gefe sai faman vidoe yake musu, ganin lokacin sallahr magariba ya kusa ne yace wa Adil suzo su tafi kar yaya bobo ya ne mesu, ba musu kuwa suka bar cage din.
Chapter 3 · 0% Book details