Sashe 82
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
idanu ganin kukan mata bame ‘karewa bane ya furta � da alama tana bukatar masu shan jini� da Sauri Abla ta furta “Kayi hakuri na dena “abun cinta ya nuna mata � oya cinye abincin ki � hannunta har rawa yake lokacin da ta d’auki Youghurt din , tunda ta saka shi a bakinta bata saukeshi ba , ita gabaki d’aya ta manta da suna zaune a wajan sabida yadda zakin Youghurt din ya yi mata mugun dadi dan arayuwarta bata ta’ba Shan yoghurt ba sai yau da little ya bata , yadda Tasha Youghurt din sosai hakan yayi musu dadi dan gabaki d’aya yoghurt din ta shanye sai data ga babu tukunna ta ajje cup , sai kuma kunya ya kamata ganin lokaci d’aya ta shanye farin abunda little ya bata dan ita Batasan ma yoghurt bane , babu Wanda ya nuna mata ya ganta kowa abincinsa yake ci, hatta fruit din da suka bata shima ta shashi sosai , suna gama breakfast din suka koma falourn gabaki d’ayansu banda bobo da ya fita , little da prince sai faman janta da iri suke tun bata sakewa sosai har ta sake kamar sunyi shekara guda take sai faman dariya suke wa junansu , uncle na gefe da jarida a hannunsa sai faman murmushi yake saki shi kad’ai, sun dad’e sosai suna hira ganin almost 12 little yasan a ko wana lokaci Big Boss zai iya fitowa shiyasa ya kalli fuskar Abla yaga tana murmushi, bayaso Big boss ya sata kuka shiyasa gabaki d’aya hope dinsa ya ragu sabida besan me big boss xai mata ma idan ya ganta dukda yasan bazai ta’ba korar taba tunda yace yana san zamanta a wajan , wani idea ne ya fad’o masa ganin anytime big boss zai iya fitowa , can d’akin kifayensu little ya ja ta , yadda taga kifayen suna motsi kwanin sha’awa ita kanta bata san lokacin da ta ‘karasa jikin glasses Dinsu ba tana shafawa, yadda suke motsi cikin kaloli masu burgewa sai sun baka sha’awa itama hakance ta kasance a ‘bangaran ta batare da tsoron ganin suna motsi ba ta soma shafa glasses din , ita kadai sai faman murmushi take saki , little na tsaye shima yana bin kifayen da kallo saida sukai kusan 40 minutes a d’akin , alokacin ya d’auka big boss ya fita daga falourn shiyasa suka fito daga d’akin little sai faman labari yake bata ita kuma tana masa murmushi kawai, saida suka zo tsakiyar falourn kamshin turaransa y dokesu gabaki d’aya musamman Abla da taji bugun zuciyarta ya canza lokaci d’aya ta dunga jin wani irin fad’uwar gaba ga kamshin da take ji na shigar mata hanci , yadda kamshin yayi mugun yi mata dad’i har wani lumshe idanuwa tayi tana ‘kara sha’kar daddad’an kamshin, ga wani irin da ta faraji lokaci d’aya da taji ‘kamshin turaran ,Little kuma gabaki d’aya kasa motsawa yayi Sabida ganin baki big boss zaune akan kujera yayi crossing legs d’insa ga idanuwansa da suke a lumshe , uncle na gefensa shi da prince , a hankali little yayi sallama yana shigowa cikin falourn, ita gabaki d’aya Abla bata san da zaman Big Boss ba sabida yadda kanta yake a sunkuye har ta ‘karasa shigowa cikin falourn Sabida yadda takejin zuciyarta , little yana shiga suka da Big boss ya nufa tare da zama a kan carpet yana yiwa Abla signal akan ta matso kusa dashi amma ita gabaki d’aya bata san yanayi ba sabida yadda ta sunkuyar da hanka ‘kasa tana tafiya , a shagwa’be little ya furta � Yaya Big boss � wani irin bugawa zuciyar Abla tayi da ‘karfi cikin sauri ta d’ago da idanuwanta , basu sauka ko ina ba sai kan kyakkyawar face d’insa da ya lumshe , kasa sha’kar nunfashi Abla tayi sabida yadda kyan Big boss yayi mugun rud’ar da ita da Sauri sauri zuciyarta ta cigaba da tsanan ta gudu, ga wani irin rawa da jikinta ya somayi lokaci d’aga , mugun tsoransane ya kamata gashi ta kasa d’auke idanuwanta akan sa musamman red lips dinsa da yayi mugun tafiya da ita sai kuma tsagar girarsa da ta zubawa idanuwa , tunda take bata ta’ba ganin kyakkyawa kamarsa ba dukda tsananin kyan dasu little suke dashi sai taga kamar nashi kyan na dabanne, tana cikin tunanin da ta fad’a ya soma bud’e eyes d’insa dan tun lokacin da little ya zauna a carfet yaji alamar ana kallansa , gabaki d’aya eyes d’insa ya bud’e basu sauka ko ina ba sai cikin idanuwan Abla da ta kafe shi da kallo, lokaci d’aya yayi mugun had’e ransa tare da tsuke fass d’insa sosai, wani irin kallo da ya jefa matane yasa tashiga hankalinta , cikin Sauri ta d’auke idanuwanta tana sunkuyar da kanta ‘kasa , gabaki d’aya ko d’an yatsanta ta kasa motsawa Sabida wani irin shakkarsa da ya kamata ,maida kallansa kan little da ya zauna a ‘kasa yayi , shima nasa raban kallon Big boss ya jefa masa , amaimakon ya Tashi daga ‘kasan sai ya shagwa’be masa face d’insa � please Yaya, please�, d’auke eyes d’insa Yayi daga kan little da ya shagwa’be fuska, cute red lips d’insa Big Boss ya d’an ta’be Batare da ya ‘kara kallan Little ba ko Abla data ‘kame kamar gunki ta kasa motsawa , shi kansa prince tsoran ya ce mata ta zauna yake kar Yaya ya bashi na sa kasan, uncle kuwa da gangan ya’ki tanka musu, kowa jiran reaction dinsa akan Abla yake , gabaki d’aya idanuwa suka zuba masa suna jiran suka abunda zaiyi mata , Allah sarki little sai faman Addua yake cikin zuciyarsa, a bazata little yaji muryar Big Boss � should I?� Da Sauri ya girgiza masa kai sai kuma ya bud’e baki � No yaya bari na zuba maka da kaina�, da kansa little ya zubawa Big boss abinci ga Abla da tun da ta tsaya ta sunkuyar da kanta itama ta kasa d’agowa , har wani zufane ta soma ganin suma gabaki d’aya babu me magana a cikin su, ganin ya soma cin abincinsa a tsanake yasa little sakin ajiyar zuciya , da sunga yana ‘ko’karin d’ago da eyes dinsa suke saurin d’aukewa dan sosai Big Boss ya tsani kallo, yadda yake tauna abincin hankali kwance kamar be san suna wajan ba amma gabaki d’aya ya karanci ko wannan su tsaf, kad’an yaji abinci yana gyara zamansa sosai a kan kujerar da yake , yanxu kam gabaki d’aya jira Suke suji Wana hukunci zai d’auka akan Abla dan idan yace No toh tabbas No d’innance babu me canzata, amma ga mamakinsu kwata kwata be tanka musu ba, sai ma diamond watched d’in hannunsa da ya kalla sau d’aya yana mi’kewa tsaye , har yanxu Abla tana a yadda take dan Dagaske ta kasa motsawa daga inda take tun kallan da ya jefa mata . Sosai little ya zuba masa idanuwa a shagwa’be, shi kuma amaimakon ya basa amsa sai ya lumshe masa idanuwansa , da’kyar ya iya bud’e cool husky voice d’insa , cikin ‘kasa ‘kasa da murya big boss ya furta � Take care �, sabida yadda suka nutsune yasa gabaki d’aya sukaji me yace , hatta Abla da taji saukar muryarsa saida ta lumshe idanunta. Bai kuma tanka musu ba ya nufi hanyar barin falourn , gabaki d’aya da ido suka bisa har ya wuce , yana fita gabaki d’aya suka saki a jiyar zuciya kusan a tare , cikin wani daka tsalla Little yayi hugging Uncle � uncle yayi approving ko?� Shima uncle murmushi ya sakar wa little yana jinjina masa kai , Big boss ba ‘karamin mamaki ya basu ba ganin gabaki d’aya be tankaba, tabbas little d’in ya cika little , tunda har ya amince wata ta zauna Sabida little , dukda be fito ya fad’a musu da baki ba , amma dole kam Abla tayi taka tsantsan dan kamar yadda yake saka su little punishment babu abunda zai hana ya’ki saka ta itama . � Daughter ki zauna mana � cewar uncle yana kallan ta, haka kawai yarinya ta kwanta masa arai , besan dalili ba yaji ita kad’ai ce zata iya yi masa aikin da yake so dukda be sani ba Daidai ne hakan abunda zaiyi ko kuma yana ‘ko’karin yin kuskure ne ?amma duk da hakan bazai ha’kura sai yayi abunda ya ‘kudurta cikin zuciyarsa.� A hankali Abla ta d’ago da idanuwanta ganin baya wajan gabaki d’aya sai kamshin sa da ya bar musu , ita kanta saida ta saki ajiyar zuciya , maganin ta little ya d’akko mata duk yadda yake da mugun tsoran shan magani yau little yana bata Tasha sabida gani take kamar kyakkyawan mutumin da ta gani d’azu yana wajan , cikin zuciyar ta kuma addua take ko aljani ne ta gani . Ta kasa sakewa gabaki d’aya kamar d’azu tun ganin big boss da tayi, saida duk maganar da little da prince zasuyi mata saidai kawai ta sakar musu ya’ke, amma bakinta gabaki d’aya yayi mata nauyi . Ana kiran sallahr azahar little ya rakata har d’aki shikuma ya koma suka tafi masallaci . Tana shiga cikin d’akin tayi saurin dafe saitin zuciyarsa , tana kulle idanuwanta taga fuskarsa lokacin da yake ‘ko’karin bud’e eyes dinsa , da Sauri ta bud’e idanuwanta tana karanto addua dan ita gani take kamar gamo tayi , ga kamshin turaransa da har yanxu take jinsa cikin hancinta , da tayi ‘ko’karin kulle idanuwanta zata ga kamar yana wajan , kallan da yayi mata d’azu sai da tantar cikinta ta kad’a musamman idanuwansa da yafi komai bata tsoro. Da kyar ta iya tashi tayi sallar azahar , sabida wani irin kasala da takeji , tana idar da sallanta little ya kawo mata fruits da yawa da yogurt shima ,lokacin da zai fita har ajiyar zuciya ta sauke ganin be ce mata ta Fito ba , kad’an ta iyasan yoghurt din dan ji take cikinta a cike yake taff batajin yunwa ko kad’an.