← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 139 OF 146

Sashe 139

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ADX FLORENCE U.S.A
**PRISON**
Tsaye suke cikin babban prison d’in ADX me shegen hatsarin gaske , da ya zamto d’aya a duk duniya baki d’aya me suna ADX Florence da ke ‘kasar America , prison ne da duk Wanda yayi gigin guduwa yake fitowa a mace, har zuwa yanzu da ba a ta’ba samun koda mutum d’aya daya ta’ba tsira daga cikin saba, shiyasa gabaki d’aya prison d’in yake da manya manyan criminals masu hatsarun gaske, tare mata kan tsaro sosai , sabida hatsarun wad’an da suke cikin sa.
Ga baki d’ayansu sanye suke cikin ba’ka’ken kaya , musamman Big Boss da gabaki d’aya mutum
Bazai gane saba sabida shigarsa, hatta ‘kafarsa sanye take cikin ba’kin takalmin David stone , da duk Wanda ya duka da takalmin nan sai ya ji a jikinsa , hatta fuskarsa baka iya ganin ta sabida Black facemask d’in da ya’ke face d’insa , gashin kansa sosai ya tufkesu a bayansa , hakan ya bawa bucket hat d’in da ya saka rufe masa ido , shiyasa idan basanın shine a wajan ba , babu mahalu’kin da zai gane sa da wuri. Bobo ma sanye yake cikin ba’kaken kaya kamar Big Boss , sa’banın shi face mask Kawai ya saka a kansa , sai gyaran gashin kansa shima da ya so rufe masa ido duk da bai saka hula ba. Suna tsaye cikin wani waje da idan mutum ya kallesa bazai ta’ba tunanin a cikin prison bane , kusan mintuna 10 suna tsaye a Wajan , time to time Bobo yana duba agogon hannunsa . Yanzu ma agogon hannun sa ya kalla duk da face mask d’in dake face d’insa mutum zai gane yayi murmushi ta ciki. A hankali ya far irga ,5,4,3,2,1, yana kai wa 1 ya furta done , lokaci d’aya wani irin ‘kara ya karad’e cikin prison d’in, cikin sauri aka bud’e inda suke tare da jefowa Bobo wani black Leda me d’an kauri , zip d’inta ya bud’e tare da ciro guns d’in da suke ciki, d’aya ya mi’kawa Big Boss , shima ya saka ta sa daga bayan rigarsa kamar yadda Big Boss yayi. Cikin sauri suka bud’e ’kofar Suka futa , da Sauri Sauri gudu gudu Suka nufi inda yawanci criminals d’in suke cin abinci ga mata kan tsaro sosai a wajan ta yadda babu Wanda zai yi ‘ko’karin yin kuskure. ‘Karan da suka ji ma d’aya daga cikin prisoner d’in ne ya samu na sarar samun gun ya saita akan d’aya daga cikin masu tsaran wajan. Daga gefen sa wani mutum ne da ashekaru zai wuce shekara kamshin, jikinsa duk tatoo d’in spider ne a jiki ba’ki hatta face d’insa , gashi ya sa anyi masa surgery a fuska ta yadda aka iya ganin ‘kofofin hancin sa , bakinsa idan ya Lura sosai zai gane alamar raba lefen da yasa akayi masa . Tunda d’aya daga cikin prisoner d’in ya samu gun yake binsa da idanuwansa da shima aka canza masa zuwa ba’ki, shiyasa gabaki d’aya ya canza halitta zuwa wani abun daban sai kace ba mutum ba . “Ka ajje bindiganka”shine abunda wasu masu tsaran suke cewa , cikin zafin nawa me ri’ke da gun d’in ya ciro bindigar da ya ‘boye a bayansa ya je fawa d’aya daga cikin prisoners d’in, shima cikin sauri ya kama tare da saita ta daidai kan d’aya daga cikin masu tsaran, a daidai lokacin da su Big Boss suka shigo wajan da gun a hannun su , cikin kakkausar murya Big Boss ya furta � ku ajje maka manku� kamar ‘kara tinzirasu yayi cikin sauri suka saka kuna ma zasu yi harbi, cikin sauri Bobo ya furta � ya isa haka ! Me kuke bu’kata ?� Gun d’in hannun Bobo prisoner din ya kalla tare da nuna wani daga cikin d’an uwansa prisoner da gabaki d’aya aka saka su kwanta , cikin sauri ya furta � your gun! Ko kuma na harbesa �, hannu Bobo ya d’aga sama tare da sunkuyawa ahankali zai ajje gun d’insa , akaro na biyu Big Boss ya furta � ku ajje makamanku !� Yana furta hakan yaja kunama shima zai yi harbi , da sauri Bobo ga bangajesa Gun d’in sa shima ya fad’i ‘kasa , pito na tsayen yayi , cikin sauri d’aya daga cikin prisoner d’in ya d’auke gun d’in Big Boss tare da saitashi akanka , gabaki d’aya suma masu tsaran sai suka saita bindugogin su , cikin sauri Bobo yake musu alama da asu ajje gun d’insu, suna cikin hakan Big Boss ya shammaci na bayansa lokacin da ya kai masa irin irin Bugu da saida gun d’insa yayi ‘ko’karin fad’uwa , Big Boss ya kwace. A bazata d’aya daga cikin prisoner d’in ya harba Bullet , daidai lokacin da Bobo zai jiyo , cikin rashin sa’a Bullet d’in ya same sa , Big boss na ganin haka shima ya harbi d’aya daga cikin su a ‘kafa bindigarsa ya bawa Bobo shi kuma wani security ya jefo masa tasa , Big Boss na kama d’aya daga cikin su ya sakar masa naushi a kumatu, saura guda d’aya da yayi saurin ja baya , gabaki d’aya sai ya nemi rud’ewa ganin yadda aka saba team d’insa za’a fitar dasu , cikin kururuwa yayo kansu shima yaji saukar bayan bunguka akansa , gabaki d’aya yayi baya zai fad’i, guy d’in dasu me tanbarin spider yana ganin hakan cikin sauri ya tare sa tare da rungumesa, batare da sanin ma’aikatan wayan da suka yo kansu ba , ya saka wa guy d’in wani abu a aljihu yana ja baya , shima Big boss hannun Bobo ya ri’ke suka fita daga wajan , ga prisoners d’in dasu ma gabaki d’aya aka sa’besu akai waje dasu , Big boss na fitowa shugaban prisoner din ya sara masa , kansa kawai Big Boss yayi knodding lokacin da yake cire bucket hat d’in kansa . Har inda helicopter d’insu Big Boss suke shugaban prisoner din nan ya rakasu, ganaki d’aya prisoner guda ukun a ciki aka saka su , sai Big Boss da Bobo da suka hau wani helicopter d’in, ragowar helicopter guda biyu kuma su Victor ne a cikin ta. Cikin ‘kan’kanin lokaci jirginsu ya tashi sabida gabaki d’aya wajan prisoner d’in babu wani abu me rai ko mutane a gabaki d’aya wajan gabaki d’aya .
Cikin sauri d’aya daga cikin sojojin ya nufi Bobo lokacin da yake ‘ko’karin cire rigar jikin sa ta sama , hannu kawai Big Boss ya saka ya yaga hannun rigar inda aka harbi Bobo, lumshe eyes d’insa yayi kawai tare da matsawa gefe , shima soldier d’in ya samu yayi wa hannun Bobo dressing bayan ya cire masa Bullet d’in ciki.

**************
************************

***NYC ***
Chapter 139 · 0% Book details