← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 146

Sashe 18

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bobo yana shiga cikin falon ya tarar da bakowa a ciki, direct d’akin uncle iron man ya nufa, yana shiga ya tarar dashi a zaune kan dadduma hannunsa d’auke da Alkurani mai girma , sallama yayi masa saida ya ga ya amsa masa tukunna ya shigo cikin d’akin, kan dannuman da uncle yake zaune shima a kai ya zauna tare da d’ora hansa a kan kafad’ar uncle din, � kayi kewar sa kenan�, murmushi bobo yayi duk da ya gane me uncle din yake nufi amma be ce masa komai ba, shima uncle din be sake ce masa wani abuba sai tray d’in da ya nuna masa � Little yace na tabbata kaci abinci, if not bazai yi bacci ba �, tray d’in bobo ya kalla shima tare da janyoshi � uncle kaima kasan shiriritan little da yawa yake, ni ya fara samun ciwan kai , and yasan bazan zauna ban ci abincin ba kamar Big boss �, rufe Akur’anin uncle yayi� Little kenan! Yayi missing d’in babban yayansa,and shine auta ka bari duk lokacin da kashirya aure zai dena sa maka ciwon kai,� kallan uncle yayi ya d’auke kansa Sabida maganar auren da yayi , sosai yaci abincin da James suka dafa ya kora fresh juice yana hamdallah, ganin uncle yana ‘ko’karin zama a ‘kasane yasa bobo yayi saurin mi’kewa � uncle ya kamata ka huta haka , dare nayi ya kamata ka kwanta ka huta�, jinjina masa kai uncle din yayi kafun ya furta� shikenan amma bari naje na ‘kara duba yaran nan�, da Sauri bobo ya girgiza masa kai � No uncle , bari zanje na duba maka su,kaima kana bu’katar Hutu�, be jira amsar uncle d’insa ba ya zaunar Dashi kan gado kamar Wanda ya samu little , har da lullu’ba masa tattausan blanket d’insa fari me shegen kyau da laushi. Saida bobo ya tabbatar uncle ya kwanta kafun ya fito daga d’akin hannunsa ri’ke da tray abincin da yaci, yana fitowa James dashi da wani soja maisuna Samuel suka ‘karasa inda bobo yake da Sauri suka sara masa zasu Amshi try din hannunsa ya girgiza masu kai , � u can all go now (zaku iya tafiya yanxu )� , yana kai karshen maganarsa ya ajje tray din akan dinning, ya wuce elevator , duk sai da suka ga wucewarsa babu Wanda ya motsa sai bayan mintu na biyu , cikin Sauri James ya wuce dinning yana ‘kara gayawa .

Bobo kai tsaye d’akinsu Little ya shiga gaba ki d’aya sun kwanta sabida yadda d’akin yayi duhu, light d’in d’akin ya kunna, da sauri ya ‘karasa shigo ciki sabida ganin yadda little yake bacci a zaune , prince kuwa baccinsa yake hankali kwance cikin half gareran wando ko singlet be saka ba , ga Acn d’akin sosai yake fitar da sanyi, gyarawa little kwanciyarsa yayi bayan ya Tottofa masa addua, gadon prince ya nufa shima, 2 fingers dinsa ya had’a ya daddage ya d’akawa prince a damtsen hannunsa, da Sauri ya farka kamar zaiyi kuka ganin Bobo tsaye a kansa yayi saurin kallan jikinsa, bashiri ya nufi d’akin dressing d’in su ya shirya cikin night wears d’insa cikin d’an sosa kai ya furta � good night yaya bobo�. Kanshi bobo ya d’aga masa kafun ya furta night too , yana kwantawa yaci gaba da baccinsa , girgiza kai kawai bobo yayi saida ya tabbatar they’re all safe sannan ya bar d’akin, duk da dare yayi sai da ya ‘kara tabbatar da lapiyan komai kafun ya nufi bedroom d’insa , shaf shaf wanka yayi ya shirya cikin flannel pajama ash colour , Daidai bakin windows d’akinsa ya tsaya ko alamar gajiya babu a tattare dashi, motocin da su Robbert suna fita ne suka shigo cikin gidan , cikin low speed, direct wajan wani parking spaces suka nufa inda jerun manyan motoci suke , cikin sauri Robbert da captain suka nufi motar bayansu, wasu samari biyu yaransu suka fito dasu waje d’aya sai faman zaginsu yake cikin turanci yake furta � kasan ko ni wanene da zaku kama ? Dukanku sai kunyi na dama daga rana irin tayau dukan ku sai kun bar aiki har banzan o ganku…� be kai ‘karshen zancan ba Sabida naushin da yaji a both side dinta , cikin azaba ya bud’e baki zaiyi ihu Robert ya fesa masa wani abu me shegen d’aci da yasa ihun guduwa , d’aya guy din kuwa gabaki d’aya a maye yake sai faman tangad’i yake ,duk abunda suke bobo yana kallansu , one of his work phone ya d’auka tare da danna number 1 , cikin ‘kan’kanin lokaci phone work d’insu Robert ya fara aiki ,muryar bobo da suka ji yasa suka ‘kara daidaita da sara masa dan sunsan yana ganinsu “ina cikon na ukun?�, sarawa Robert yayi cikin girmamawa ya furta � baya town sir �, daga ‘bangaran bobo yana jin hakan ya saki wani simple smile da ya ‘kara masa kyau , kit ya kashe wayar ya nufi bed d’insa.

🍃🍃🍃🍃🍃

THE NEXT DAY

Tun kafin bobo ya fito ko ina na gidan angyarasa cikin zafin nama sabida gabaki d’aya cikin gidan babu mace ko d’aya a gidan koda masu aikine , gabaki d’aya sojojine suke aiki a gidan hatta abinci da gyaran gidan sojojine sukeyi babu single mace a cikin gidan da sunan mai aiki. Kamar yadda suka saba kullum , musulman cikin za a yi sallah tare dasu, ragowar kuma suna kula da tsaran gidan , kamar Robert da kullum in bobo zaiyi sallah shima yana bakin masallacin ri’ke da bindigarsa.
Ana idar da sallah kowa komawa yayi ya shirya cikin kayan training d’insu, sojojin gabaki d’aya dogon wandan sojojine a jikinsu sai singlet da suke sawa sanyin safiya na Busasu amma ko a jikinsu, prince da little ma gabaki d’ayansu yau sun shirya da wuri har sun Riga uncle iron man shiryawa, ‘karfe 8:30am suka gama motsa jikin su, little sai faman duba inda bobo yake amma be gansaba tunbayan idar da sallar asuba, prince kam ko ajikinsa dan yasan inda yake, kai tsaye dinning ya nufa yana jiran uncle da su little.little Kuwa bedroom d’in bobo ya’kara duba wa still baya ciki.”yaya prince ina yaya bobo ? Banganshi ba ?�, banza prince yayi masa tare da danna wani abu kamar bell dake kan dinning da Sauri wasu sojoji sanye da black suit su biyu suka fito atare ko wannansu cikin girmamawa suka sara masa� serve me �, kawai prince yace musu sabida gabaki d’aya bashi da jumurin yunwa, cikin cika umarninsa suka fara bud’e masa manyan warmer din kan dinning , saida ya za’ba abunda ya keso tukunna suka fara serving d’insa cike da ‘kwarewa, be dad’e da fara cin abincin ba uncle da little suma duk suka ‘karasa , ynxu su james ne suka yi serving d’insu duk yadda akai da little ya Za’bi abunda zaici ‘kin kula kowa yayi , hatta abincin ‘kin ciyayi sai hot coffee da shima ko rabi besha yace ya ‘koshi, gabaki d’aya Prince da uncle kallansa sukai basu ce masa komai ba musamman � wannan rigimammen yaron yanxu ma wata rigimar kake shiryawa ko, toh wallahi ba ruwana a ciki tsakaninka da yayyunka � duk cikin zuciyar sa prince yake wannan maganar , shi kuwa uncle murmushi kawai ya saki dan yasan inda rigimarsa ta dosa.mi’kewa little yayi ya nufi wata door , prince zai tsayar dashi uncle ya hanashi .
Chapter 18 · 0% Book details