← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 146

Sashe 105

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

✨✨✨✨� MONDAY Da wuri Abla ta tashi yau tun bayan sallar asuba da tayi ta kasa komawa , sanin cewa Little ya fad’a mata da wuri zasu fita yasa bata zauna ba ta gyara d’akin ta wanke toilet kamar kullum , tana yi tana duban agogon gudun kar lokaci ya ‘kure , ita kad’ai sai faman sakin murmushi take ga murnar fal cikin zuciyarta, wai Itace zata fara zuwa Makaranta, Sabida zumud’i jiya bacci rabi da rabi tayi,cikin sauri ta fito daga cikin d’akın, babu kowa sai hasken fitila , batare da damuwar komai ba ta nufi ‘bangaran simba , yau ko tsayawa magana da shi batai ba tayi wucewarta, tazo zata shiga cikin gida ta had’u da little da prince ,� yaya prince ina kwana , yaya little ina kwana ?� Kusan lokaci d’aya suka samar mata murmushi me ‘kayatarwa kamar had’in baki kuma suka amsa � kintashi lapiya LIL?� Da murmushi akan fuskar Abla ta jinjina masu kanta dan yau ko murmushin face d’inta ya kasa ‘boye tsananin farin cikin da tashiga ,� Let’s go LIL, kinsan yau akwai school ya kamata kiyi breakfast sannan ki shirya , it’s now 6:40am , and kinga 7:35am to 7:40am zamu bar gida , okay ?� Suna cikin tafiya Abla ta furta � okay yaya � a haka suka ‘karasa cikin gidan Abla ta nufi d’akin ta dan kar suyi latti, suma su little d’akinsu suka koma dan su shirya Sabida gabaki d’aya yau ko training bazasu yi ba Sabida Ablansu. Tana shigewa d’aki bata zauna ba toilet ta wuce tayi wanka, cikin mıntunan da basu gaza 15 ba tafito daga toilet d’aure da wani pink robe na wanka , yadda fuskarta take ta ‘kyalli mutum sai ya d’auka abu ta shafa , tana zuwa gaban mirror ta cire abun kanta take a wajan gashinta da Big Boss yasa ta yanke ya fito , da tuni da abunda zata tafi makaranta yau, � Allah sai ya saka mun ai , kuma zan gyara gashina tunda yana da saurin fitowa d’an ba’kin kuma shida Allah�, cewar Abla tana ‘karewa kan nata kallo da yake black colour sosai . Wani pink Baby oil ta d’auka ta shafa a jikinta , duk uban mayukan da suke wajan bata shafasu ta fi shafa baby oil d’inta , tana gamawa inda ta ajje akwatin kayan ta nufa sabida bata samu damar bud’e su ba tun jiya , tun da ta bud’e ta kasa motsawa Sabida yadda kayan sukayi masifar yi mata kyau tun kafun ta sanya a jikinta , yadda taga ko wanne da set d’insa a had’e yasa ta zaro set d’aya, bayan ta mayar da jakan, underwear d’inta ta fara sakawa kafin ta d’auko Dark blue d’in wandan da ta ciro , ita kad’ai sai bin wanda take da kallo kamar wacca aka gwada dan sosai ya zauna a ‘kugunta, white shirt d’in ciki ta saka itama Daidai jikinta , kamar wacce ta san kan tsarin shigar haka tayi tokking d’inta cikin wandon, daman Abla akwai san yin dressing Allah ne be yi ba sai yanxu, kafun ta ‘kara saka komai turare ta fesa ka d’an , d’an ‘karamun half rigar da ake d’ora wa a sama ta saka , itama Dark blue dan ta ta’ba ganin yadda ake sawa a cikin system d’in da little ya bata .cikin Sauri ta d’auko babbar dark Blue din rigar sama da ta sakko mata har kusan Gwiwa duk da bata ‘karasa ba sai mad’aurinta da ta d’aure . Gaban mudubi Abla ta ‘karasa , Yadda ta ga ta koma ita kanta saida tayi mamaki , tanbayar kanta take Anya Ita ce kuwa ? Dan ba ‘karamun had’uwa Abla tayi ba, musalta yadda kyan da tayi ma ‘bata baki ne , ga white glowing skin d’inta da ya ‘kara haskata cikin kayan, har yanxu ta kasa gaskatawa ita d’ince ko canza ta akayi, � Tubarkallah Masha Allah tuf tuf� cewar Abla bayan ta gama ‘karewa kanta kallo, white sock d’inta ta saka mara tsaho yar guntuwa , wani medium white# hijab ta d’auko da ko ‘kirjinta be wuce ba amma sabida yadda kayanta Suke asabe babu ta yadda shape ko wani ‘bangare na jikin Abla da ya fito. Beret d’in kan gadon ta d’auko tana ‘kare masa kallo , batasan yadda ake sawa ba shiyasa ta rike a hannunta kawai , ganin befi saura mintuna 10 su tafi ba ta d’akko white shoe din da uncle ya bata , yadda Abla ta fito a cikakkiyar d’aliba zata burgeka, ga kyau Allah ya bata, ga sanin ya kamata duk da batayi makaranta sosai ba amma tayi na islamiyya kuma tana alfahari da hakan, a karo na ba ‘adadi ta ‘kara kallan kanta tunda babu school awajan , bata tsaya ‘bata lokaci ba ta fito daga cikin d’akin hannunta ri’ke da beret d’in da ta kasa sakawa. Lokacin gabaki d’aya familyn suna zaune a falour banda Big boss hatta Bobo yana falour yau, little ne ya fara hangota, cike da wani irin excitement da mamaki ya mi’ke tsaye yana furta “oh my God , you look so awesome, adorable,cute , beautiful,oho lil � gabaki d’aya kallan direction d’in da little ya kalla suka kalla, cikin lokaci ‘kan’kani suka fara furta � Tubarkallah Masha Allah�, wani irin kunya ne taji yana kamata , cikin sunkuyar da kai ta ‘karaso wajan, a hankali ta gaishe da uncle , ya amsa mata cikin sakin fuska, gaishe da bobo tayi lokacin da yake binta da wani irin kallo da shi kad’ai ya san ma’anarsa , cikin muryarsa ya furta � kinyi kyau a cikin uniform dinki� kanta a sunkuye ta saki murmushi tare da furta � nagode sosai yaya bobo�, turn d’insu little tayi tana kallansu cike da murmushi da har saida dimple d’inta ya lotsa � yaya prince ina kwana ?� Amaimakon ya amsa shima sai ya furta � Tubarkallah Masha Allah , Lil Sis kinga yadda kikai kyau ? � still murmushi tayi masa batare da ta ce komai ba ,� wait wait ! Nifa I think ko lokacin da nake zuwa school Lil ta fini kyau a kayan makaranta ko ?� Cewar little yana tanbayar prince , da Sauri prince bashi amsa da � yeah ! Ni karku fara rud’ar dani , because sister kinyi more than kyau �. Mi’kewa tsaye bobo yayi yana kallan uncle � uncle wad’annan yaran idan na biye musu zasu ‘bata mana lokaci , sai mun dawo�, kansa uncle yayi knodding kafin ya d’aura da � ku kula please �, oya let’s go all � cewar bobo yana nufar ‘kofar fita har lokacin beret d’inta tana hannunta bata saka ba , suna fita wasu manya ba’ka’ken motocine kusan guda 5 sai ta tsakiyarsu da tafi gabaki d’aya sauran motar kyau duk da kasancewarta black colour itama , yau gabaki d’aya sojojin da zasu fita dasu ba’ka’ken kayane a jikinsu sai ba’kin glass da yake kan fuskarsu, Robert ne ya bud’e Musu mota , little da Abla suna back seat kamar wancan lokacin sai bobo da prince da suke middle seat, cikin wani unique way motocin suka bar gidan, duk inda motocin nan suka gifta sai sojoji sun sara musu, ko tsayawa traffic basa yi da motocinsu sun danno kai za a bud’e musu hanya. 20 minutes ne ya kai su babbar makaranta HORACE MANN SCHOOL, tundaga tsarin gidin makarantar da building d’insa mutum zai san ba ‘karamun kud’i aka kashewa makarantar ba , makaranta ce ta Wana da wane , makaranta ce da ya’yan masu kud’ine kawai suke da zarrar shiga makarantar Sabida yadda take da tsad’a sosai , sosai makarantar ta ‘kawatu ta ko ina , tunda babban gate akai scanning motocinsu lokacin da suka shiga , babbar makaranta ce sosai me shegen girma da ‘kawatu wa , ga abubuwan zamani na stundent, gabaki d’aya motocin nan cikin harabar makarantar suka danno kai lokaci d’ad’d’ai kun student zaka gani awajan da alama sun shiga cikin class ne , Daidai wani medium building motocin su sosai parking, daga wace wasu malamai ne kusan guda 4 , mata 2 , maza 2 sai faman sakin murmushi suke lokacin da suka ga motocin su bobo, kallanta little yayi � sis ya naga ban kisa beret d’inki ba �, kamar zatayi kuka ta furta � ban iya sawa ba � kar’ba little yayi ya saka mata a kanta tare da karkatar mata da ita � haka ake sawa ok ?� Kanta ta jinjina masa tana furta � thank you �. � let’s go all � cewar bobo , face mask little ya d’auka ya saka a face d’insa , itama Abla sawan tayi ya zamo ba’a ganin face d’insu gabaki d’aya sai kyawawan idanuwansu masu matu’kar ‘kayatarwa, yanxu ma Robert ne ya bud’e musu motocin , tun kafin su fito sojojin sun zaganesu gabaki d’aya ko hangosu ba’a yi , Abla ce ‘karshen fitowa , � welcome sir ! Welcome � cewar wata baturiya da alama tasan da zuwansu yadda take faman gaishesu a girmame, kansa bobo ya jinjina mata lokacin da take nuna musu hanya , haka suka hau ta elevator suwa second floor , Robert da captain ne kawai suka biyo bayansu gabaki d’aya ragowar sojojin suna waje sai faman zare ido suke. Office d’in da suka shiga babban gaske ne , me shegen kyau , ga wasu set d’in kujera Ash colour masu kyan gaske, akan kujerun suka zauna bayan Dr din ta bawa bobo wasu files ya ciccike , yana gama wa ya mi’ka mata , cike da girmamawa ta amsa tana ‘kara dubawa kafun ta washe masa baki � you guys don’t have to worry , tunda sir bobo ya riga da yayi mun bayanin komai tuntuni , yanxu class kawai za’a bata bayan d’an tanbayoyin da Dr Haris zai yi mata kad’an, and wanna cards d’inta ne , ta ‘karasa tana d’aiko wasu card guda uku � d’aya is for her meal ko me take bu’kata zata iya kar’ba a captaria, the other one shi kuma all her necessary school things za a bata su tundaga kan school bags , shoes, book etc and the last one na library ne , hope you get it all �, okay thank you � cewar
Chapter 105 · 0% Book details