← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 146

Sashe 37

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Eshaal ba ‘karamin aikatuwa tayi ba a kitchen , ita kadai sai faman aikin girkin baby take , sallah ne kawai ki dakatar da ita , lokacin da ta kammala girki a gajiye ta fito falon, yanxu babu momcy a falon sai baby ita kadai da take kallo, tayi crossing legs dinta ga wani d’an iskan cingum da take ci sai faman bada sautin kas kas kas , tana ganin shigowar Eshaal ta ja dogon tsaki, “Abincin suna dinning �, abunda Eshaal tace mata kenan tana kokarin juyawa , � ke � cewar baby, d’an juyowa tayi tana kallan baby, � haka aka koya miki? Ko uwarki da take kabari haka ta koya miki idan aka saki abu�. Rai a’bace Eshaal ta kalleta , amma bata ce mata komai ba sai danne abun da tayi a zuciyar ta , sau dayawa tana jin zafin maganganun Baby amma tana rabuwa da ita ne sabida a zauna lapiya tasan yanxu tace zata biye mata itace a ruwa , ita zata wahala , a gadarance baby ta furta � biyoni� tana nufar dinning din da Eshaal ta cika ga kamshi sai faman Tashi yake , amma baby na zuwa sai ta fara toshe hanci wai bata san warin aroma din be mata va ,kallanta kawai Eshaal tayi har ta Bud’e pepper chicken din da yasha kayan had’i sai faman tashin ‘kamshi yake , duk Wanda yaga kazar nan sai ransa ya biya sabida yadda ta had’u, ta’be baki baby tayi kafun ta bud’e next warmer din da kamshin fried rice ke tashi ga veggies din da ya kara ‘kawata shi, gefe d’aya ga coslow da lemukan da Eshaal ta had’a, a yangance baby ta furta � serve Allah yasa na iyacin ‘kazantar nan �, anan ma Eshaal ta so ya ‘ba mata magana amma ta rabu da ita tasan tana tankamata baby ba akanta zata huce ba akan Amma zata huce shiyasa take shanye duk abunda baby take mata sabida Amma, ba musu Eshaal tayi serving din baby in a unique way duk da ashekaru Eshaal zata iya girman baby da watannin da bazasu Gaza uku ba . Spoon d’in farko baby ta kai bakinta duk da abincin yayi mata dadi sai tayi saurin furzarwa tana wurgar da plate din ‘kasa gabaki d’aya abincin sai yazu , “wannan Wana irin dabbancine zaki yi mun wannan abinci sai kace wata dabba irin ki? Haka uwarki ta koya miki?� Tass Eshaal ta d’auke fuskar baby da mari, itama bata sauke hannuntaba taji saukar mari dama da hagu, a gigice Eshaal ta dafe kumatunta, tana d’ago da kyakkyawar face d’inta da Tasha mari , Dadynsu ne ya mareta , yadda taga ya had’e rai ne yasa tasha Jinin jikinta , ko kallo be isheta ba sai ma baby da ya kalla, itama tana ganin abunda yayi wa Eshaal ta shagwa’be fuska har da fashewa da kukan ‘karya , lokaci d’aya dadyn su ya rud’e ganin baby na kuka , ashagwa’be ta turo masa d’an karamin bakinta ,� Dady daman sai da na fad’a maka Eshaal ba ‘kaunata take ba ka kalli yadda ta mareni dan kawai nace bazan iyacin abincin da ta dafa ba , gaskiya dady shiyasa nace bazan koma u.s tare da ita ba Sabida zata zubarmun da class, in karatun kake so tayi kasamo mata ko makarantar kwana ce ta gwamnati dan dashi ta fi dacewa �, amaimakon yayi mata fad’a sai ma murmushi da ya sakar mata � don’t worry my dear, ko me kikeso shi za’ayi miki ai , ina momcy dinki take ban ganta ba � ta’be masa baki Baby tayi tare da ware masa hannu alamar ita ma bata sani ba � tace na fad’a maka ta fita ,so ni kuma na gaji bazan iya zuwa part d’inka ba shiyasa ban fad’a maka ba �, cewar baby sai faman ya tsine take , yanxu ma wani murmushin ya saki � Toh ba komai ai bansan ma tafita ba , amma ai duk yadda tayi shine Daidai , yanxu kishirya ni sai na kaishi shopping da kaina �, duk abunda suke Eshaal na tsaye dafe da kuncinta tana binsu da kallo , babu abunda ya fi tsaya mata arai kamar yadda Dadynsu ya nuna rashin wanzuwarta a wajan , gabaki d’aya hankalinsa kaco kam yana kan baby� Dady give me some minutes bari na shirya sai mu tafi�, okay my dear cewar kyakkyawan Bafullatanin da akallan farko zakaga tsantsan kamanninsa da Eshaal, Baby na barin wajan shima dady ya juya zai bar wajan, murya a sha’ke Eshaal ta furta � Dady �, wani irin kallan tsana dady ya bita dashi tare da jan wani dogon tsaki yana barin wajan, yadda yayi mata beyi mata dadi ba dukda ta saba da irin wad’annan abubuwan ko ma fiye da haka amma yanda yake nuna mata tsantsan tsana kamar bashi ya haifeta ba , wani lokaci har tanbayar kanta take Anya shine mahaifinta na gaskiya ko kuma wanine mari’kinta , tana tsaye a wajan baby ta fito cikin shigar ‘kananan yana da suka matse ta Amma ko a jikinta , d’an ‘karamin mayafin da ta d’akko a hannu ta ri’kesa , sai kantamemiyar wayar ta d’aya rike a hannu cike da yanga, tana fito wa dadynta ya fara tafa mata , fuskar sa d’auke da murmushi � my daughter kinyi kyau �,Thanks kawai tace masa , suna had’a ido da Eshaal ta kashe mata ido d’aya tare da kama hannun dads dinta , sunzo zasu fita baby ta juyo tana kallan Eshaal da tun d’azu bata motsa daga inda take ba “kishiga ki gyaramun d’akina kafun mu dawo, sannan kada ki kuskura wata ‘kazama tashigar mun d’akin har ta cika mun d’aki da warin jikinta , and lastly Kema ba yadda nayi dake ba sabida duk lokacin da na saki aiki sai na nemi abu na rasa , so be careful �, ta karasa tana jan hannun mahaifinta da sai murmushi yake sakar mata . Tana ganin fitarsu ta juya a guje ta nufi d’akinta, dakin da ko kwatan na Baby be kai ba , bayan set din gado babu wani abu na ado a cikin d’akin akwai da haduwa kwata kwata bazaka had’a shi da na Baby ba dan d’akin baby dakin yan gata ne da kome take so ake zuba mata sabo.
Kan gadanta ta fad’a tana fashewa da kuka me ta’ba zuciya , sallamar da akai ne yasa tayi saurin goge face d’inta tana share hawayen da suke ‘ko’karin zubo mata , yar aikin da tashi ga d’akin baby ce , da Sauri Eshaal ta saka murmushi akan face d’inta � Amma sannu da zuwa , aikine yayi mun yawa shiyasa kika ga d’azu banzo kinyi mun kitsan ba �, murmushi Amma ta sakar mata , cikin sanyayyiyar murya ta furta � kiyi hakuri, komai me wucewa ne � sai alokacin wasu hawaye Suka sake zubo mata � Amma nagaji da gidan nan, nagaji da abubuwan da suke , mahaifiyata ta rasu, mahaifina da nake tunanin xai Sharan hawayena ko rabarsa bayaso nayi, wacce zan kalla kamar uwata ta tsaneni, bayan ke babu me sona Amma , Wana irin lefi nayi musu haka da na cancanci irin wannan hukunci?� , kowa da irin tasa jarabawar Eshaal , Allah yana jarabtar bayinsa ta ko wace hanya bawai dan baya san suba , ah ah Sabida ya kwada imaninsu ne , ki dena saka komai a ranki duk lokacin da kikaji ranki ya ‘baci ki kunna karatun alkurani zai debe miki kewa �, kanta Eshaal ta jinjina � nagode sosai AMMA , nagode Amma dan Allah Amma ki dunga hakuri da abubuwan da baby take miki acikin gidan nan �, karki damu babu komai wallahi, � yanxu ma naga sun fita ne bansan me za’a dafa mata na dare bane shiyasa nace bari nazo na tanbayeki �, hawayenta Eshaal ta goge � Karki damu Amma yau baza muyi girkin dare ba , na Riga na dafa yana dinning , nasan yanxu kingaji ya kamata Kema ki dunga hutawa kinji Amma �, Allah yayi miki albarka � cewar Amma , itama cike da farincikin adduar Amma ta furta Ameen, Amma na barin d’akin ita kuma tashiga wanka , shaf shaf ta Fito kaya kawai ta saka sai turare kad’an , batasan lokacin da su baby zata dawo ba tasan kuwa intace bazata gyarawa baby d’akin ba wani karin drama ne zai faru da zata kwana tana kukan bakin ciki. Shiyasa bata zauna a d’akinta ba ta nufi na Baby dan ta gyara mata tunkafun momcy ta dawo itama .

🍃🍃🍃🍃
GERMANY
FRANKFURT
Chapter 37 · 0% Book details