← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 146

Sashe 103

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****** Abla kuwa tun lokacin da su Little suka koma cikin gidan suke janta da hira , dukda yadda take tsoran had’uwa da ita dan yanxu kam ta bashi shugaban malintar mugaye tunda ya yanke mata gashin kan ta, duk yadda taso gudu little ya ‘ki bata wannan chance d’in dan dole ta zauna sukai hira tun bata sakewa har ta warware gabaki d’aya, basu wani jima sosai ba suka wuce dinning dan yau fruits kawai unclee yasa akai masa d’akinsa , shiyasa susu uku kawai sukai dinner d’insu, suna kammalawa little yaje Zaije d’akı ya dawo, Abla tana ganin haka ta gudu d’aki itama , tana Tuna’nın yadda zata Kai masa coffee batare da ta ganshi ba . Ita kad’a a cikin d’akin sai faman masifa take kamar yana kallanta , lokaci zuwa lokaci kuma bud’e drawer da ta ajje gashin nata sai kuma ta kalli Wanda yayi saura akanta , ji take da za’a bata dama itama da sai ta aske masa gashin kansa tass , batasan lokacin da maganar da take so tayi ya fito fili ba � kuma wallahi kwalkwal zanyi maka kamar kod’ad’d’an farantin Zinariyya �, ita kanta maganar da ta fad’a ta bata dariya .
Ba ita ta sakko daga cikin d’akin ba sai wajan around 11 , lokacin gabaki d’aya babu kowa a falourn da alama ko wannansu ya koma part d’insa , Tuna’nı Abla ta soma akan ta tsaya ta kai masa coffee d’inne ko kuma itama tayi wucewarta dan a gajiye take yau , haka ta cigaba da Tuna’nın mafita , daga ‘karshe sai tayi deciding ta fara bashi coffee d’insa kar ya zuba mata kwando kwandon bala’in sa, Tun tana jiran dawowar sa har bacci ya d’auketa a cikin falourn.
Sai wajan ‘karfe 2am Big Boss ya shigo cikin gidan , yadda yaganta kwance akan kujera ne yasashi ya d’an ta’be lips d’insa kafun ya danna button d’in falourn , gabaki d’aya fitilun suka d’auke ya sama sai dum light mara haske , ko takan inda take be biba ya nufi part d’insa . karfe 3:20am fitsari ya farkar da Abla , lokaci d’aya ‘kirjinta ya buga sabida duhun da ta gani, da ita ‘karfinta ta kwalla ihu , tana faman dube duben hanyar guduwa , yadda take fusge fusge kamar wacce take ‘ko’karin ficewa daga cikin haryacinta, cikin kuka ta soma maganganun da ita kanta bata san me take cewa ba � Duhu , Wayyo dubu banaso, banasan duhu, Wayyo Allah na , please wani ya temaka mun dan Allah,� bata fi mintuna biyu tana maganganu ba Abla ta fice daga cikin hayyacinta gabaki d’aya ga kanta da ya soma sara mata sosai , amma dukda hakan ‘ko’karin neman hanyar barin falourn take , cikin Sauri take ta zagaye d’akin tana ‘ko’karin guduwa amma Sabida yadda ta kasa kwantar da hankalinta waje d’aya yasa bata lura da haske kad’an d’in da yake wajan stairs ba , burinta taga ta fita daga Wajan shiyasa ko kula da inda take ta kawa bata yi , har ‘kafarta ta daki wani waje tayi baya baya zata fad’i, da hannu d’aya ya ri’ke mata hannun duk da kasancewar cikin duhune , Abla kuwa tunda taji an ri’keta ta ‘kara fashewa da kuka tana fad’in � please ku kunna fitula , banasan duhu dan Allah �, be furta ko uffan ba ya kunna light d’in falourn , gabaki d’aya ta had’a gumi ga face d’inta da ya ‘baci da hawaye sosai , tana ganin haske tana soma a jiyar zuciya , ko uffan be ce mata ba ya juya ya bar wajan , itama cikin Sauri ta nufi d’akin tana sakin wani ajiyar zuciyar.

WASHE GARI
Tunda akai sallar asuba Abla bata koma bacci ba sai data gyara d’akinta sosai ta wanke toilet shima sannan tayi wanka cikin doguwar ‘bakar riga har ‘kasa , kamar tayi kuka duk lokacin da ta kalli gashin kanta ta gansa a aske , bata tsaya ‘bata lokaci ba yau ta kaiwa simba abinci har cikin d’akinsa , ganin be motsaba yasa ta ‘kara tura masa abincin, nan ma still yana zaune ba kamar da ba da duk lokacin da aka kai masa abinci zai mi’ke ba , kamar wata mara gaskiya ta sand’a zuwa inda yake , a hankali kuma kamar me rad’a ta fury “Simba ? Simba ? Baka jina ? Ka tashi ga abincin ka nan karkasa a sakani wani punishment d’in dan Allah kaji?”ganin har lokacin be motsaba yasa Abla ta ‘kara matsowa inda yake dan yanxu bata tsoranshi sosai � Simba ?� Nan ma still shiru simba be kula taba sai idanuwansa da yake motsawa , finger d’inta d’aya ta saka ta dankwali kansa sai ta daka tsalle tayi gefen ‘kofa, a karo na biyu still ganin be motsa ba ya ‘kara matsowa inda yake ta kara dan gwalar kansa , sosai ta matso inda yake tana furta � simba ? Dan Allah ko zabura ne kayi, tsakanin da Allah kar me gidan ka yace guba na baka kaga jiya yasa na yanke gashi yau kuma ina tunanin hanci ko baci zai sa na guntule ,”’ita kad’ai kamar wata me iskokai ta furta � Toh ko dai bashi da lapiya ne ? Oho Nidai nasan ban baka guba ba dan haka wallahi bazan tsaya a hukun tani ba � ko da zata fito daga d’akin sai data le’ka wai sabida kar wani ya ganta tukunna ta wuce ta bar wajan, ita kad’ai sai mita take a cikin zuciyar ta wai simba ya mayar da ita yar iska , Sabida tana masa magana (🙄🙄Abla dole Big Boss yace kina da almatsu tsai akanki, daman zaki yana magana ? Ko kema kinsha abunda yasha ne ?🙄🙄 Team Abla wallahi kuyi mata fad’a dan mu ba ruwanmu duka zata sha 🤭).

Tana koma cikin gida ta tarar da uncle shi kad’ai zaune a kan kujera, cike da girmamawa ta ‘karasa har inda yake ta gaishe dashi, � uncle ina kwana ?� Da murmushi akan face d’insa ya furta � Lapiya Lou daughter kin tashi lapiya ?� Itama Ablan face d’inta d’auke da murmushin ta furta � Lapiya Lou Alhmdllh �, suna cikin zamansu Bobo shima ya fito , cike da girmamawa ta gaishesa shima , a Daidai lokacin da su little suka fito � Sister yau har kin tashi ? Kwanda ma ki more baccinki na yau da gobe kafun ki koma school Allah , karkizo kina school kina lumshe musu idanuwa� cewar little , gabaki d’aya dariya suka saki Sabida abunda little ya nufa , kallan yaya bobo little yayi � yaya ina yaya Big Boss yake ?� Harararsa bobo yayi kafin ya furta � na siyar dashi , ina kasan kara ganin sa kaje kasuwa �, cikin d’an zaro ido prince ya furta � kai�.. yaya bobo, yaya big boss din zaka siyar ? Su kuma Victor da Anthony suna ina ?� Direct bobo ya bashi amsa da � suma na siyar dasu� yanxu gabaki d’aya kuma dariya suka saki jin abinda bobo yace , cikin dariya dariya little ya furta � ni fa yanxu ku dena sakani dariya sosai , sister zaki yadda na dunga rakaki school ?� Da murmushi akan face d’inta ta furta � eh � satar kallan inda bobo yayi yana d’an langwa’be masa � yaya ai zaku dunga bari na ina raka sister makaranta ko?� Da bud’ar bakin prince shima sai ya furta � Nima yaya please zan rakashi , tunda ba court zan dunga zuwa ba yanxu for a while � cike da tsokana shima uncle ya furta � Nima zan dunga rakasu “yanxu ma kusan tare sukai dariyar Sabida yadda sukamayar da abun joke , daga nan dinning suka nufa gabaki d’ayan sukai breakfast, sai da suka kammala su uncle suka dawo falour shi kuma bobo ya fita. Haka suka cigaba da hirarsu gwanin burgewa har Suka d’auko game sunayi.
12 nayi Abla ta koma d’aki ta d’auko system d’inta tana anfani dashi har lokacin sallah yayi , tana idar wa kuma tabi
Lapiyar gado ta kwanta .

******** Tun wajen ‘karfe 12:00 motocin sojoji suke yawa a cikin Garin New York , ta ko ina zaka tsarin ya canza Sabida sojojin da suke shigowa cikin Garin, hatta Chief da kansa ya shigo cikin Garin New York duk sabida Big Boss , shiyasa kowa yake taka tsantsan.
Cikin babban office dinsa da ya gaji da had’uwa ya zauna kan wani kujera white colour sai wani dattijon mutum da kana kallansa kasan ba ‘karamun soja bane, ya dad’e yana fama da mugaye, cikin shigar ‘kananan kaya , sosai yake kama da LG, fuskarsa d’auke da murmushi yake kallan Big boss da yayi mugun had’e ransa , cikin kwantar da kai ya furta � cool down Big Boss , she maid a mistake abunda tayi , and she will apologized, but ya kamata kayi hakuri yanxu , okay.? � Big boss zai yi magana Chief yayi saurin magana � please Son kar kace No , nasan halin ka sosai , just for my sake please , please ,please �, gashin kansa Big boss ya shafa kamar bazai ce komai ba sai kuma ya furta � it’s okay zata koma gida , but if she dare ta ‘kara saka ‘kafarta a inda nake , this time around ba Victor ko anthony ne zasu yi mata hukunci ba , I will do it my self � mamaki ne ya kama Chief ganin Big Boss ya ha’kura dan kusan halinsu d’aya shima Chief a zamanınsa kusan kowa tsoran sa yaje amma yadda akejin tsoran big boss ya wuce tunanin me tunani ,still da mamaki akan face d’insa ya furta � for real da gaske kake zata dawo � kansa kad’an Big boss yayi knodding , cikin farin ciki Chief ya mi’ke tsaye ya ‘karaso inda Big boss yake yayi hugging d’insa , � that’s my boy ! Thank you so much, I have to go now jirgina ya kusa tashi, Big boss yana mi’kewa chief yayi hugging d’insa � take care son�, okay Kawai big boss yace masa dan kusan wani lokaci halayensu d’aya ne yanxu ne chief yayi sanyi amma yana da mugun zafin rai duk de kai Big boss ba.
Chapter 103 · 0% Book details