← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 146

Sashe 107

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

not � cewar Eshaal , a tare suka fito daga class duk inda suka bi sai kallansu ake gani Eshaal yau tare da wata amma duk da hakan basu damu ba tunda sunsan Daga yau Abla bazata kuma tarayya da ita ba . Har office d’in Mr Mj Eshaal ta rakata amma bata shiga ciki ba ta tsaya a waje tana addua Allah yasa ba haukan da ya saba yiwa Cristian student din makarantar zai ce zai kwada mata ba , Abla tana shiga ta tarar shi kad’ai ne a cikin office din yana ganin ta ya washe mata hakwara tare da nuna mata Seat d’in zama , zaman kuwa tayi tana jiran jin me zaice Sabida gabaki d’aya she’s not comfortable , ganin ya zauna a chair din kusa da itane yasa ta d’an ja baya kad’an ‘kara matso da chair d’insa yayi � you’re new student right ? Ki cire face mask dinki mana let me see you sosai ,� Abla bata gama shiga mamakin halin saba taga yana ‘ko’karin ta’ba mata fuska zai cire mata facemask, da Sauri ta mi’ke tsaye, dariya yayi yana kallanta � what’s diş ? Come over here , you will get a lot of mask , and I will make you the overall � ya fad’a yana ri’ko hannunta , Abla bata san lokacin da ta d’aga hannu ta tsinka masa mari ba , harta fara tara kwalla a idanuwanta sabida ta kaici, ko kuma kallansa batayi ba ta bar office d’in, ran Mr Mj ba ‘karamin ‘baci yayi ba , babu student d’in da ya ta’ba gigin marinsa kamar yadda Abla tayi , sosai ransa ya ‘baci , amma da ya tuno yadda yake sha’awarta sai ya saki wani murmushi da shi kad’ai yasan ma’anarsa � I most get you no matter , kin burgeni and I will teach you a lesson marina da kikayi� ya ‘karasa yana shafa gaban wandansa kafun ya saki wani yan iskar dariya shikad’ai. Abla tana fitowa ta tarar da Eshaal na jiran ta , itama Eshaal tunda taga reaction d’in Abla tasan Mr Mj yayi mata halin nasa ne , a hankali Eshaal ya furta � kiyi hakuri haka halin Mr Mj yake sai kinyi hakuri da halinsa kinji ?� Kanta Abla ta jinjina mata kafun ta furta � thank you � ganin lokaci na ‘ko’karin wuce wane Eshaal ta ja ta zuwa capterian makaranta, yadda yake da kyau da tsari mutum sai ya d’auka wani Restaurant d’in ne ga chairs a Wajan da ban da ban wasu student na kai wasu kuma karban abunda zasu ci, card d’insu suka nuna lokacin da zasu shiga, tunda Suka shiga nan ma kusan gabaki d’aya student din zuba musu ido sukai ganin yau Eshaal da wata dan Baby har ta riga ta had’asu acikin restaurant d’in, Abincinsu sukai order dukda ma ‘karfin yi Eshaal ce tayi musu sabida ita bata san kan abincin su ba , gashi duk ta ‘ki sakewa Sabida yadda taga ana binsu da kallo, can nesa da student suka koma suka zauna sai a lokacin Abla ta cire facemask dinta , kyakkyawar fuskar Abla ta fito sosai , d’an kallanta Eshaal tayi kafin ta furta � you’re so beautiful , da alama shiyasa kika kulle face d’inki� murmushi Abla tayi mata da har saida jerarrun hakwaranta suka fito kad’an , a haka suka soma cin abincin duk da Abla ba wani ci take ba Sabida yadda taka an ‘kara zuba musu ido musamman yadda aka ga ta cire mask d’in fuskarta , suna cikin ci aka bud’e kofar da karfi gabaki d’aya d’ago wa akai aka kalli ‘kofa banda Abla , daman ita Eshaal ta san ko su wanene “BAD BOYS , BAD BOYS , BAD BOYS� shine sunan da student suke faman fad’i lokaci guda , wasu mazane guda biyar guda biyun cikinsu zakaga turawane sabida yadda skin din su yayi yayawur d’ayar daga cikin su kuma ba’kar fatane sai wasu guda biyu da kallo d’aya idan kayi musu zakagane fulanine amma gabaki d’ayansu ko wanne da kitso akansa ga wani zazzago da wando da sukayi, d’aya daga cikinsu da ya fi kowa d’aura fuska ya soma binsu da kallo d’aya bayan d’aya dan duk Wanda ya ke a makarantar yasan su wanene BAD BOYS dan basu da mutunci ko kad’ai ga rashin kunya da take d’awainiya dasu , duk Wanda suka ga dama su taka sau uke kenan suna repeating Sabida wasa da suka sa da rashin mutum ci a cikinsu kamar kamar be , Baby ce ta shigo wajan daman friends dinta ne tana ganin su tayi shewa tare da furta � BAD BOYS � bafullatanin cikin sune ya mi’ka mata hannu suka tafa, daman ita ce ta kirasu da ido ta nuna musu inda su Abla suke , tunda ya kai idanuwansa wajan ya kasa d’aukewa sabida lokaci d’aya wani kibiyar soyayyar Abla ta shiga cikin zuciyar sa kowa nutsuwa yayi yaga me BAD BOYS zasuyiwa su Eshaal dan ba sau d’aya ba ba sau biyu ba suna ciwa Eshaal mutumci a bainar nas, a gadarance ya kalli Eshaal tare da furta � ke !� Dan d’agowa Eshaal tayi ta kallesu, Abla ya nuna mata cikin bada umarni ya furta � kawo mun wannan yarinyar nan wajan � kallan Abla tayi kad’an kafun ta furta � yana kiranki � banza Abla tayi mata , a tausashe Eshaal ta ‘kara furta � yana miki magana plx� kallanta Abla tayi kafun ta furta � kin gama cin abin cinne?� Da Sauri Eshaal ta d’aga mata kai dan batasan Abla ta shiga Sabgar BAD BOYS, mi’kewa sukai kowa yayi tunanin Abla wajan su Bad boys din zata har Eshaal kuwa, ganin tayi gefe zata wuce ne yasa wanda yayi wa Eshaal magana ya sha gabanta “ke har wacce ana miki magana zaki share mutum � banza tayi masa zata wuce ya ‘kara shan gabanta Sabida yadda ransa ya ‘baci yasa ya d’aga hannu ya tsinka mata mari gabaki d’aya wajan ihu ya d’auka , rai a ‘bace Abla ta d’aga hannunta itama ta wanka masa mari gabaki d’aya Wajan tsit yayi Sabida mamakin ta , be gama shiga mamakin marin da tayi masa ba ta ‘kar d’aga hannu ta tsinka masa Mari saida ta yi masa maruka uku kafun ta kallesa rai a’bace tayi wucewarta , Eshaal ma da Sauri ta bi bayan ta suka koma class , ga mugun mamakin da ta bar kowa da shi ganin ta ta’bo me gayyan BAD BOYS, suna komawa class sauran teachers din sune suka shish shigo , yan class din lokaci zuwa lokaci suna kallan Abla hatta baby da take sakin wani murmushin mugunta. Lokacin short break nayi ita da Eshaal basu fita ba , sbida karatun da ta fara koya mata . ‘Karfe 1:45pm aka tashesu gabaki d’aya , tare suka fito da Eshaal ta na fitowa ta hango Little sanye da face mask shima , sallama tayi wa Eshall ta nufi wajan sa Sabida gabaki d’aya motocin suna waje ya hana su shigo sai mota d’aya , yana ganin ta ya sakar mata murmushi � weldone Lil da alama kin gaji sosia � sosai ma kuwa � cewar Abla dariya Little yayi mata � with time zaki saba let’s go� da haka suka shiga cikin mota saida da suka hau babban titi sannan motocinsu suka shiga Gana da bayansu har suka ‘karasa cikin gida , tana shiga d’aki ta wuce tayi sallah sannan tayi wanka dan ta huta, 2:15pm little ya kira ta cin abinci tana gama ci ta koma d’aki ta kwanta sai around 3 ta farka da Sauri ta fito daga cikin d’akin dan gabaki d’aya ta manta da kaiwa simba Abinci, shaf shaf ta kai masa ta dawo falourn lokacin su little suna falour , itama a falourn ta zauna suka ci gaba da irarsu gwanin burgewa har ta d’auko assignment d’in tayi suma suna mata bayanın wanda akai bata da ta note d’in Eshaal.
Chapter 107 · 0% Book details