Sashe 46
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
yadda muscle dinsa suka fito sosai sai ya razana ka ga kirjinsa shima d’an dashi dan dukda jigar dake jikinsa zaka ga alamar six packs dinsa ya fito sosai Sabida yadda yake motsa jiki, muscle din hannunsa kamar zasu fasa hannun rigar su fito dan duk mutumin da ya rike bazaiji da dadi ba . Door d’in cikin d’akin yashiga yafi tsawan 1 hour a ciki , tun kafun ya fito wani irin daddad’an ’kamshi turaransa ya cika ko ina cikin ‘kan’kanin lokaci, sosai kamshin turaran Boadicea The victorious carbon sapphire ya cika ko ina na d’akin musamman yadda yake fitar da wani irin cool sanyi me tsayawa a rai, a hankali farar ‘kafarsa dake cikin takalmin Yeezy fitowa sosai cikin takalmin musamman yadda takalmin ya kasance black colour , hakan ya bawa farin fatar kafarsa fitowa sosai cikin takalmin, hatta nails din kafarsa abun kallo no gwanin burgewa , jikinsa sanye yake cikin Brooklinen ba’ka’ke masu laushin gaske , hakan ya ‘kara bawa kakkarfar jikinsa fitowa, fuskarsa a had’e take yanxun ma sai gyaran gaishinsa da ya gyara bakamar d’azu ba , yanxu gabaki d’ay doğan gashinsa yayi packing d’insa hakan ya bawa gashin damar sakko wa har wajan kafadunsa, yadda ba’kin kayansa suka fito sosai haka siririyar sal’kar diamond d’in wuyansa fitowa sai faman ‘kyalli take d’auka , haka wasu abun hannu da suke hannusa , black and white suma sai faman shining suke , da ‘karamin d’anna yatsansa ya saka wajan giransa da take a yanke ya d’an sosa wajan tare da taunar rep lips dinsa kad’ai, a hankali kamar baya san taka ‘kasa ya fara tunkarar wajan balchony d’in dakin da yake futar da wani irin sayyi daga wajan zaka Iya ganin yadda sojoji suke faman zagaye a cikin gidan ga su Bruno da aka saki sai faman bud’e bakinsu suke , ya dad’e a tsaye a wajan kafun ya mayar da idanuwansa kan stars , ya jima sosai a tsaye yana bin ko mai da idanuwa ba wai gajiya ce beyi ba , be saba kwanciya da daddare bane sai bayan sallar asuba shiyasa a ko da Yaushe idanuwansa biyu yana kallan komai da sanin duk abunda ke faruwa , sai wajan karfe 4am ya bar wajan tare da fitowa daga part d’in gabaki d’aya , yaga lokacin da bobo ya fito har ya koma alamar zai kwanta kenan, direct kasa ya nufa cikin d’akin uncle , already bobo yayi masa duk abunda ya kamata shiyasa ko light be kunna ba yabar d’akin , still saida ya sake shiga d’akin su little ya kara duba lapiyarsu kafun ya nufi part d’in bobo, gabaki d’aya light din aka she sai dum light da suke a kunne da alama shima ya kwanta, a hankali ya bud’e door d’in d’akin sai ya tarar da light din d’akin a kunne ga bobo kwance a kan gado, har karshen gadon ya nufa ganin kamar bacci ne ya soma d’aukar bobo batare da sanin saba , hannu d’aya big boss yasa jai gyara masa kwanciyarsa, azabure bobo ya d’aura masa Binduga aka cikin zafin nama big boss ya juyar da bindugar takıma saitin bobo, da wani d’an iskan kallo yabi bobo dashi yana matsawa gefe , zai juya yaji saukar muryar bobo � ya kamata ka huta kafun yan biyunka su tashi da mamakin dawowarka musamman that Jerry of yours�, saida ya kallesa sosai kafun ya iya bude bakinsa � zaka iya siyar dashi mana , since ka gaji da ganinsa�, ga baki d’aya maganarsu cikin turanci suke dan ko da wasa basufiya yin Hausa ba sai ta kama idan big boss bayana, � in ka yadda shafshaf ai bazaiyi tsadaba�, red lips dinsa big boss ya d’an ta’be kad’an yana juyawa sai da yazo Daidai light din bobo kafun a hankali ya furta � Night� yana kashe light din. Shima part d’insa ya koma amaimakon ya kwanta ya huta sai ma zama da yayi kan wata sofa, wata azababbiyar phone d’insa da duk duniya babu me irin ta ya d’akko jikinta har tanbarin zakine d’an mitsitsi a wjan , ba ‘karamin billions ya kashe akan wayar ba sabida da kansa ya bada idea din yadda za’ayi masa ita, sosai Kenta ya wuce musali, ‘karin ban sha’awa bayan ninkata uku da akeyi har Çan za tsarinta ake ta yadda kome yake cikin wayar zai iya ganin sa gaba da baya komai na cikin wayar ana gani, ko kuma aka rage mata tsahonta, iya had’uwa wayar ta had’u, yadda yake kallan wayar hakan ya bawa green eyes din idanuwansa fitowa sosai ga red lips dinsa da ya d’an ciza a hankali ,sosai lokaci zuwa lokaci yake shafa girarsa guda d’aya da alama habit dinsa ne wannan. Sai daf da kiran sallahr asuba ya ajje wayar tare da nufar ‘kofar d’azu, bai jima sosai ba kamar d’azu , kamshin turaransa har ya kama ko ina sabida bala’in dad’insa, ba shigar d’azuce a jikin saba yanxu sanye yake cikin white d’in riga da ta d’ame damtsen hannunsa kamar zasu fasashi su fito waje , sai farin dogon Wanda sa shima fari kirar kamfanin Armani, sosai farin fatarsa ta fito , hannunsa d’aya ya saka Wajan girarsa ya d’an sosa kafun ya sauke hannunsa, fuskarnan kamar hadari babu fara’a Sam a tattare dashi ko kad’an , Daidai wjn shan iska d’akin ya tsaya har yanxu sojojin suma suna nan a tsaye suna gadon gıdan, har aka fara kiraye kirayen kiran sallah . **** yau hakanan prince shine ya fara tashi tun kafun yaya bobo ya tashesu, saida ya tabbata yayi wanka sannan ya Tashi little shima , yau be ‘bata lokaci ba ya mike shima ya shiga Wanda duk iskancinsu basa so jam’i ya wuce su, shiyasa yau da wuri suka shirya , Sabida sanyin asuba kaya me kauri sosai little ya saka sabida sanyin da yake ji, su fito daniyar tashin bobo da uncle suka tarar da bobo suma sun fito shida uncle , with a suprise bobo ya furta � addua akai muku kuka tashi yau dawuri �, dariya little ya saki yana nuna masa ya prince � yaya bobo , shine fa ya fara tashi yau dawuri �, da mamaki uncle da bobo suka kalli prince , shi kuma hararan little ya ke yi � addua kayi ka Tashi da wuri?� Cewar bobo , kamar zaiyi kuka ya furta � please yaya bobo ka bari� yanxu ma dariya little ya kara saki yana sakar masa gwalo � lokacina tafiya fa� cewar uncle , jinjina masa kai bobo yayi � yes uncle ! But ku ‘kara 5 minutes tukunna �, lokacin sallar za’a karawa lokaci?� Cewar uncle yana kallansa da mamaki, bobo murmushi kawai ya saki ba tare da ya ce komai ba , elevator din da aka bude ne gabaki d’aya uncle , prince , little Suka mayar da kansu waje cike da shakkar abunda zasu gani, banda bobo da ko juyowa beyi ba sabida sanin ko wanene, cikin ta kunsa ya fito daga elevator fuskarsa kwata kwata ba annuri, prince be san lokacin da bakinsa ya fara furta � Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun� , Sabida yadda zuciyar sa ta buga bummmm yasan tabbas yanxu dole ya shiga taitayinsa ,kafun big boss ya canza masa kamanni da Sauri ya toshe bakinsa , yana zare ido , uncle ma da shock da mamakin lokacin da ya dawo ya hana sa motsawa, sosai jikin little ya fara rawa yana ‘ko’karin magana amma ya kasa sabida tsananin murna da yake ciki, da’kyar bakinsa ya iya furta � yaya big boss dina ?� Sai kuma ya kalli yaya bobo, ganin ya jinjina masa kai yasa da Sauri ya ‘karasa wajan big boss da yake tunkaro inda suke ,be tsaya ‘bata lokaci ba yayi hugging d’insa ,cikin kuka little ya furta � nayi missing dinka sosai, plx kadunga tafiya dani�,sai kuma ya soma kuka kamar wani ‘karamin yaro.