← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 146

Sashe 57

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

NEW YORK Karfe 11:00 pm na dare gabaki d’aya sojojin da suke duty suna yin aikinsu ko wannansu da shigar sojoji a jikinsa , gabaki d’aya gidan zagaye yake da katin katin sojoji masu Jini a jika , kowa ka kalla fuskarsa zaka ga babu murmushi ko annashuwa akan fuskarsa sabida yadda fuskar kowa take a had’e , first gate da aka bude ne ya karasa gabaki d’aya sojojin shiga taitayinsu, har aka bude gate na biyu zuwa babban gate din gidan , lokaci d’aya motocin bobo suka shigo gidan wajan karfe 11:20pm, tsadajjan agogon hannun sa ya kalla ganin yadda lokaci ya ja , babu Wanda ya fad’o masa arai kamar little yasan yanxu haka ya damu musamman rashin dawowar big boss duk da ba saban abu bane, iskar bakinsa ya fitar kad’an lokacin da Robert ya bude masa kofa, be bata lokaci ba kai tsaye ya nufi cikin gida yau ko tsayawa wajan su Bruno beyi ba , yana shiga kamar yadda yayi tsammani suna zaune akan kujera little har yayi bacci a zaune ga prince shima da yake gyangyadin amma ko wannansu ya ki zuwa ya kwanta , shima uncle be shiga daki ba yana zaune hannunsa dauke da jaridar da yake karantawa , kallan little da prince bobo yayi kafun ya girgiza kansa, � uncle� cewar bobo , murmushi uncle ya sakar masa � thank god ka dawo yanxu , look at them gabaki d’aya sun ki zuwa su kwanta , especially little da yake jiran dawowar yayansa �, shima murmushi bobo ya saki � uncle kai ma kasani rigimar little sai big boss ai, dare yayi yanxu be kamata suna bacci akan chairs ba� yana kai karshen maganarsa ya sabi prince dashima ya soma bacci kamar bayajin nauyinsa haka ya nufi part Dinsu dashi, sai da ya kaishi daki da kansa sannan ya tashesa ya canza kayansa zuwa na bacci sannan ya gyara masa blanket dinsa sabida yadda d’akinsu ya dauki sanyin Ac. Down stairs ya dawo har lokacin little na bacci shima d’aukarsa bobo yayi kamar wani karamin yaro ya kaishi d’aki , be tashe saba sabida already shi ya zansa kayansa , shima gyara masa kwanciya bobo yayi yana shafa lallausan bakın gashin kan little , tsawan 30 seconds yana kallan face dinsa kafun ya saki murmushi akan fuskarsa yana kashe musu light zuwa dum . Uncle ma ya nufi part d’insa shiyasa bobo yana fitowa kai tsaye part din sa ya nufa yayi wanka ,cikin kayan baccin Hanes yayi dressing dark blue , gyaran gashin kansa yayi gyarasa duk da kasancewar dare ne , Daidai bakin window din dakin ya tsaya yana jin yadda daddadar ni’imar Allah yake kadawa , sosai iskar tayi masa dad’i shiyasa ya tsaya a wajan. Durar motar da yajine yasa ya mayar da kallansa zuwa gate , kamar yadda yayi hasashe motocin big boss ne suka shigo cikin gidan a jere Daidai building Dinsu motocin sukai parking shiyasa bega fitowar sa har ya shige cikin gidan , watches din dakin ya kalla already yanxu past 12 yasan kuma big boss beci komai ba shiysa ya saka half sleeper dinsa ya bar dakin sa. Big boss kuwa yana shigowa ciki ko dago da eyes dinsa beyi ba balantana yasan da mutane a cikin falourn ko babu, yadda falourn yayi shirune yasashi lumshe kyawawan eyes dinsa , kai tsaye be zauna a falourn ba ya wuce part din sa directly . Yadda yaga ko ina a gyarane ya bashi tabbacin su little sun shigo d’akin . Hakan ne kuwa ya kasan ce bayan wata plasma da big boss ya kunna take a wajan videon su little ya bayyana lokacin da suke gyara masa dakin amma idan ka kalli fuskar little zakaga gabaki d’aya babu fara’a ko walwala akan face dinsa , lumshe ido big boss yayi tare da ta’ba lallausan gashin kansa da ya tufke , phone din hannunsa Kawai ya ajje kan center kafin ya shiga wata kofa dake cikin dakin. Almost 30 minutes big boss yana ciki be fito ba sai da aka kara 5 minutes kafun a turo kofar , daddadan kamshin turaransa ya Kara cika dadin tun kafun ya Fito, a hankali yake taka kafarsa me sanye da farin takalmin web slides , yadda takalmin yake fari sai ya fito da dogayen yan yatsun kafarsa masu shegen kyau, sanye yake cikin kayan bancin flannel dark ash , sosai kayan sukai masa kyau , kyakkyawar sumar kansa a wannan karan ta zubo masa har bayansa sabida yadda ya sake ta , kyawun fuskarsa sosai ya Kara fitowa kamar kullum kyawunsa kara kyau yake , amma gabaki d’aya face dinsa ba fara’a ko sakin fuska , a d’aure take tamau ,hakan kuma be sa kyawun fuskarsa guduwa ba sai ma kara wani sahir taccen kyau da yayi , a hankali yake motsa red lips dinsa kwanin burgewa ga eyes dinsa shima da duk lokacin da yayi motsi dasu sai dogayen eyes lashes din idan sa motsawa , yadda fuskarsa take a hade hakan be hana kyawun tsagar gidansa guduwa ga diamon bracelet dinsa guda biyu da haryanxu suke hannunsa , hatta sarkar diamond dinsa dake wuyansa sai faman kyalli take . Phone dinsa kawai ya dauka ya bar dakin Daidai floor 2 akwai Wani waje da ya’ke d’auke da wasu fararan kujeru nashan iska , yadda iska take kada wajan shiyafi komai burgewa , daga inda mutum yake yana iya hango duk abunda ke faruwa a cikin gidan sosai , idan bakasan glass din ya kare maka iska sosai yaka iya danna bottun wajan ya bud’e , akan d’an table din ya ajje phone dinsa , hannunsa gabaki d’aya a cikin aljihu yana kallan yadda weather din Garin yake ga stars da suka fito sosai shiyafi komai kawata wajan , � Assalamu alaikum� cewar bobo yana karasowa Inda big boss yake , a hankali ya motsa lips dinsa da ko shi bobo bai ji muryar saba amma sanin cewa ya amsa din ne yasa bece masa komai ba � can I ?� Cewar bobo yana kara tanbayarsa bayan medium tray din da ya ajje saman center , bansa big boss yayi masa tun bayan amsa sallamar da yayi be kara motsawa daga inda yake ba , kananan cups din da ke cikin tray bobo ya dauka tare da zuba coffee din da ya hada da kansa , cikin cups biyu , inda big boss yake a tsaye ya nufa tare da mika masa cup din , kamar bazai karba ba dan ko kallan inda bobo yake be ba sai da ya dauki 30 seconds sannan ya saka hannunsa d’aya ya dauka tare da lumshe masa idanuwansa. Suna tsaye a wajan babu Wanda yayi magana a cikin su musamman big boss da yake shipping coffee dinsa a hankali kamar ya manta da wanzuwar bobo a Wajan, � His excellency gobe zai shigo cikin New York with his family and nasan suna bukatar magana da kai akan yarancan�, cewar bobo yana kallan big boss , red lips dinsa big boss ya tabe kadan batare da yace komai ba tsawan good 5 minutes , bobo har ya cire ran zai basa amsa sai kuma yaji saukar muryarsa � who are they ?�, cewar big boss , tsayawa kallansa bobo yayi wai who are they shi be ma sansuba, � don’t start it please � cewar bobo, sexy eyes dinsa big boss ya dago yana bin fuskar bobo da kallo na yen seconds cikin izza da ta zamar masa jiki ya furta � daka gobe bana bukatar jin magana akansu,”dan maganar nan da yayi sai da ya tsaya yan kusan 1 minutes kafun ya furta � idan na kara jin maganar wannan case din , huh zan dawo da case din hannu na�, yana kai karshen zancansa ya bar Wajan suka kan chair din Wajan , cikin dan zaro ido bobo ya kallesa yasan idan har ya kar’bi case din sai yayi wa yaran mugun illa da bazasu kara mo ruwa ba , tunda ya furta zuwa gobe ai musu hukunci toh tabbas zuwa goben za’ayi musu, yasan wanene big boss farin sani , wani lokaci Dan rigima ne shi sosai , shima kan chair din ya samu ya zauna kafun ya fuskanci big boss sosai � nasan Nicholas yana wajan ka ?� , dan tsaki big boss yaja yana dauke kansa zuwa kan wayarsa , doguwar maganar nan da yayi har ya soma jin kansa na dan sara masa , wasu dan danne dannensa yayi cikin waya kafun ya jefa wa bobo wayar da yayi saurin cafkewa, da Sauri kuma ya dago da eyes dinsa yana big boss da kallo kafun ya mayar cikin wayar , ba kowa bane face Nicholas, Dylan sai logan a sakale gabaki d’aya an ratayesu kowanne fuskarsa a kunbure , gabaki d’ayansu ko wannansu a tattale musu kafa daga su sai gajeran wanduna a jikinsu sai kuka suke suna bada hakuri, a hankali big boss ya furta “Do you think zaka fitar da wasu daga cikin gidan nan sabida karna gansu? Just one word ko wannansu za’a yanke abunda yake iskanci dashi�, yadda bobo ya gansu ba karamin dariya suka bashi ba kamar wayanda ake shirin yiwa kaciya ko wannansu ya fice daga cikin hanya cinsa , abu d’aya zai iya musu zuwa gobe a hukuntasu idan ba haka ba yadda aka tattale musu kafarnan ba makawa big boss nacewa go on zasu yayyankewa yan iska gaba , ba VC ba ko president ba zai tanka masa ba ko ya tanbayesa why? Dan duk Wanda yasan big boss yasan zafin ransa, samun saukin mutum yabi tsarinsa. � yah nasan zaka gano inda suke but yayi wuri sabida baka dade da dawowa ba� kallansa big boss yayi for seconds ya dauke kansa tare da saka slice pine apple a bakinsa , yadda yake taunawa kamar Wanda aka saka dole dan a hankali yake taunarsa kamar bazai cinye ba , be karabi ta kan bobo ba sai kallan yadda weather ta karayin duhu yayi, maida kallansa yayi kan watches din hannunsa yaga har 1 ta wuce � ka kunna musu heater Sabida jikinsu�, cewar big boss yana mikewa tsaye , shima bobo mikewa tsayan yayi yabi bayan
Chapter 57 · 0% Book details