← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 146

Sashe 43

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

repeat that mistake, it’s called a mistake , next time kuka ‘kara yin wannan mistake din ni dakune , kuje ku canza �, da Sauri kuwa suka amsa masa suka koma , ko 5 minutes basu ba suka sakko da wasu drinks masu tsadan gaske , soldiers din falon ne suka amsa da Sauri suna barin falon Sabida lokacin har sun kammala aikin nasu � kiyaye kiraye kiran sallah magrib ne ya hana prince tanbayar da yake san yiwa bobo, babu Wanda ya ‘bata lokacin ya koma ya kimtsa kafun su tafi masallaci, hatta uncle yayi mamaki ganin komai a tsare rinkin baninkin yadda yake da , basu gama mamaki ba sai da suka fito waje , tsarin komai na Wajan sai da aka canza , duk da kullum a tsaftace yake wajan babu datti amma yanxu kana kallan tsakar Wajan zaka ga har wani iska iskan dadi take bayarwa , flowers gabaki d’aya an ‘kara gyara su, motocin wajan sai faman kyalli suke d’auka , basu wani mamaki sosai ba lokacin da suka shiga masallacin suka ga ancanza komai na ciki, sabida wanda tsarin gidan ne time to time ana canza komai amma na yau na musamman ne , babu Wanda yace komai har sukai sallahrsu both magrib and isha, suna komawa gida kuma dinner d’insu sukai kowa bakinsa fall tanbaya amma be basu damar hakan ba ya wuce part d’insa. Suma duk basu zauna ba a falon kowa ya nufi d’akinsa daman little me saka hiran amma yau kasa yi yayi Sabida zuciyarsa da take masa zafi Amma ya ki fad’awa ko sannan ya hanasu fahimta sabida yadda fuskarsa take d’auke da murmushin sa, ga tsokanan uncle da prince da yake duk dan karsu gane su tayar da hankalinsu. Yana komawa d’aki magungunansa ya d’auka yasha, lokacin ya bar prince a ‘kasa , ko minti biyar be yi ba , bacci me nauyin gaske ya d’aukesa sabida harda maganin bacci a cikin magungunan sabida zuciyar sa ta huta sosai, prince yana shigowa d’akin ya tarar da little har yayi bacci batare da ya canza kayan jikinsa ba , da kansa ya cire masa riga da wando jikinsa ya bar masa wani dogon wandansa da zai kai rabin kwiwarsa sannan ya lullu’besa da duvet me kauri yana rage sanyin Acn d’akin, shaf shaf yayi wanka ya saka kayan baccin sha shima Dan a gajiye yake , shiyasa ya ka she light d’in shima ya kwanta. Yau gabaki d’aya tunda bobo ya nufi part d’insa bai fito ba sannan bezo ya duba su little ba kamar yadda ya saba dubasu . 1:00am na dare lokacin da mafi aka sari mutane ke samun daman hutawa , a Daidai lokacin bobo ya fito daga part d’insa sanye da kakin sojoji , hular sa a gefen hannunsa na hagu, shigarsa ba kad’an ba tayi masa kyau duk da kasancewar dare yayi, d’akin su little ya nufa , ya duba lafiyarsu, tun kafun ya fito daga d’akin ya fara jin ‘karar helicopters na tashi, murmushi kawai ya saki yana barin d’akin, kai tsaye fitowa yayi daga part din gabaki d’aya , wasu irin dandazan sojojine a wajan ko wannansu cikin kakin sojoji side by side sunja layi sosai kowa da gun d’insa a hannu, ta sama kuma helicopters ne kusan guda biyar suke shawagi daga saman gidan . Suna ganin bobo kowannansu ya ‘kara ‘kamewa tare da yi masa salute cikin girma, babu Wanda ya amsawa sai tsayawa da yayi a tsakiyarsu yana fuskantar hanyar da zata sada ka da main gate , kusan mintuna 30 suna tsaye a Wajan babu Wanda yayi koda kwakkwaran motsi, lokacin da Suka ji bud’ewar gate d’in farko gabaki d’aya suka ‘kara shiga taitayinsu, hularsa bobo ya d’auka shima , ana bud’e gate na biyu shima ya ‘kame lokaci d’aya , gate din main door din gidan aka bude , wasu ba’ka’ken bike ne suka fara shigowa gidan a jere side by side guda biyar ko wannansu da shigar kakin soja tare da abubuwan jikin bike a jikinsu, tunda bike d’innan suka tunkaro cikin gidan ko wana soldier ya ‘kameta tare da sarawa cikin girmamawa, duk Wanda kaga fuskokinsu zakaga gabaki d’aya kawunansu a ‘kasa yake hannunsu kuma sun d’aga alamar sarawa ,lokacin da bike dinnan suka nufo Inda bobo yake gabaki d’ayansu da hannu d’aya suka rike bike din d’aya kuma suka sara masa shima , bayan su wasu manyan ba’ka’ken Hyundai palisade cars ne suka shigo ba’ka’ke kirin dasu , gabaki d’ayansu kuma tinted glasses ne dasu, saida guda bakwai suka shigo irin ta kafun bobo cikin wani irin salo ya matsa ya juya yadda cars din zasu shigo, bike din a jere suka tsaya lokacin da combo cars d’in nan suka shigo, daga bayansu wata irin zafaffiyar farar Mercedes Benz GT63s ta shigo gidan babu Wanda ya ‘kara ‘ko’karin motsi sai kara sarawa da sukai a jere cikin layi da tsari, daga kallo d’aya zaka san motar ba ‘karamar bota bace da a’kalla kudin ta zaikai 2.7 crore, sai faman d’aukan kyalli take babu alamar d’igon’kura a tattare da su, tana shigowa sauran motocin da Suka shigo sukai gefe ita kuma ta shiga tsakiya , daga bayantama wasu combo Hyundai palisade ne Suka tare mata baya . Wajan shiru ya d’auka kamar babu mutum me rai a wajan , kowa ka kalla kuma zakaga kansa a ‘kasa Alamar girmamawa hatta bobo yau sai da ya ‘kame irin ‘kamewar kwararran soja da yaga uban gidan sa , gabaki d’aya combo cars d’in da suka shigo fitowa sukai cikin motocinsu, ko wannansu sanye da black suit, da black guns a hannunsu, babu d’igon murmushi ko fara’a a tattare dasu, hatta farar motar Wanda ya kasance driver shima ya fito daga cikin motar , fuskarsa babu ko d’igon fara’a da walwala, babu Wanda fuskarsa take a sake , kwakkwaran motsi kawai suke jira su harbe mutum, cikin girmamawa d’aya daga cikinsu ya bud’e ‘kofar bayan cikin Farar motar, a wannan karan har bobo sai da ya sara lokacin da aka bud’e motar, ga wani irin kamshi me dad’i da yake fitowa daga cikin motar , tsawan mintuna 10 suna tsaye a haka babu Wanda ya motsa kuma daga position d’insa , a mintuna 15 da bud’e kofar wani kyakkyawar farin hannu ya d’an sako hannunsa fari tas dashi me had’a da farar kumba da Suka sha gyara sosai kamar ba farce ba diamond watched d’in hannunsa sai faman kyalkyali yake na ban Mamaki da ya ‘karawa dogon hannusa kyau, a hankali kuma ya zuro da farar ‘kafarsa me sanye da ba’kin horsebit loafer ( wani takalmi da za a iya kiransa da half shoe )da a kalla zai kai $890 , yadda takalmin yake d’aukar ido haka fatar kafarsa take d’auka ido dukda tana cikin takalmi kuwa, dogon farin wandansa da be kai har kasa wajan takalmin saba ya fito kirar kanfanin Armani kana kallansa zakaga alamar ba ‘karamin laushine dashi ba , a bazata ya Fito da gabaki d’aya jikinsa da ya ‘kara saka gabaki d’aya sojojin shan Jinin jikinsu.
Chapter 43 · 0% Book details