Sashe 30
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
****** Abla tana shiga d’akin ta tarar da arwa kwance tana kuka , a gefenta abla ta zauna, itama Arwa tana ganin abla ta Tashi zaune , cikin kuka ta soma magana � Abla na gaji da wannan kuncin rayuwar da muke ciki, mutane kullum burunsu su lalata marasa gata , Menene aibun mu dan muntashi cikin maraici? Ko maraicin da muke ciki ne yasa kowa burinsa yayi lalata da mu? Dabadan kinzo da wuri ba Abla da tuni sun lalatamun martabata, kece kadai kike sona , ban sani ba kuma bansan lokacin da ilham take cikinsuba abun ya d’aure mun lokacin da na gansu tare ga Aneesa da husna suma sun lalata musu rayuwa, ji nake Abla dama wani mummunan abu zai sameni na mutu ko zan huta da wannan takaicin rayuwar�. Saurin toshe mata baki abla tayi � inda rai ya ‘baci hankali ai be gujewa, ko Menene ya samemu jarabawace daga Allah, yana sane damu sannan yasan halin da muke ciki, wani jirkirin Alkairi, kindunga kyautata Alkairi cikin zuciyar ki�, duk yadda ran abla yake a ‘bace Hakan be hana tayiwa Arwa lallausan lafazi me kwantar da hankali ba . “Abla yunwa nake ji, ina tunanin bara zan fara ko zamu samu abinci dan bazan kara cin komai na zunubin suba . Inda ta ajje kudin ta ta shafa taji suna nan, � zo mufita � cewar abla tana ri’ke hannun arwa, a duniya dari biyar d’in da aka bata sadaka ce kawai tayi mata ragowa gashi tace duk sati zata dunga biyan uwar karuwai kud’in kwananta, ‘kosai ta siyowa Arwa na hamsin, ganin kudin na yin ‘kasa yasa ta hakura daci tabarwa arwa , ita kuma ta Samu gyad’ar ashirin taci , suna gama ci gidan ruwan da Abla ta ta’ba zuwa sukaje amma sosai akwai layi saida suka bari aka gama zubawa manya mota ruwan kafun azo kansu , yau ma talatin ta bayar aka bata guda 9, haka suka d’auka suka fara yawo Dashi cikin traffic ga ranar da ake me zafi ci amma haka suka shiga cikin traffic ko za a samu me shiyan ruwa , sun dad’e suna yawa daga traffic zuwa traffic kafin a siye musu ruwan , cike da farinciki suka ‘kara komawa a wannan karan na 40 aka ‘kara musu guda biyar akai , su biyu sai yawo suke cikin zafin ranar, suna cikin tafiya ko d’ad’d’an silifas din Abla da yayi mata kad’an ya tsinke, cikin da bara ta samo leda ta kulle takalmin ta mayar ‘kafarta tunda bata da kudin siyan wani , ko da tanadashi ma bazata siya ba sabida kudin da zata bawa uwar karuwai. Har wajan karfe biyu suna abu d’aya saidai su Samu waje suyi sallah kafun su cigaba , sosai rana ta dakesu amma duk da haka sun kwammace su zauna a cikinta akan su koma gidan karuwai.sai da sukai la’asar suna siyar da ruwa ‘kafafuwansu gabaki d’aya ya sage sabida gajiya , duk da bawani kudi suka samu ba Amma iya ribar da suka zamu cikin ruwan da suka siyar sosai sukai farin ciki da haka , lokacin da Abla ta bawa Arwa wani kaso a cikin kudin ‘kin kar’ba tayi , acewarta in sun samu abinci sai su siya dashi, yau ko daman zuwa makarantar allon Malam sule batayi ba, da zasu dawo gida zallan rogo suka siya na hamsin d’insu . Kamar yadda ta saba dawowa kullum Anfara tashin kid’a yau sai tayi sa’a basu kunna ba sabida itama ta dawo gida da wuri , babu Wanda yaga shigowarta ita da Arwa suka shige d’akinsu, suna shiga suka tarar da husna zaune kan katifa ga wata tanfatsetsiyar waya a hannunta tana dannawa , ga lemo da gasashshiyar kaza tana ci, da harara da Abla dashi itama Abla ko kallan inda take batayi ba ta zauna ita da Arwa akan kwalinsu suka faracin rogonsu, wata yar iskar dariya husna ta kwashe da ita � a haka mutum zai ‘kare a tsiyace ana nuna masa gabas yana runtse ido , in banda tsiya mata da maita me mutum zai ci a rogo �, wani banzan kallo Abla tabi husna Dashi da yasa ta rufe bakinta, cike da wulakanci husna zata d’ao gashshiyar kaza ta yaga sai ta furta � Gaza da dadi rangen rangengen �, babu Wanda ya kulata tsakanin Abla da Arwa , Aneesa ce ta Fito cikin toilet tana ganin Abla ta sakar mata murmushi � Abla har kun dawo �, tsayawa kallanta Abla tayi ganin yadda Wajan idanuwanta sukai baki baki gata ita kanta sai faman rangaji take kamar zata fad’i, wata sabuwar doguwar Riga ta saka mara nauyi ta haye katifarsu nan da nan bacci ya d’auketa me nauyin gaske , Ana kiran sallah kid’a na tashi me ‘karfin gaske da kashe dodan kunne , da ‘kyar Abla ta Samu tayi sallah sabida yadda kid’an ya karad’e ko ina , a matsayinta na ‘ya mace be kamata tana zama a waje ba cikin dare musamman yadda duniya ta lalace , shiyasa duk da ‘karan da yake tashi ta yi zamanta tunda babu yadda zatayi, wasu tsofaffin papers ta d’auko sai faman dubasu take d’aya bayan d’aya tana ‘kara karantasu, har lokacin Aneesa da ta kwanta bacci take kamar wata bawa , lokaci zuwa lokaci Abla takan d’ago ta kalleta ganin yadda take baccinta kamar mara rai ajiki . Tunda Husna ta fita tasan bazata dawo ba sai kuma wani ikon Allah sabida wankan da tasha, har lokacin kuma bata ‘karasa ilham a idanuwanta ba itama kuma bata damu da inda tashiga ba.
Lokacin da Arwa ta dawo d’akin hirarsu suka sha gwanin burgewa , 10:30 na dare lokacin da kid’an yafi tashi suka kwanta tunda sunyi sallar isha’insu, sai da abla ta kulle musu ‘kofa gagam kafun su kwanta , har lokacin Aneesa bacci take .
✨✨✨✨�
WASHINGTON D.C
1600 PENNSYLVANIA AVENUE, N.W.
THE WHITE HOUSE
PAY YOUR MONEY INTO 2681892316 , AISHA UMAR , ZENITH BANK SAI A TUROMUN SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee �
Littafin IBTISSAM is now 300 instead of 500 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
Littafin ibtissam ‘kir’kirarran labari ne , ban yadda wani ko wata ya juyamun book ta ko wana sigaba. Duk Wanda littafina yazo d’aya daga cikin wani sashe na rayuwar sa, to a rashi sani ne .
___💞💞And ( Remember)when your lord proclaimed,â€if you are grateful, I will surely increase you (in favor );but if you deny, indeed, my punishment is severe “â€?..💞💞___
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
Season __11
WASHINGTON D.C
1600 PENNSYLVANIA AVENUE, N.W.
THE WHITE HOUSE
Lokacin da Arwa ta dawo d’akin hirarsu suka sha gwanin burgewa , 10:30 na dare lokacin da kid’an yafi tashi suka kwanta tunda sunyi sallar isha’insu, sai da abla ta kulle musu ‘kofa gagam kafun su kwanta , har lokacin Aneesa bacci take .
✨✨✨✨�
WASHINGTON D.C
1600 PENNSYLVANIA AVENUE, N.W.
THE WHITE HOUSE
PAY YOUR MONEY INTO 2681892316 , AISHA UMAR , ZENITH BANK SAI A TUROMUN SHAIDAR BIYA TA WANNAN NUMBER 07041879581.
https://chat.whatsapp.com/DBN2FLDRV5XKMpvHpltmLt
IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)
Story & written
By
Mss Lee �
Littafin IBTISSAM is now 300 instead of 500 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.
Littafin ibtissam ‘kir’kirarran labari ne , ban yadda wani ko wata ya juyamun book ta ko wana sigaba. Duk Wanda littafina yazo d’aya daga cikin wani sashe na rayuwar sa, to a rashi sani ne .
___💞💞And ( Remember)when your lord proclaimed,â€if you are grateful, I will surely increase you (in favor );but if you deny, indeed, my punishment is severe “â€?..💞💞___
___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___
BOOK 1
Season __11
WASHINGTON D.C
1600 PENNSYLVANIA AVENUE, N.W.
THE WHITE HOUSE