Sashe 62
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Eshaal ce tsaye a wajan oven tana gasa cake din da take had’awa daga gefenta kuma AMMA ce a tsaye take temaka mata da wasu abubuwan ,musamman yadda take koya mata wasu da barin yin cake din kala kala mutum saiya d’auka wata kwararriyar me cake ce Sabida yadda take koya mata , itama Eshaal sosai tamaida hankalinta kan Amma dan yawanci ta sanadiyar Amma ta iya komai, hatta karatın Alkur’ani AMMA tana koyar da ita shiyasa ta saba da yinsa tun tana yar ‘karamarta. � AMMA ya kamata ki Hutu tun d’azu fa kike aikace aikace �, murmushi Amma dake tsaye tayi � karki damu ai babu wani gajiya , inaso naga yadda zaki gama ne ko akwai abunda kike bu’kata �, dan jiyowa Eshaal tayi ta kalleta � Amma karki damu babu abunda nake bu’kata , ko da ma ina bukatar abu ai ba sai na wahalar dake ba , kawai nidai ki samu ki huta d’an Allah kinji �, toh shiknn cewar AMMA, amma duk da hakan bata zauna ba , sai da Eshaal ta juye cup cake din cikin oven ta saka wani , kama hannun Amma tayi ta zaunar da ita kan dinning din cikin kitchen din , Amma Zata mike Eshaal tayi saurin dakatar da ita � Haba Amma kiyi zamanki karki damu kinji ? Bari na zuba miki cup cake din Mss Eshaal kimun testing nasan wannan karan Amma sai na fiki iyawa�, ta ‘karasa tare da zubawa Amma cake din cikin wani unique plate me kyau, ta ajje mata tare da d’auko mata d’aya daga cikin zoban da tayi d’azu � oya AMMA kiyi mun testing amma karkiyi Santi fa�, cewar Eshaal cikin zolaya “karki cika baki fa , dan nasan ba wani dadi zaiyi ba�, ta ‘karasa tana cin d’aya daga cikin cake din , kamar Wanda beyi dadi ba sai kuma ta d’an ya mutsa face dinta hakan kuma ba karamin kyau yayi mata ba , yadda Eshaal taga Amma ta ya mutsa fuska yasa jikin ta duk yin sanyi a tunaninta cake din ne beyi dadi ba , sai dataga Amma ta ‘kara gutsira tana d’aga wa Eshaal 3 fingers alamar yayi dadi dan ko magana ta kasa , � Amma yayi dadi ?� Cewar Eshaal tana ‘kara tanbayar Amma dan tabbatarwa � sosai ma� cewar Amma , ai Eshaal bata san lokacin da tayi hugging Amma ba tana dariya , � Kutmar uba ,lalle Eshaal baki da hankali , akan abin anfaninmu zaki sa mana kazamarnan har ta zauna akai ? Sannan taci abinci da plate dinmu?� A zuciye Eshaal ta juyo tana kallan Baby, itama AMMA mikewa tayi daga kan kujerar tana ajje cake din , � Menene haka ? Kin cika shiga sabgata me ya shafeki da duk abunda zanyi ? Taci d’in ni na bata , iskancinki ya isheni haka� kuyi hakuri dan Allah� cewar AMMA , � No AMMA bakiyi mana komai ba , iskancine Kawai irin nata , dan Allah kiyi hakuri mu cigaba da aikin mu �, ni kike cewa yar iska ?�, cewar baby , a zuciye Eshaal ta furta � Amfad’amikin kiyi abunda zakiyi �, hannu ta d’aga tare da nuna side din Amma � wannan Itace �.� Bata karasa ba Eshaal ta d’auke fuskarta da mari, � Duk iskancinki ki tsaya a kaina , naga kwana biyu kanki na rawa , kada ki kuskura ki kara saka AMMA cikin banzayen maganarki , sabida tafiye mun ku gabaki d’ayanku dan ita din mahaifiyata ce , karki manta kamar yadda kike yar gidan nan haka nake , nice babba bake ba , ina d’aga miki ‘kafane sabida ita, shashasha kawai , fitar mun a kitchen� ta daka Mata tsawa , ita kanta Baby batasan lokacin da ta fice daga cikin kitchen d’in va . Maida kallan Eshaal tayi kan AMMA , � AMMA dan Allah kiyi hakuri , zauna mu cigaba da cake din kinga ma yakusa ‘konewa� ta karasa maganarta tare da nufar wajan Oven din .
A cikin falour kuwa , waya Baby ta d’auka ta soma dialing number Momy amma gabaki d’aya calls din basa tafiya, ita kadai sai cizan yatsa take tana jijjiga kai ganin called din mom bayashiga ne yasa ta mayar da akalar wayar zuwa phone din dady , shima kamar had’in baki yana d’aga wa be jira tayi magana ba ya sanar da ita yana meeting, zata katseshi ya Rigata ta hanyar kashe wayar da yayi . Dogon tsaki kawai taja tare da barin falourn rai a’bace zuwa d’akin dan sosai Eshaal ta ‘bata mata rai � kamar ni zatace zata fad’awa magana ? , lalle wuyanki ya isa yanka amma zanyi maganinki� ita kadai take maganar ta cikin zuciyarta tana Tunanin irin hukuncin da zata saka mom tayi wa Eshaal.
✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨
A cikin falour kuwa , waya Baby ta d’auka ta soma dialing number Momy amma gabaki d’aya calls din basa tafiya, ita kadai sai cizan yatsa take tana jijjiga kai ganin called din mom bayashiga ne yasa ta mayar da akalar wayar zuwa phone din dady , shima kamar had’in baki yana d’aga wa be jira tayi magana ba ya sanar da ita yana meeting, zata katseshi ya Rigata ta hanyar kashe wayar da yayi . Dogon tsaki kawai taja tare da barin falourn rai a’bace zuwa d’akin dan sosai Eshaal ta ‘bata mata rai � kamar ni zatace zata fad’awa magana ? , lalle wuyanki ya isa yanka amma zanyi maganinki� ita kadai take maganar ta cikin zuciyarta tana Tunanin irin hukuncin da zata saka mom tayi wa Eshaal.
✨✨✨✨
✨✨✨✨✨✨