← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 146

Sashe 94

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda big boss ya shigo cikin falourn babu Wanda yayi wa magana har ya zauna akan kujerar da yake yawan zama , fuskarsa gabaki d’aya ba annuri a tattare dashi , cikin nutsuwa yake danna wayar hannunsa , � yaya sannu da zuwa”cewar prince , amaimakon ya amsa masa sai ya lumshe masa eyes d’insa kamar yadda ya saba , bobo da uncle kuwa face d’insa suke bi da kallo shiyasa ya ‘kara d’aure face d’insa .
Suna zaune har little ya d’auko wa big boss abinci ya jera masa kamar yadda suka saba , ga Abla dake facing d’in inda yake , gabaki d’aya sai taji ta ‘koshi bata jin yunwa dan ko kwakkwaran motsi ta kasa , har little ya gama serving din yaya big boss . � Lil ya kika dena din abincin ?� Cewar bobo bayan ya kalli big boss da ya ‘kara shan kunu, yasan Sabida big boss ne ta kasa cin abincin , muryarta na rawa ta furta � Na ‘koshi ne…� girgiza mata kai bobo yayi � No lil ai bakici sosai ba , ko kuma kawai ki tafi dashi d’aki � kamar jira take kuwa ta jinjina masa kai da Sauri tana d’aukan tray d’in, little zai dakatar da ita bobo ya hanasa . Big boss kuwa kamar be san me ke faruwa a falourn ba , hankali a kwance yake cin abincinsa , lokaci zuwa lokaci kuma yana danna wayar hannunsa. Cike da d’an zolaya bobo ya furta � yaya big boss mufa yadda kake d’aure mana face d’in nan yana bamu tsoro kaga ka saka sister d’in mu guduwa�, wani irin kallo big boss ya zubawa bobo da yasa ka babu shiri bobo ya saki dariya � maida wukar yaya bani na kar zoman bafa �, big boss be ce masa komai ba ya cigaba da cin abincinsa , saida ya gama tukunna ya mi’ke tsaye yana kallan black Rolex d’in hannunsa . Da Sauri bobo ya furta “Are you going out ?� Ba tare da ya kallesa ba big boss ya d’an yi knodding kansa , murya ciki ciki ya furta � yeah ! See you all� yana kai ‘karshen maganarsa yayi hanyar barin falourn , da d’an ‘karfi little ya furta � yaya please karka manta ! Love �.

Sai da prince ya ga fitar Big Boss kafin ya kalli little � me ne ne � d’an harararsa little yayi � Allah yaya prince kana san jin gulma � babu komai fa ! Lil nace asaka makaranta � kusan lokaci d’aya prince da uncle suka furta � ya amince ?� Kansa little ya girgiza akan Ah’ah , murmushi bobo kawai ya saki batare da yace komai ba , har ya juya sai kuma ya d’an tsaya � I think you get some visitors may be � cikin tsokana Uncle yace � kodai sirikai nane?� Lokaci d’aya bobo ya d’aure face d’insa , bai bi takan maganar uncle ba ya juya ya bar wajan.

Abla tana shiga cikin d’aki ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ‘kirjinta , kamar zatayi kuka ta furta “wallahi wannan zuciyar tawa matsoraciya ce , ko uwar karuwai da take kawo mun hari bana jin wannan bugun zuciyar ! Haba fisabilillah�, gabaki d’aya sai taji abinci ya fice mata arai har ta ‘koshi , a fili kamar me magana da wani kuma ta ta’be baki � Mutum kullum sai ‘kara kyau yake kamar wani aljani�.
Ledojin jiya ta janyo ta fara bubbud’e kayayyakin da aka siyo mata , ba’karamun kyau sukayi ba ita kad’ai sai faman dariya take . Gabaki d’aya kayan jera su tayi cikin wardrobe , ta kalmi da jaka ba gabaki d’aya kowa da inda ta saka su hatta kayan za’kin da Prince ya kwaso mata , lokaci d’aya sai d’akin ya canza ya zama na cikakkiyar budurwa me ki da gata .

✨✨✨✨�

2:50pm ta sakko daga d’akin ta gudun kar ta sake yin wani laifin , tasan idan bata Kai wa simba abinci ba , ita big boss zai mayar simba , ga tsoro da take ji, dad’in ta tana sakkowa taga little zaune akan kujera , � yanxu nake shirin kiranki Lil , ya kamata ki kaiwa simba Abinci kai ki sake wani laifin ko ?� Da Sauri Abla ta furta � Eh� suna tafiya suna hira dan yanxu ta rage tsoran sojojin sosai . Suna shan hanyar da zata sadasu da d’akin simba wasu manya manya motoci suka shigo cikin gidan kusan guda takwas, cikin Sauri wasu sojojin Suka kare wata mota , kafun lokaci d’aya su bud’e musu both side , His excellency ne ya fara fitowa daga cikin motar , sai Her excelling da ta fito itama cikin shigar ‘kananan ‘kaya , a gadarance ta furta � let’s go sweetheart� wata farar ‘kaface ta soma fitowa da ta cin red jan farce a ‘yan yatsun ‘karta , cikin iyayi ta fito daga cikin motar , ba kowa bace face Alice da taci wankan turawa hirar jikinta black colour ko cibiyarta bata rufe mata ba , sai red d’in wando da shima ko kwiwar ‘kafarta be kai ba , ga wani uban hill shoe da ta saka , sai Faman ya tsine face take , dukda kasancewar ta yar president ba ‘karamin tafiya da imaninta tsarin gidan yayi ba kasancewar wannan ne zuwanta na farko , ta ko ina kamar kiran president Jami’ai ne , Jami’an da suka ninka nasu a yawa da girma , lokaci d’aya wani murmushi ya su ‘buce mata � soon I will be the queen of this house ! Zanyi ruling kowa ! Wow�. Sweetly let’s go � cewar her excelling , cikin yanga Alice ta soma ta ku, so take kawai ta saka big boss cikin idanuwanta , tun accident din da ya faru har bobo ya tsinka mata mari bata sake ganin sa ba duk yadda taso hakan kuwa . Har ciki Robert yayi musu iso , lokacin uncle ya fito daga part d’insa bobo ba haka , hugging din bobo his excellency yayi � my son how are you � fine Kawai bobo yace masa , itama Alice ganin Dadynta na wajan ta mi’ke wai zatayi hugging d’insa , kallan da yayi mata ne yasa ta waske ta koma ta zauna sai faman zuba ido take taga ta inda Big boss zai ‘bullo .

A ‘bangaran Abla kuwa suna zuwa wajan d’akin tsoro ya kamata , dad’insu ma yau ba Victor bane dukda kusan halinsu d’aya amma Ana bud’e d’akin simba Abla ta je fa masa abinci kamar yadda suka shirya plan d’insu ita da little , suna tafiya suna dariya abunsu, a hanyar komawarsu gida sukaga manyan motocin da suka shigo , sau d’aya little ya kalli motocin ya san bana yayansa bane , suna tafiya suna hira abinsu gwanin burgewa , suna shiga cikin falourn sukai sutus Sabida mutanan da suka gani zazzaune a falourn, Lokaci d’aya Alice ta mi’ke tsaye rai a ‘bace � me wannan ‘kazamar take anan kuma ?”kallan tara saura Abla ta bita dashi lokacin da suke shigo cikin falourn , shima little cikin ido ya kalleta � she’s the sister of the family kinga ba ‘kazama bace �, dakatar Dashi bobo yayi � it’s okay little calm down !� Turo bakinsa little yayi kafun ya gaishe da su mr president duk da ya sansu amma kwata kwata face d’insa ba fara dan gabaki d’aya basuyi masa ba , itama Abla gaishe dasu tayi zata juya little yayi saurin furta � Lil ! Zo muje garden � toh kawai Abla tace zasu juya Alice tayi Saurin furta � sorry guys zan iya binku� little har Zaice mata ah’ah sai yaga bobo yayi knodding kansa , kamar yadda big boss yake magana a fusge shima yau haka little yayi kafin ya furta � why not � Abla lokaci d’aya kamar little ya rikid’e ya koma mata Big boss , suna tafiya yana janta a hira banda Alice da sukayi kamar basu san da zuwanta ba . Suna shiga cikin garden d’in Abla ta fara furta � wow ! Wajan nan yayi kyau sosai � murmushi little ya sakar mata � ko muje wajan pool? Zaifi � da Sauri ta furta yes , haka suka bi wani side duk a cikin garden d’in lokaci d’aya ya kawosu wani babban pool me shegen kyau da fad’in had’uwarsa ‘bata bakine . Wani shu’umin murmushi Alice tayi batare da tace musu komai ba , little har zai zauna a bakin pool d’in sai kuma ya dakata tare da furta � Lil ina zuwa � okay Abla tace masa lokacin da ya bar wajan yayi saura daga ita sai Alice , kallan ta Alice tayi daga sama har ‘kasa cikin wani irin kallan tsana ,� how dare you ? Waya baki izinin zama a cikin gidan nan ?� Kallan baki da hankali Abla ta bita dashi batare da ta tanka mata ba sai ma pool da ta zubawa ido ganin yadda yayi blue , cikin tsawa rai a ‘bace Alice ta furta � how dare you ! Ina miki magana kin shareni? I can easy killed you ! Stupid !� Yanxu banza Abla tayi mata hakan ya ‘kara ‘bata wa Alice rai da ‘karfi ta janyo rigar Abla � how dare you ?� Itama Abla rai a ‘bace tayi ‘ko’karin kwace rigar ta batare da ta tankawa Alice ba , ko kawa suka soma yi Abla tana ‘ko’karin kwace rigar ta Alice kuma tana ‘kara ri’keta, a zuciye Kawai ta jefa Abla cikin pool, gashi Abla bata iya ruwa ba , lokaci d’aya ta fara wutsul wutsul a cikin ruwan ta na mi’ko da hannunta, ga ruwa da ya’ke shigar mata hanci, sosai Abla ta soma ‘ko’karin fitowa Amma kamar ruwan janta yake , tsaki Alice taja ta juya tabar Abla tana wutsur wutsur gashi ko idanuwanta bata iya bud’e , lokaci d’aya nunfashinta ya soma sar tsewa sabida rashin nunfashi da bata sha’ka, tun tana ‘ko’karin cecan kanta har ta dena motsi da hannunta , gabaki d’aya jikinta ya soma nutsewa cikin ruwan.

PAID BOOK*
300 into 2681892316 Aisha umar, zenith bank . Sai a turo shaidar biya ta wannan number 07041879581.

https://chat.whatsapp.com/B5v9kh9BrGm6wjMuygdK1p
Chapter 94 · 0% Book details