Sashe 15
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tun da su Abla suka fita daga gidan karuwai gabaki d’aya barin unguwar sukai, sai da sukayi tafiya mai Nisan gaske kafin su zauna suna hutawa , ilham kamar zatayi kuka ta kalli Abla â€? yanxu Abla kinga abunda muka jawo wa kanmu yanxu me kwatar mu a wajan shegiyar matar nan sai Allahâ€?, kallanta Abla tayi kafin ta d’an ta’be bakinta ,cikin siririyar muryarta me dad’in gaske kamar sarewa ta furta “kome zatayi mana Allah na tare da mu ai , kuma ita bata isa tayi mana abunda Allah be nufa ba, kwanda ma ki kwantar da hankalinkiâ€hawayenta ilham ta share duk da har yanxu akwai tsoro a tattare da ita â€? Abla kinsan halin matar nan, bata da Imani musamman ke da ta fi nuna wa tsana , bansan Sharrin da Zinariyya zataje ta ‘kulla mana ba , shegiya kanta kamar duwawun d’an buriâ€?, dungure mata kai Abla tayi â€? kar ki wani dasu, ki tashi muyi abunda zamuyi kafin yamma tayi, kina an fara kiran sallar‘karfe d’aya , damun idar zan ‘karasa layin Formella , idan basu gama karatun suba , na saurara ko Allah zaisa na iya wasu abubuwan, Allah yasa Malam Sule yayi Tarihi yauâ€?, shiru ilham tayi kamar me tunani kafin tace â€? Amma Abla me zai hana yau muje kasuwar kubwa ,ko kayan kwanjone mu siyaâ€mi’kewa tsaye Abla tayi , tare da zubawa ilham manyan dara daran milky eyes d’inta, dukda tana cikin halin rayuwa amma babu abunda ya canza daga kyawunsu,daga cikin idanuwanta har wasu d’igon tauwadane guda biyu da suke ‘kara Haska kyawun kwayar idanuwanta da suke zara Zara kamar wacce ta saka kwalli a cikin idan, ‘kara ‘kiftasu tayi akan ilham take a Wajan dogan gashin idanunta suka soma sama da ‘kasa ba’ka’kye Wuluk kamar tasaka , cikin daddad’ar muryarta me kama da na sarewa ta cewa ilham “idan kika kashe su ranar da kike bu’katan kudin ya zakiyi kenan? Karki manta su kad’aine dake duk duniya yanxu, na d’auka zakice zakisi wani abu ki kwada siyarwa? Ni kam babu ruwana babu wani kubwa da zanje, kinga biyu ta kusa ki taso muje muji karatun malam sule , banaso tarihin Annabi ya wuceni yauâ€? Amma abla idan bamu je kasuwar ba Wana irin abu kikeso musiyar?â€? Soma tafiya Abla tayi ilham tabi bayanta da Sauri â€? Allah zai haska mana ai, Kema kuma kinsan akwai sana’a sosai da mutum zai iya farawa , Nidai yanxu damuwa ta, kar agama karatu banjiba, ga tarihin da nakeson ji, ki bari zan fad’a miki Wana irin kasuwanci zamuyi kinji?â€? Jinjina mata kai ilham tayi tare da kama hannunta suka soma tafiya , saida suka ‘karayin tafiya me Nisan gaske kafun suzo wata makarantar Almajira da ke cike da maza, can gefe dasu Ilham da Abla suka ra’be suna sauraran karatun Malam suke dayake ‘karawa almajiran, ganin lokacin sallah yayi ne suka samu wani guntun ruwa sukayi alwala da sallarsu, kafin su ci gaba da sauraran karatun. Karfe 3:00 daidai Malam sule ya dakata da karatun ya soma yi musu tarihin annabi yusuf, gabaki d’aya nutsuwa Abla tayi tana sauraran tarihin, ita kadai sai faman murmushi take , 4:00 ya dakata musu, d’an ‘karamin tsaki Abla taja tare da kama hannun ilham suka bar wajanâ€? wallahi Malam sule wani lokaci bashi da M, saida na nutsu ina jin tarihi zai katse mana â€?, dariya ilham ta saki daman tasan za a rina , duk lokacin da zasu zo jin karatun Malam sule a’karshe sai tayi complain musamman idan tarihi ake yi lokacin , Kiraye kirayen sallar la’asarne yasasu tsayawa daidai gefen wani masallaci, saida suka tabbatar sun shiga sallah kafun su samu suma suyi Alwala da ragowar ruwan butocin wajen, can gefe da masallaci su bi jam’i suma , ana idar da sallah muma suka tashi suka soma tafiya , wani dakali da Abla ta hango ta nufa, itama ilham zama tayi a gefenta, cikin nutsuwa suka soma karanto adduar safe da maraice, duk inda ilham tayi kuskure sai abla ta sake gyara mata , har suka gama sai lokacin ilham ta fara ri’ke cikinta â€? Abla wallahi yunwa nake ji,â€duk da itama Ablan yunwa take ji sai bata nuna hakan ba ita , cikin tsokana ta ce wa ilham â€? toh taho mu koma kurkukun muâ€?, tsallan data ga ilham tayi ne yasata ‘kyal’kyalewa da dariya da har dimple dinta na both side suka lo’ba, â€? wallahi Kema kinsa in muka koma zamu san sauran balalle ma musamu abinci ba, ga me awaracan dan Allah ko na d’ari musamu muciâ€?, ‘karar da cikin abla yayi ne yasa ilham ‘kara kallanta “kinga Kema yunwa kikeje, karkimun musu kawai ki taso muje muci awaranâ€?, batayi mata musu ba kuwa suka tsaya wajan me awara saida suka ci ta d’arinsu suka kora da ruwa kafin su fara tunanin komawa gida , wata bishiyar KARARA Abla ta hango da sauri ta nufeta ilham na binta abaya , saida suka ‘karaso wajan ilham ta zaro ido â€? Abla me zakiyi da karara kinsan ‘kai’kayine dashi fa sosai, dariya mugunta abla ta saki kafun ta samo wasu manyan ledoji guda uku, biyu ta saka a hannunta,d’ayar kuma ilham ta rike mata ,tsabar mugunta irin na abla wad’an da Suka bubbushe ta tsutstsunka, sai da ta tara masu yawa sannan ta dakasu da dutse , ilham gabaki d’aya ta tsorata batasan me abla zatayi dasu ba , saida ta tabbatar ya mata yanda take so kafun suka nufo hanyar gida lokacin magariba ta kusa, a farkon layin suka hango husna ita da wani a tsaye daga jikin bango sai wani mammanne mata yake, tana ganin su Abla ta d’auke kai,kamar Abla zatayi mata magana sai itama ta shareta, hannunta ilham ta kama â€? Abla ki ‘kyalesu, duk wanda yace baya bu’katarki a rayuwarsa Kema ki rabu dasu, kinyi iya kokarin ki akansu amma basa ganin haka â€?, d’an murmushi Abla ta sakar wa ilham kafun ta furta “insha Allahu â€? . Kid’an da Abla ta somajine yasa ta girgiza kai, haka suke tun farkon magariba suke sa kid’a har isha’i, a Wajan gidan kuwa kamar yadda tayi tsammani mata da maza ne kowa tare da ‘yan matansa, wasu kuma matane kawai, ko wannen su da ‘yar iskar shiga , suna shiga Sukatar da abun yafi worse ma dan gabaki d’aya daga wacce zaka ganta kwance jikin namiji sai wanda suke kiss da shafe shafe ba ko kunya, kauda kanta Abla tayi tana neman tsari daga sharrinsu, da Sauri ta kama hannun abla kada su Zinariyya su gansu, suka nufi store d’in da ya zama kamar d’akinsu, karo suka ci da Aneesa dake ‘ko’karin fitowa daga d’akin cikin wata doguwar Riga , mamaki ne ya kama su Abla dan basu ta’ba ganin ta da irin wannan kayan ba â€? Anee?â€? Cewar Abla , itama Aneesa murmushi ta sakar musu , cike da murna ta furta â€? tun d’azu nake tanbayar inda kuke akace ba’a san inda kuke ba , Aushe zan ganku dai kafun na fita â€?, kallan ban gane ba Abla ta bita dashi, fahimtar hakan Yasa Aneesa bud’e wata swag Jakarta itama da Alama sabuwa ce ta Fito da ma’kudan kudi tana nuna musu â€? A ina kika samo wannan kudin? Karkisa na fara zargin ko sata kika fara ?â€? Dariya Aneesa ta sakiâ€? haba Abla ki dunga mun kyakkyawan zato man, inda naje ne nasa mu wannan kudin kyauta , kinga tun jiya kaza da lemo nake sha sai abunda yayi mun yanxu na dena kwanan yunwa , zan dunga samun kudiâ€? atare suka had’a baki wajan furta kamar yaâ€?, bata damu ba itama ta soma musu bayaniâ€? kawai fa hotel zakuje, Wanda aka had’a ku dashi ya d’an shash shafaku,shikenan faâ€?, da mamaki Abla ta furta â€? kina nufin karuwanci?â€? Girgiza mata kai Aneesa tayi â€? ni ba karuwanci nayi ba , nace miki shash shafa ni yayi yana mun wasa da breast d’ina , ni kuma yace na sha masa…â€?, bata ‘karasa ba Abla tayi Saurin daka mata tsawa â€? ya isa haka Aneesa bana bukatar jin zancenki , Allah ya shiryeki, banga anfanin mu’a mala da me irin halinki ba â€?, daga bayan ta taji an furta â€? sai me idan bazaki yi mu’amala da ita ba ? Ko kina ba’kin cikin kudin da ta fara samu bakamar ke da kike a wahale ba? Gabaki d’aya maida kansu sukai wajan wacce tayi maganar , Husna ce tsaye sai faman harararsu Abla take , babu Wanda ya tanka mata tsakanin ilham da Abla, Hakan sai ya ‘kara ba’kanta mata musamman ydda Abla ta sakar mata murmushi tayi wucewarta, itama ilham wucewarta tayi batare da tace musu komai ba , tsaki husna taja dan ba haka taso ba â€? Alhaji sammani yace na fad’a miki yana waje yana jiran ki, karki saurari maganar su? Ba’kin ciki suke miki dan sun fara ganin kin fara samun kudi, da suke cewa karuwanci, me kikayi a ciki dan kawai an shafa ki? Ki rabu dasu nima ke nazo kira daman Zinariyya tace mun akwai wani Alhaji da yake jira na, zo mu tafi â€? ta kama hannun Aneesa sukabar wajan gudun kar Abla ta fito ta hana ta zuwa.