← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 146

Sashe 72

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

FLASH BANK
Abunda ya faru jiya bayan Big Boss da Bobo sun fita , details d’in wasu yan mata ne guda biyu da akai kidnapping d’insu a cikin New York , cikin ‘kan’kanin lokaci bobo ya bincika bayanan yaran har ya samu details d’in ’kasar da aka fitar dasu , wannan dalilinne Big boss ya basu umarnin zuwa Canada tun a daran jiya , shiyasa washe gari da sassafe Bobo dasu Robert sukabar New York , tsakanin America da Canada tafiyan hour 3 ne a jirgi kasantuwar private jet suka hau 2 hour 20minute ne ya kawosu kasar Canada . Wannan ne dalilin zuwan su bobo Canada shiyasa kowa yayi mamakin ganin big boss a ‘kasar dan babu Wanda yasan da zuwansa ko dalilin zuwan nasa hatta bobo yayi mamakin ganinsa a canada.

******
**********
9:01pm na dare motocin bobo suka danno kai cikin asibitin, Daidai parking lot motocinsu suka tsaya , cikin Sauri robert ya fito ya bud’e masa mota . A yanxu babu ba’ka’ken kayan d’azu sabida yanda ya canza dressing zuwa blue d’in wando da white shirt d’in Riga sai wata white coat dayake sanye da ita sabida sanyin da akeyi . Tun kafun ya shiga cikin premises d’in asibitin likitan d’azu ya fito cikin sauri ya ‘karaso Inda bobo yake , cike da girmamawa ya furta � this way sir�, hakan ce kuwa ta kasance, bobo be shiga da kowa cikiba sai Robert da yake binsa a baya , shima bobo sabida facemask d’in face d’insa ne yasaka ya shiga cikin asibitin, sabida yadda asibitin ya d’au shiru sai d’ad’d’an kun mutane da suke giftawa. Kai tsaye floor 5 suka nufa cikin elevator , gabaki d’aya yanda wajan yake ba hayaniya ko kad’an ya tsarin wajan da ya banbanta da sauran zai tabbatar maka da waje na musamman suka shigo da bakowa ake iya kaiwa wajan ba , yar tafiya kad’an sukai kafun suzo Daidai wasu ‘kofofi guda biyu da suke nesa da sauran, tun kafun su shiga cikin d’akin suka soma jiyo murya kadan kadan daga ‘kofar hagunsu , cikin sauri doctor ya bud’e bobo ya shiga. Babban d’akin asibitine me girman gaske da kallon farko da mutum zaiyiwa d’akin zaisan bakowa ake kawowa ‘bangaran ba tundaga kan yanayin d’akin mutum zaisan a cikin d’akunan ma Wannan Vip ne .
Cikin Sauri doctor da bobo suka ‘karaso cikin d’akin ganin nurses a tsaye sai faman furta � calm down� suke Sabida yadda Abla ta burkice gabaki d’aya sai kuka take tana ‘ko’karin cire ledar ruwan da aka saka mata, ga rigar big boss da tayi mugun yi mata yawa amma Sabida yadda bata cikin nutsuwarta taki bari a cire mata balantana Tasha iska . Cikin French doctor d’in yake tanbayarsu abunda yake faruwa, nurse d’in kusa da shine ta basa amsa da � Dr taki tsayawa ta kwantar da hankalin ta, hakan kuma xai iya ja mata matsala a brain d’inta sabida allurar da aka dunga mata ba Bisa tsari ba �, kallan doctor bobo yayi alamar ‘karin bayani sabida maganganun nurse d’in nan duk a cikin kunnansa , yana ‘ko’karin masa bayani Abla ta ‘karasa sakin wani saban ‘kara muryarta har sha’kewa take wajan furta � karku ta’bani ni banaso, ina ne nan ? Su wanene ku ?� Iya abunda Abla take furtawa kenan ga gashin kanta da ya rufe mata fuska ba’a ganin face d’inta sosai , ganin taki na tsuwane yasa bobo ya d’an daka mata tsawa kad’an lokaci d’aya kuwa tayi shiru kamar ba itaba, a hankali ta d’an d’ago da face d’inta basu sauka ko ina ba sai akan fuskar bobo da ya tsaya yana kallan ikon Allah , yadda ta tsaya tana kallansa ga gashi duk ya rufe mata fuskane yasa ya d’an harareta kafun ya nuna wa nurse akan suyi abunda zasuyi mata , da ‘kyar tabari nurse d’innan ta ta’bata Sabida ganin yadda bobo ya kafeta da ido, ga tsoro ya kamata sosai ganin fararan mutane cikin zuciyarta sai addua take ganin kyaun bobo ga shi dukda ba sosai take kallan fuskarsa taga ko murmushi bayayi, d’an ta’be baki tayi kad’an kafun ta furta � mugu da alama maganin mutuwa zasu sakamun, ai gwanda na mutu ma kowa ya Hutu,� duk wannan zan tukan cikin zuciyarta take yinsu can kuma ta ‘kara ta’bile bakinta tana had’iye kukan da yake ‘ko’karin fito mata ga tsayuwar su bobo ko nunfashi sosai taji ja, � yanxu shikenan uwar karuwai ta siyar dani wajan ‘yan ‘yankan kai?”yadda bobo ya kafeta da idone yasa ta ‘kara shiga taitayinta gabaki d’aya a tunaninta bobo shine shugaban yan shan Jinin shiyasa yake kallanta yana Tuna’nın yadda zai tsotse mata Jini.(😂😂😂wonder shall never end 😂😂 bobo ya zama shugaban yan shan Jini ).
Chapter 72 · 0% Book details