← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 146

Sashe 87

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

SORRY UPDATE DIN YAU BA YAWA 👏👏�
https://chat.whatsapp.com/EiJWfeCdg234T6P0k5NU2Y

IBTISSAM
( A heart touching story of love and destiny)

Story & written
By
Mss Lee �

Littafin IBTISSAM is now 300 , me bu’katar ya karanta littafin har ‘karshe zai iya biyan kud’insa ta wannan bank d’in 2681892316, zenith bank , Aisha umar, sai a turo da shaidar biya ta wannan number 07041879581.

MARUBUCIYAR * Gidan Aunty * and now *IBTISSAM*

💞ALL PRAISES ARE FOR ALLAH IN ALL CONDITIONS 💞.

O Allah ,ya hafeez , help and protect the people of Palestine 🇵🇸. O Allah, ya lateef ,ease their pain and suffering in Gaza . O Allah , ya Rahman,bestow your mercy on them . O Allah , ya Fattah,open the door of sustenance & provide relief to the besieged😭😭.

___💕 BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM 💕___

BOOK 1

SORRY FOR THE TYPING ERROR BANYI EDITING BA!!👏👏�

S____24💞

Ihun ‘karar da tayine yasaka cikin Sauri little da prince Suka tunkari d’akin simba , cikin Sauri Victor ya tare Hanya, kamar little zaiyi kuka ya ‘kara kauce wa zai shima amma still Victor ya tare masa hanya, a zuciye ya furta � wallahi Victor idan baka matsamun a hanya ba zankira yaya na fad’a , dan zalimci kana ji sister tana ihu amma zaka hanani shiga�, kamar Wanda yake magana da gunki dan gabaki d’aya tunda Victor ya tsaya be motsaba , gashi ko kusa be d’ago kansa ba balantana su suka ran zai basu amsa , shima prince cikin cool voice ya furta � Victor allowed us to enter plx , ba abinci kawai yaya yace ta tunda kaiwa ba ? Then ka barmu mushiga muga lagiyarta � nan ma shiru Victor yayi masa dan ko d’agowa ya kallesu bayayi, duk yadda suka so shiga ciki Victor ya’ki tanka musu balantana su saka ran zai amsa .
A cikin d’akin kuwa tunda Abla ta ga simba ta sume bata ‘kara motsawa ba kamar wata matacciya, shima simba Abla ya soma zagayewa tunda ga farkon kafarta har zuwa Kanta , lokaci zuwa lokaci kuma yana bud’e bakinsa kamar me shiri kai mata hari, daya ga bata motsi kuma sai kawai ya zauna a gefenta yana kallanta , banko ‘kofar da akai da ‘karfine yasa ka Simba tashi tsaye yana bud’e bakinsa da farcinansa . Bakowa bane yashigo cikin d’akin face little da prince da sukai ‘ko’karin ture victor suka shigo dukda kasancewar sa right side din big boss amma bazasu iya barin sister d’insu cikin ma wuya cin haliba musamman da ya kasance karo na farko da ta fara yin arba dasu , gabaki d’aya little ya rud’e kamar yayi kuka haka yakeji ganin gabaki d’aya bata motsi , simba yazo zai ta’basa little ya banka masa harara kamar Wanda zai fahimci harararsa ake. Dube dube little da prince suka soma ko zasu ga ruwa a cikin d’akin amma gabaki d’aya babu sai wani ruwa da may be simba ya sha shi shiyasa basu yi ‘ko’karin d’ibarsaba . Cikin Sauri prince ya bar d’akin shikuma little ya saka gabaki d’aya hannunsa guda biyu yana fiffita mata , simba na gefe shi kuma ya tsura musu kamar Wanda yasan me suke yi , ba a d’au dogon lokaci ba prince ya dawo cikin d’akin dauke da bottle water , cikin Sauri little ya zuwa a hannunsa tare da fesawa Abla amma kamar Wanda yayi da gawa dan ko kad’an Abla bata motsawa ba , hankali a tashe little ya ‘kara d’ibar ruwan ya fesa mata , cikin ikon Allah taja wani irin doguwar ajiyar zuciya , tun kafin ta bud’e eyes dinsa tasaka wani irin ‘kara tare da fashewa da kuka � Dan Allah kayi hakuri bazan sake ba , Dan Allah zai cinye ni ku fitar dani daga Wajan nan , daman nasani babu Wanda yake sona gashi anyi kyautar namana, shikenan zakine xai cinye ni , Wayyo Allah na, shikenan na mutu, na mutu Wayyo zai cinye ni�, abunda Abla take iya fad’a Kenan cikin shash she’kar kuka , ga idanuwanta da ta’ki yarda ta bud’e duk atunaninta naman jikinta simba zai cinye, yanda yake faman zai cinye ta da surutun da take yasaka gabaki d’aya little da prince tsayawa , shi prince dariya ce ma ta kusa ‘kwace masa lokacin da take furta � shikenan na mutu, na mutu � ganin ta’kiyin shiru ne yasa little jijjiga ta � sister bud’e idanuwanki babu abunda zai miki� ai Abla tana jin hakan amaimakon ta bud’e idanuwanta sai ta ‘kara fashewa da kuka � Aidaman nasani, na mutu kawai ,Wayyo Arwa please kizo ki temakeni� da karfi little ya furta sister da yasaka cikin sauri Abla ta bud’e idanuwanta, tana bud’ewa kuwa ta ‘kara cin karo da simba, wani saban kukan ta ‘kara fashewa dashi gabaki d’aya fuskarta tayi ja na tashin hankali sumamman hancinta, da Sauri zata ‘kara sakin wani kukan little yayi saurin furta � sister kiyi shiru babu abunda zai miki, kika cigaba da masa ihune fa zai cinyekin� ba kai ga ‘karasa maganar saba Sabida d’if d’in da Abla tayi kamar ruwa ya cinyeta, sai faman muzurai take, gana ganin yadda ta ‘bata face d’inta ’kiris take jira simba yayi wani motsin ta ‘kara fasa ihu. � babu abunda zai miki fa , simba d’in yaya big boss ne fa�, kamar zatayi kuka Abla ta furta � daman ba d’an uwan ku bane simban? Dan Allah ka bashi hakuri kalli yadda yake kallo na , da bakuzo da tuni ya cin ye na mana ya bar ‘kasu suwan�, shima little yanxu dariya ce ta’ke ‘ko’karin kwace masa dan bin hakkı Abla iya gaskiyar ta take magana , � ki kwantar da hankalinki simba fa baya cizo, kalla ma kigani � ya ‘karasa yana shafa kan simba, kamar wata aljana haka Abla taja bata tsaya a ko ina ba sai a bakin ‘kofa , cikin d’an ’bata rai kad’an ta bankawa simba harara � mugu kawai Allah sai ya saka mun kuma namana kurrr� sai kuma fitt kamar wata aljana tafi ce daga d’akin, little da prince me zasuyi kuwa Inba dariya ba , tsabar dariya prince handa tsugunnawa ‘kasa , wannan shi ake kira � ga tsoro ga ban tsoro� duk Wanda ya kalli fuskar Abla 100% zai bawa kowa tabbacin innocent ce ita amma da alama za’ayi yar bala’I , gabaki d’aya wannan zan tukan cikin zuciyar sa yake yi , shi gabaki d’aya ya fara hango irin dramer da za’ayi dan wallahi yasan ba ‘karamun cud’ata big boss zaiyi ba kamar kayan wanki, ganin shirun yayi yawa ya cikin Sauri little ya janyo wa simba abincinsa suka fito, babu kowa a wajan sai Victor da yake can bakin gate , tunda Suka gansa kuma sunsan Abla tana wajan tun da ba lalle ta iya ‘karasawa wucewa ba , amma abun mamaki babu ita babu alamarta, har sunzo giftawa ta wani bishiyar mangwaro sukaji kamar siiissii da baki, cikin Sauri gabaki d’aya suka jiya bayansu amma basu ga kowa ba , a karo na biya aka ‘kara yi musu siiii siii , shima still ‘kara juyawa sukai basu ga kowa ba , sharewa sukai suna ‘ko’karin cigaba da tafiyarsu kamar wata aljana sai ganinta kawai sukai daga sama ta diro daga saman bishiya, cikin Sauri sukaja baya prince har yana ‘ko’karin saka gudu , Abla da Suka ganine yasa gabaki d’aya mamakinta ya kamasu � sister me kikeyi asaman bishiya ?� Kamar zatayi kuka ta nuna musu direction d’in da Victor yake , � Na kasa wucewa ne� shiyasa kika d’ane bishiya ?� Cewar prince , kanta ta jinjina masa kafun ta furta � tsoro suke bani Wallahi, saura kad’an zuciya ta tabuga sabida halittar da nagani�, cikin yar dariya dariya little ya furta � Ai zuciyarki bazata buga ba Indai kina gidannan, amma fa simba ba d’an uwan mu bane, zakin big boss ne� lokaci d’aya Abla taji kwalla na tarar mata a ido � Toh dan Allah ku bashi ha’kuri kunji�, had’a ido little da prince sukai cikin sauri prince ya furta � karki damu indai kinajin maganar yaya toh bazai miki komai ba , duk lokacin da ya bada umarni kawai kibi kinji� Kanta ta jinjina musu cikin sauri dan ita yanxu bata san abunda zai had’a ta dashi tunda har yake ‘ko’karin sawa a cinyeta � Allah saiya saka mun�, cewar Abla cikin zuciyarta , Tunanin me kike ?� Prince yayi saurin katseta, � babu komai�, cewar Abla , � oya taho mu tafi toh , ya kamata mu koya miki yadda ake had’awa yaya coffee d’insa , yanxu hud’u takusa ya kamata ki koya kafun ya dawo , idan ba haka ba a d’akin simba zai kulleki�, cewar prince � Dan Allah da gaske kake ?� Cewar Abla, ganin tana ‘ko’karin yin kuka ne little yayi saurin kallansa � yaya prince Menene haka plx , kanaso ka sata kuka ? Allah zan fad’awa yaya idan ya dawo � cikin Sauri prince ya furta � sorry yaya Adil , nayi shiru ku taho mu tafi � daga nan basu kuma cewa komai ba , lokacin da su Abla zasu wuce Victor shima sai da kyar ta iya wucewa , hatta cikin farfajiyar gidan da ‘kyar Abla tayi wucewa Sabida sojojin da suke wajan shima saida prince da little suka kakkareta , da ‘kyar da ‘kyar Suka samu ta wuce shima tana tafiya tana juyowa , ko kuma motsi kad’an ta zabura , saida suka shiga cikin falourn ta saki wani irin ajiyar zuciya da har saida little ya bata ruwa Tasha. Basu dade ba suka nufi coffee maker , gabaki d’aya yadda ake had’awa big boss coffee saida suka koya mata , da abunda ake samasa da abunda ba’a sawa , hatta irin cup d’in da ake saka masa coffe d’in saida suka nuna mata , gabaki d’aya babu abunda basu koya mata ba na tsarin shan coffee d’in big boss, abu na farko da suka fara fad’a mata ba’akawo wa big boss coffee me d’imi sai me zafin gaske , dan idan ya salamce kada ta kuskura ta bashi, cikin ‘kan’kanin lokaci gabaki d’aya Abla ta gane yadda ake had’a coffee d’in cikin sau’ki sabida baiwar kwakwalwa da saurin fahimtar abu da Allah ya bata . Lokacin sallahr la’asar nayi su little suka tafi masallaci itama kuma Abla ta koma cikin d’akinta, tana idar da sallah d’akin ta gyara tunda little ya nuna mata komai na , hatta kayan da Suka siyo mata suna cikin kwaba a ninke, rayuwa ce daman ta mayar da ita ‘kazama amma mutum ce me sam tsafta musamman turare da take mugun so , a d’aki tayi zamanta dan gudun kada ma ta had’u da sojojin gidan ko d’au uwan kyakkyawa ( sunan da ta sakawa big boss ), tunda ta shigo d’aki shine yake faman yi mata yawo a cikin zuciya , duk lokacin da ta tunasa kuma sai taji bugun zuciya ko taji wani irin yar a jikinta, tana kanta na neman yi mata ciwo ne yasa ta ‘karasa wajan window d’in d’akin, tana d’agawa ta hango sojoji, cikin Sauri ta saki labulen d’akin tana dafe zuciya , kamar wacce aka saka sai kuma ta ‘kara le’kawa kad’an , cikin Sauri ta ja baya tana sakin ajiyar zuciya � su gidan nan gabaki d’aya ‘kartin mutane ne a ciki? Toh Ina maman su da babansu?”ita kad’an sai tanbayar kanta take , amma duk da haka bata daddara ba sai le’kensu take ta window d’in musamman wasu flowers da take hango wa masu kyau kamar taje ta tsun’kosu haka taje ji.
Chapter 87 · 0% Book details