← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 146

Sashe 143

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Cikin wani irin shock Abla ta ja baya ganin abunda tayi, jikinta har rawa yake , gashi sai faman girgiza kanta take hawaye na sakko mata a kan face d’inta , a hankali Big Boss ya d’ago da eyes d’in sa yana binta da wani irin kallon da shi kad’ai yasan ma’anar sa ,yadda yaga ta tsoratan ne yasa shi d’aga girar fuskarsa kad’an tare da matsowa inda take, itama Abla cikin sauri ta soma ja baya hawaye duk ya ‘bata mata face d’in ta , ko kusa ta ‘ki d’ago da idanuwanta balantana ta kallesa , haryanzu kuma be mata komai ba sai matsowa inda take da yayi, yadda taga yana matso ta sosai yasa bata san ina take zuwa ba har ta cigaba da ja baya itama, bata ankara ba taji ta a bango zata matsa yayi saurin saka hannun sa guda biyu a both side d’inta.
Abla kamar zatayi kuka ta kawar da face d’inta tare da kulle idanuwanta gam tana jiran jin irin hukunci da zai mata.
Murmushin gefen baki ya saki kad’an duk da be fito sosai ba , face d’insa ya matso da ita Daidai fuskarta kafun ya furta � open your eyes “kamar ya ‘kara zugata kuwa ta ‘kara kulle idanuwanta gagam, lumshe eyes dinsa Big Boss yayi tare da ‘kara bud’esu yana bin face d’in Abla da kallo, Babu mahalu’kin da ya ta’ba Marin sa ko da namiji ne sai ita , Wanda shi kad’ai yasan punishment d’in da zaiyi mata , a hankali ya ‘kara furta � open your eyes � yanzu ma kulle idanuwanta Abla ta ‘karayi a hankali ya sakko da hannunsa kan cikinta yana zagaye mata shi da öne finger d’insa , a razane Abla ta ware idanuwanta a kansa wasu hawayen suna ‘kara sakko mata, duk da yadda ta bud’e idanuwan nata be dena zagaye cikin ta da 1 finger d’in saba, cikin Sauri Abla tabuge masa hannun nasa , duk da ‘karfin hali ne take yi , cikin d’an masifa masifa ta furta � Ni karka ‘kara ta’bani…� bata kai ga ‘karasa maganar taba ya had’e lips d’insu waje d’aya , a razane Abla ta ware idanuwanta kamar zasu fito waje , lokaci d’aya jikinta ya soma karkarwa , ‘kafafunta sun mata sanyi, ‘ko’karin zamewa take ya saka hannunsa guda d’aya ya talla’bota , har yanzu kuma be saki lips d’inta ba duk da yadda taso kwace wa , ji tayi gabaki d’aya nunfashinta yana ‘ko’karin d’aukewa ga wani irin abu da yake ratsa mata tun daga d’an yatsar ‘kafarta har zuwa kwakwalwarta, duk yadda taso kwace lips d’inta Big Boss ya ‘ki bata wannan damar,a hankali wani irin hawayen takaici suka soma sakko mata daga cikin idanuwanta ,Ji take kamar lips d’inta zasu tsinke sabida tsabar rad’ad’in da suke mata, cikin ‘karfin hali da ragowar ‘karfin da yayi mata saura ta cije a lips d’in sa itama. A hankali ya soma bud’e eyes d’insa da suka soma canza kala zuwa launin ja , yadda yaga ta kawar da kanta gefe tana ‘ko’karin kwace jikinta yasa ya motsa lips d’insa kad’an kamar Wanda yake shirin murmusasu, cikin cool voice kamar bashi ba ya furta � Marin da akai mun kuma da me zan rama ? � banza Abla tayi masa sai ma faman kwace hannunta da take ‘ko’karin yi , a hankali ya furta � it’s Okay � cikin ‘kasan ma’koshi kamun ya soma bud’e bottom d’in rigarsa cikin Sauri Abla ta ja baya , wasu hawayen suna ‘kara sakko mata, gabaki d’aya ta tsorata da yanayınsa , ita kad’ai sai faman Kallan ‘kofa take , a hankali ta furta � kayi hakuri�, tsayawa yayi da ‘balle button d’in da yake kafun ya matso da face d’insa Daidai saitin kunnanta , a hankali ya furta� we’re so sweet Mrs Omar Farooq�, da wani irin ‘karfi Abla ta bangajesa ta arta na kuje cikin sauri ta janyo doguwar rigar ta , tunda ta turesa be motsa ba har ta ‘karasa wajan ‘kofa, da manyan idanuwan ta da suka cika da kwalla sakar masa harara cikin ‘kasa ‘kasa da murya ta � Allah sai ya saka mun d’an iska kawai � , sarai yaji abunda tace , shiyasa yayi kamar zai mi’ke , cikin tsoro Abla ta bud’e ‘kofar ta arta a guje, wani irin lallausan murmushine ya su’buce masa akan lips d’insa , har hakwaransa suna fitowa waje kad’an, yadda yayi murmushin ba’karamun kyau yayi ba kamar fuskarsa ta tsaya a hakan , ga dimples d’insa da suka lotsa sosai , a hankali ya fesar da iskar bakinsa , cikin ‘kasa ‘kasa da murya ya furta � Batajin magana�.

Hotunan da suke zu’be a ‘kasa ya kalla, lokaci d’aya mood d’insa ya soma canzawa , d’aya daga cikin hotunan ya d’auka me d’auke da hotan jariri a ciki, gabaki d’aya jikin yaron jinine da alama kuka yake aka d’auki hotan , a hankali Big boss ya lumshe idanuwansa ,tun bayan tsawan shekara 22 hotunan suke ajje, Sabida ko kusa bayasan tuno da abubuwan da suka faru,lips d’in sa na ‘kasa ya d’an ciza Kafun ya mayar da pics d’in cikin envelope . Gucci watches din hannun sa ya kalla , a hankali ya furta � Oh God � sai kuma ya mi’ke cikin nutsuwar sa ya nufi dressing room d’in sa .

Abla tana barin part d’insa cikin sauri sauri ta saka doguwar rigar ta , ga hawayen face d’inta da suka ‘ki tsayawa , har ta wuce uncle a falourn bata sani ba , gabaki d’aya bata cikin nutsuwar ta , kai tsaye d’akin ta ta wuce tare da saka wa ‘kofar key , cikin masifa masifa Abla ta furta � ‘Dan iska , mugu kawai , Allah sai ya saka mun , idan ka tashi hukuntani karka barni da raina kayanka ni gunduwa gunduwa �, tana surutun tana cire kayan jikinta , bata tsaya a bedroom d’in ba ta wuce toilet tayi a wanka . Ta d’au kusan mintuna 15 a cikin toilet d’in kafin ta fito , kallan fuskarta tayi a mudu bi, lips d’in ta har ya d’anyi ja sabida muguntar da yayi mata , lokaci d’aya kuma ta saka kuka me ta’ba zuciya � akan me kake ‘ko’karin zagar mun iyayen da bansani ba suna raye ko sun mutu, bana san ka , bana ‘kaunar ka , Nima na tsaneka kamar yadda ka tsaneni , mugu kawai � ita kad’ai sai sanbatu take yi, lokaci zuwa lokaci kuma tana mitar abunda yayi mata. Doguwar Riga kawai ta saka ajikinta , tunda ta kwanta akan gado take juyo , gabaki d’aya ta rasa meke mata dad’i, da ta kulle idanuwanta abunda ya faru a tsakanin su yake sake dawo mata , cikin ‘kan’kanin lokaci Abla ta rud’e jikin ta yasoma rawa kamar me zazza’bi, duk yadda taso bacci ya d’auke ta abun ya ci tura , sai fuskar Big Boss da ke faman yi mata gizo a duk lokacin da ta kulle idanuwanta , har wajan ‘karfe 2 idanuwanta biyu , sai juyi take akan gado da ‘kyar wani irin wahalallan bacci ya d’auke ta .
***** 3:10am
Cikin wani irin d’aki me duhun gaske ta tsinci kanta , ga wasu irin abubuwan tsafi dake cikin d’akin ta ko ina , a tsorace Abla ta soma bin cikin d’akin da kallo hankali a tashe , � Abla ! Abla ! Abla � sunan dake faman kira Kenan , cike da tsoro Abla ta d’aga kanta sama Sabida muryoyin wad’an da taji , a gigice ta ‘kwalla kara kafun ta soma kiran � Eshaal , Baby ,Fanan ku matsa zasu kashe ku, ku matsa ,� cikin kuka Fanan ta girgiza mata kai � Abla mutuwa zamuyi, suna bin mu duk Inda muke , ke kad’ai ce zaki iya cecen rayukan mu,� cikin Sauri Abla ta soma ‘ko’karin kwance kanta , amma igiyar kamar merai da tayi ‘ko’karin kwance wa zata ji igiyar ta ‘kara matse mata jiki . Da ‘karfi su Fanan suka furta � Abla…� suna furta sunan ta gabaki d’aya Jini ya fara fito musu ta baki da ta hancin su , ihu Abla ta saki tana ‘kokwarin kwace kanta , da tayi ‘ko’karin Yin addua zataji an matse mata ma ‘koshi , gasu Baby da suma sai fitar da Jini suke ta baki , cikin azaba Abla ta furta “Ya Al…Al…Allah�, cikin ‘kan’kanin lokaci igiyar data d’aure ta , ta ‘bace batt babu ita , tana kai dubanta idan su Fanan suke taga nan ma wayam babu su babu a lamarsu, wani irin jiwane ya soma kamata , gani take kamar ba’kin dakin yana juya mata , da’karfi ta toshe kunna wa tare da kurma ihu *****
Bakinta cike da addua Abla ta farka daga baccin da ya d’auketa , gabaki d’aya jikin sai faman d’aukar rawa yake ga wani irin zufa da ta had’a ta ko ina , wayar ta tayi saurin janyowa tare da kunna karatun alqurani, kusan mintuna 5 tana zaune tana sauraran al_qurani me girma, kafun ta soma a jiyar zuciya a hankali Sabida nutsuwar da ta soma samu cikin ranta .

***WASHE GARI***
Chapter 143 · 0% Book details