Sashe 58
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
big boss da ya soma tafiya kai tsaye d’akinsu little suka nufa yadda suka ga kowannansu a tattakure ne yasa suka bisu da kallo, heater din dakin bobo ya kunna ya kashe musu Ac, tare da dakko wani man zafi guda biyu ya mikawa big boss d’aya , a hankali big boss ya bude magani tare da sakawa little dinsa a kafarsa, a hankali yake matsa masa kafar cike da kwarewa , shima bobo hakan ce ta kasance , prince yake shafawa a kafar sai da suka tabbatar man ya shigesu sannan suka ajiye, gashin kan little big boss ya ta’ba Daidai lokacin da little ya rike hannunsa cikin bacci, a hankali yake furta â€? am sorry yaya big boss , am sorry yaya boboâ€?, duk cikin magagin bacci yake furtawa , â€? kansa big boss ya shafa kawai yana lumshe eyes dinsa da hakan ya zamar masa tamkar a jininsa tare da gyara masa kwanciyar sa sosai , kafun su bar dakin sai da ya kara tabbatar da lapiyar bugun zuciyar little sannan suka kashe musu light, a bangaran uncle ma lokacin da suka shiga d’akinsa yayi bacci shiyasa bobo ya rage masa sanyin Acn dakin . Big boss na tsaye a falon hannunsa sanye cikin aljihu haka bobo kamar yadda yasaba kullum saida ya tabbatar da lapiyar komai na gidan kafun ya dawo cikin falon har lokacin big boss na tsaye ko gajiya da tsayuwar bayayi , sai da yaga shigowar bobo sannan ya juya zai bar Wajan , cike da tsokana bobo yayi saurin karaso wa inna yake “daga ganina kuma sai kajuya ? Hira fa zaka zo muyi â€?, big boss bai tanka masa ba sai hannun sa d’aya daya daga ya kaiwa bobo naushi, cikin azama bobo ya kauce yana dariya “ba’a banza ba little ya iya mugunta ba faâ€? cewar bobo yana kashe wa big boss ido d’aya alallai sai ya nemi rigima dashi , dauke eyes dinsa big boss yayi tare da soma takawa zuwa elevator har ynxu bobo na biye dashi , sai da ya shiga ciki tukunna lokacin da bobo yazo shiga big boss ya hanka dashi baya ya kulle bayan wani irin kallo da ya jefa wa bobo , har yanxu bobo dariya yake masa musamman yadda yaga ya hade rai . Gabaki d’aya light din ya kashe ya bar dum tukunna ya koma part d’insa , ba jima ba ya kwanta shima . Big boss kuwa yana komawa part d’insa system dinsa ya janyo ya soma operating dinta cikin kwarewa kamar ba dare ba Sabida yadda ko damuwa da ya kwanta ba yayi , ya dau tsawan lokaci yana operating akan system din nan sai wajan karfe 4 ya kashe system din , still be kwanta ba sai da ya kara komawa part din su little wannan karan har dakin bobo ya shiga , duk da yadda bobo ya girma hakan be hana big boss gyara masa blanket ba kamar yadda ya sabayi masa, sai da ya tabbatar shima he’s okay tukunna ya koma part dinsa. Daidai Wajan balchony ya tsaya yana shakar daddadar kamshin wajan ko damuwa da yadda dare yake karayi bayayi ga sojoji da suke yawo ta ko ina . Yana tsaya akai kiran sallar Asuba , saida aka gama kiran salla ya bar wajan , cikin kankanin lokacin ya kara Shiryawa cikin wasu cotton kaya farare tas dasu , yau gashin kansa a nannad’e be tufkeba, ga kamshin turaransa ta ko ina da ya kama dakin. Tun kafun ya sakko down stairs prince da little suka fito falo, yau sun ruga kowa tashi daga bacci dan wallahi big boss ya Riga su fitowa suma sun san sauran shiyasa duk lokacin da yake gida suka saka alarm, Allah ya temakesu tun 6pm na yamma jiya prince ya saka musu alarm , uncle da bobo ma kusan lokaci d’aya suka fito suna jiran fitowar big boss. Saida suka kara kusan 10 minutes tsaye a wajan tukunna ya fito gabaki d’ayansu suka nufi masallaci dakaga fuskar little zai baka tausayi Sabida canjin face dinsa yau ko fara’a bayayi so yake yaya ya kulasa amma gabaki d’aya babu Wanda ya kula a cikinsu har suka tafi masallacin. ðŸƒðŸƒðŸƒðŸƒðŸƒ ABLA Da ido ta fara bin dakin da kallo tana Tuna’nın ta yadda za’ai tayi sallah, batasan ya zatayi ba tunda ko kwakkwaran motsi bata iyayi da gabbanta, sun cutar da iya iya cutawa da bazata ta’ba yafe musu ba , da’kyar ta iya jan jikinta ta jingina da bango tana lumshe eyes dinsa da hawaye suke sakko mata , yunwa take ji ba kadan ba tun safe bata saka komai a cikin taba gashi har yamma tayi bata ci komai , jinta take kamar ‘ya’yan cikin ta zasu fito waje , tunanin yadda zatayi sallah kawai take cikin ranta da tayi kokarin mikewa zataji jiri na neman kayar da ita , bata da wani zabi face tayi niyya cikin zuciyarta ta rama sallolinta. Sai wajan karfe 8 aka kara bude kofar dakin da take , wannan karan ba a shigo ciki ba sai ledar bread da aka jefo mata tare da pure water guda d’aya aka sake kulle ta , dukda tsananin yunwar da take ji ko kallan inda bread din yake batayi ba ta kara silalewa a kasa ta kwanta cikinta har wani yaji yaji yake mata na yunwa , a haka wani irin wahalallan bacci ya d’auke ta . Binta shagala kuwa daga waje ta bada umarnin ajefawa Abla bread da ruwa dan bil hakki lokaci d’aya taya taji wani irin tsoran Abla ya shigar mata zuciya babu abunda yafi tsoratarda itama kar ace Abla tana da aljanu dan dukan da Abla tayi mata har yanxu bata dena shakkar tava , gani take Aljanun Abla ne suka tashi shiyasa bata kara tun karan ko inda dakin yake ba .