← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 146

Sashe 12

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

✨✨✨✨✨✨

NIGERIA

ABUJA

ADEMOLA ADETOKUMBO STREET

Karfe 3:30am na safe uwar karuwai ta banko d’akin dasu Abla suke a kwance ita da ilham , ruwan fridge d’i data shigo dashi me shegen sanyi ta watsa musu, a firgice suka farka sabida yanda ruwan sanyin ya sauka a jikinsu ga sanyin asuba daya fara busosu, cikin karkarwa ilham ta kalli uwar karuwai a tsorace , Abla sosai jikinta ya soma karkarwar sanyi, cikin wani irin shegen kallo uwar karuwai tabi kirjin abla da kallo gabaki d’aya hankalinta yana kan ‘kirjin Abla da ruwa ya ta’ba , fahimtar hakan Yasa Abla tayi saurin saka hannunta cikin hijabinta tana adduar neman tsari daga sharrinta ,dogon tsaki uwar karuwai taja � dan ubanku sai nace muku ku Tashi ku fara aiki? Tsinannun yara da basu san hanyar arziki ba, daka yanxu tsarin aikin ku ya canza , dake da wannan shed’aniyar yarinyar ku zaku dungayin aikin komai da komai na gidan nan tunda kun ‘kibin hanyar arzikin da na saku sannan kullum zaku dinga kawo mun 500 kud’in zaman d’aki , duk ranar da kuka kuskura baku kawo ku d’innan ba ku tabbata ranar sai nayi kud’i daku dan akwai Alhazawa dayawa da suke kwad’ayinku, shegun yara masu kashe wa mutum kasuwa , idan kun gama ke � ta nuna husna � ki sameni a d’akina “‘kara kallan ‘kirjin Abla tayi da kallo kamar idanuwanta zasu fad’o ‘kasa kafun ta bar d’akin tana sakin ajiyar zuciya . Hannu ilham ta d’ora aka “nashiga ukuna�, sauke mata hannu Abla tayi, kuka ta fashewa Abla dashi � na shiga uku Abla , matarnan bata tsoran Allah babu Allah aranta, Kema kinsan duk Wanda takira d’akinta toh ba abun alkairi zatayi dashi ba , Abla ina tsoron matar nan , ki temakamun Abla dan Allah �, idanuwanta da suka fara ‘kan’kancewa kamar zatayi kuka Abla ta lumshe kafun ta rungume ilham � karki damu ilham, insha Allahu Allah yana tare damu babu abunda suka isa suyi mana , ki share hawayenki da yardar Allah ita bata isa tayi miki komai ba kinji?�, girgiza mata kai ilham tayi zata kuma magana itama Abla tayi saurin dakatar da ita� Karki damu babu abunda zai sameki kin manta kina da Abla �, ajiyar zuciya ilham ta saki � nagode Abla � hawa yan idanuwanta abla ta goge mata � karki damu insha Allah babu abunda zai sameki, har yanxu su Anee basu dawo ba? Allah yasa suna lapiya suma � hawayenta ilham ta share � Amin Abla Nima nayi mamaki danaga har yanxu basu dawo ba �, jinjina mata kai Abla tayi kafun ta mi’ke tsaye � ya kamata mu fara gyaran gidan nan kafun su dawo , ki fara gyara d’akunan ‘kasa ni sai na hau na yi nasa kafun ayi kiran sallahr asuba �, toh kawai ilham tace mata lokacin gabaki d’aya baka jin motsin kowa sai su biyu da suke aiki tun kafin Garin Allah ya waye, Tun wajen 4:00am na asuba suka fara aiki lokacin da kowa yake runtsawa har akai kiran sallah asuba basu gamaba sabida ydda d’akunan suke a har gitse, basu suka kammala ba sai wajan karfe 9:00am, ganin lokacin sallah na kurewa ne yasa sukabar aiki suka shige d’akinsu, saida suka tabbatar sun kulle yadda su Zinariyya bazasu iya bud’esu ba tunda dokar uwar karuwai ne ,duk wacce aka kama tana mata sallah a cikin gida sai tasa Ammata dukan kawo wuka kamar ba musulma ba, suna idar da sallahr azkar d’in safe da maraice sukayi kamar yadda Abla ta saba koya musu, cikin Sauri suka mi’ke zasu fito ilham ta tsayar da Abla , inda ta ajje musu ledar jiya ta bud’e tare da d’akko musu manyan biscuit da zasuci � Abla wallahi yunwa nake ji ki bari idan munci Abinci sai mu cigaba da aikin”murmushi Abla ta sakar mata � Tohm kiyi sauri ki kammala kinsan ako da Yaushe zasu iya dawowa�, gyada mata kai ilham tayi kafun ta miko mata ledar biscuit d’in guda d’aya � da Sauri Abla ta girgiza mata kai � Azumi nake �, sakin baki ilham tayi, itama Abla manyan idanuwanta ta lumshe mata , gudun karta ‘kara wata maganar yasa tace “kiyi sauri bamu da lokaci�, da Sauri kuwa ilham ta soma cin biscuit d’in, saida ta cinye manyan biscuit d’in kafun ta soma ajiyar zuciya , da sauri kuma ta tattara ledojin biscuit d’in ta Mayar cikin ledar data ‘boye cikin wani fasash shen gini daya lalace. Cikin sand’a suka fito daga d’akin gabaki d’aya ajiyar zuciya suka sauke ganin su Zinariyya basu fito ba, uban kayan wanke wanken da aka ‘bata masu shegen yawa su Abla suka fara had’a ita da ilham, basu suka kammala wanke wanken nan ba sai wajan karfe 12, lokacin da su Zinariyya suka fito kowa yana hamma acikinsu . Kallan su Abla Zinariyya tayi kafun ta ja wani dogon tsaki � matsiyata kawai �, acikin su babu Wanda ya tanka mata saida suka kammala komai , sai alokacin fargaba ta soma kama su Abla , musamman da ilham ta tuna mata kiran ta da Uwar karuwai take , Jim kad’an Abla tayi kafin ta kalleta cikin ‘kasa ‘kasa da murya � mu gudu sai mu dawo anjima � da Sauri ilham ta girgiza mata kai cike da tsoro� a’ah Abla Nidai ina tsoro wallahi�, kama hannunta Abla tayi � idan bamuyi hakan ba kinsan me zatayi miki idan kika shiga d’akin? Ko kin manta lokacin datasa kawayen ta su danneki tana ‘ko’karin farka miki kaya Allah ya ceceki daga cikin zaluncinta ?� Ajiyar zuciya ilham ta saki, ganin hakan yasa Abla taja hannun ilham Suka gudu, sunzo fita daga gidan Zinariyya ta hangosu, duk yadda taso taresu abun yaci tura saida suka gudu, tsaki zinariyya ta saki tana taunar le’ben kasan bakinta.

✨✨✨✨�

UNITED STATES
Chapter 12 · 0% Book details