← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 146

Sashe 60

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Koda aka idar da sallar asuba babu Wanda ya ‘bata lokaci tsakanin prince da little , cikin kankanin lokaci ko wannansu ya shirya cikin sport dinsa na training , musamman yadda suka ga big boss be shigo cikin gida ba , hakan ya basu tabbacin ko minti d’aya suka kara zasu gamu dashi . In ka kalli face din little yau zaka ga gabaki d’aya babu walwala a tattare dashi, daga big boss har bobo suna sane da halin da yake ciki, shi bobo yayi masa shirune sabida big boss yayi masa magana , big boss kuma izza da miskilanci ya hana ya kulasa. Cikin Sauri gabaki d’aya suka shirya tare da fitowa , cikin kankanin lokaci suka nufi wajan training, Wanda suka ganine yasa suka sha jinin jikinsu ganin sa a tsaye yayi folding hannayensa , zasu soma magana ya zuba musu rikitattun eyes dinsa da yasa ko wannansu yin shiru . Hatta sojojin da suke cikin wajan kowa cikin kwarewa yake motsa jikinsa dan idan tsautsayi yasaka kayi mistake babu ruwan big boss wai kai sojane, sawa zaiyi a rataye masa kai na 2 hours shiyasa ba karamun mugun shakkarsa suke ba . Cikin sunkuyar da kai suka nufi main dakin da suke motsa jiki, suna shiga Suka tarar da ba kowa a ciki shiyasa wani irin dadi ya kamasu , prince harda buga tsalle ganin bobo baya ciki yasan da wuya shima big boss ya shigo shiyasa ko wannansu ya d’auko abun motsa jiki mara sa wahala . Shi little da yafi kowa ma wani mat na training ya shinfida tare da daukar babbar balloon da ake motsa jiki da ita , prince Kuma skipping rope ya dauka shima , a tunaninsu big boss bazai shigo ciki bane shiyasa suka d’auki ‘kananan abubuwan nan ,prince yana cikin skipping dinsa juyawar da zaiyi kawai idanuwansa ya sauka kan big boss da yaya bobo dake gefensa, shi kansa besan lokacin da ya kusa hantsulawa ba , da Sauri ya yardar da I giyar shi little gabaki d’aya be kula da yanayin da Prince yake ciki ba sabida kulle eyes dinsa da yayi , kallan da big boss yake bunsu Dashi kadai ma yasa hantar cikin sa kad’awa , da Sauri prince ya ta’ba little , shima yana bud’e eyes dinsa yayi saurin mikewa tsaye , cikin rawar murya ya furta � yaya please kuyi hakuri kunji?� Ya karasa da niyar matsowa inda bobo yake sabida yadda yake tsoran Kallan side din big boss , shima bobo kallan da ya jefa wa little ne ya hanashi motsawa daga inda yake , big boss be ce muku komai ba sai juyawa da yayi ya bar wajan, shima bobo kallo d’aya yayi musu kafun ya furta � follow me� yaya please ka bashi hakuri , we’re sorry � cewar prince , amaimakon bobo ya bashi amsa sai ma cikin kakkausar murya ya furta � 2 minutes kawai na baku� yana kai karshen zancansa ya juya yabi bayan big boss , cikin rud’ewa prince ya fara furta Innalillahi wa inna ilaihi raji’un , little please ka bawa yaya big boss hakuri please� shima little kamar zaiyi kuka ya furta � fushi yake dani fa, ni tsoro nake ji� bai karasa maganar da zaiyi ba shida prince suka bar dakin a guje sabida minti biyun da bobo ya basu har yayi . Kamar yadda suka sani wajan horan sojojin da suka je jiya zasu nufa , shiyasa kai tsaye cikin ‘kan’kanin lokaci suka karasa wajan , yaya big boss baya wajan shiyasa gabaki d’aya suka saki ajiyar zuciya duk da kasan zuciyar su fall tsoran hukuncinsa suke ji, inda bobo yake a tsaye wani waje ne me kamar tiles ,yadda Wajan yake kyalli zai tabbatar maka da abun santsi sojoji Suka zubawa a Wajan , kallan kallo prince da little sukai kamar zasuyi kuka dan sun gane me zasuyi shiyasa tun kafun bobo yace su cire takalmansu Suka ciresu tare da tsayawa a Daidai sai tin wajan , wasu sojoji guda biyu Suka karaso Inda suke tare da wani fork a hannu saida suka rike fork din sosai kafun sojojin su saka musu kwai a kai , duk abunda yake faruwa bobo na kallansu bayasan ganin yadda face Dinsu take , shiyasa yadan daure face dinsa kadan � you can start , duk Wanda ya fadi a cikinsu zai fara daga farko , duk Wanda egg din fork dinsa ya fadi zai gane kurensa , you can start �, cewar bobo, prince yana saka kafarsa a wajan yaji yana kokarin sullu’bewa, da Sauri ya ja baya da yasa egg dinsa fashewa,� ^2� cewar bobo, shima little yana shiga yaji yana kokarin faduwa , saura kadan ya fadi shima amma Allah ya temakesa, saida yazo Daidai tsakiya ya su bale kwansa ya fadi, kamar zasuyi kuka haka ya kara dawowa farko , shima prince da yayi nisa santsi yake d’ebarsu suke faduwa , sunfi 20 minutes suna abu d’aya amma sun kasa karasa zuwa inda zasu ajje kwan, akan idan bobo duk abunda yake faruwa , gwanda shi yayi musu hukunci akan big boss yayi musu , idan ba hakaba ba karamun jigatasu zaiyi ba , yadda santsi yake kayar dasu ba karamun dariya da tausayi zasu baka ba , hatta little cikin faduwar da yayi saida ya Bige hannunsa amma ya ki bari bobo yagani shiyasa ya cigaba , ga zafi da hannunsa yake masa amma hakan ya cigaba da shiga cikin santsin yana fad’uwa , tun yana kokarin dannewa har ya soma hawaye , , shikansa bobo da yake kallansu ba dadin abin ya ke jiba , a ka’ida punishment 4 zaimusu amma ba xai iya ba shiyasa ya dakatar dasu ya bar wajan , Allah sarki little yadda fuskarsa tayi jajawur ba karamin tausayi zai baka ba , dakyar suka taka Suka koma cikin part Dinsu , babu kowa a cikin falourn kai tsaye d’akinsu suka shiga sukai wanka , shi prince sabida yadda ya gaji kai tsaye lapiyar gado yabi, little kuwa kasa kwanciya yayi Sabida tunanin yayansa da ya’ke shiyasa ya nufi part d’insa , ko da yashiga kasa tun karar dakin big boss yayi shiyasa ya kwanta akan sofa a takure , yasan bazai fito yanxu ba Sabida yanxu ne lokacin baccinsa , shiyasa shima yayi kwanciyarsa kan sofa , sai da ya dau kusan 20minutes kafun wani irin wahalallan bacci ya daukesa. Tun lokacin da ya shigo big boss ya gansa , amma miskilanci da izza ta big boss ta hana yace ya shigo d’akin, tsawan wannan lokacin yana zaune kan sopa yayi crossing legs dinsa , tun lokacin da little yake kwance kan sofa da yadda ya takura har yayi bacci duk a kan idan big boss , lokaci zuwa lokaci yana lumshe kyawawan idanuwansa sabida yadda yaji kansa yana sara masa , saida ya ‘kara d’aukar 10 minutes zaune a wajan tukunna ya mike ya nufi palourn da little yake a kwance, gabaki d’aya eyes dinsa ya zuba masa yana bin kyakkyawar face dinsa da tayi ja kadan da kallo, a hankali ya soma takawa har ya karaso inda yake a wance , hannunsa da yasa cikin aljihu ya fitowa dasu tare da daukar little kamar Wanda ya dauki wani jariri ya nufi d’akinsa dashi, akan lallausan king size bed dinsa ya kwantar da little tare da d’auko wani unique roba d’an ‘karami, hannun little dayaga ya d’anyi ja ya shafawa a hankali gudun karya tashesa daga baccin da yake yi , saida ya tabbatar maganin yayi masa yadda yakeso kafun ya ja masa Duvet dinsa sosai sabida yadda sanyin Ac ya karad’e ko ina . Ya jima zaune a inda little yake yana bin kyakkyawar innocent face dinsa da kallo , lokaci zuwa lokaci kuma yana lumshe idanuwansa da suka fara canza launi kad’an, idan mutum ya kallesa yaga yadda yake lumshe idanuwa sai ya dauka wani izzar ya’ke kara nunawa , amma gabaki d’aya sabida saramasan da kansa yake masa ne yake lumshesu, a wannan lokacin kamata yayi a ce yana kwance , amma ya hana kansa haka sabida little da yasan zai shigo d’akin. Yanxu ma saida ya tabbatar baccin little yayi nisa sosai kafun ya koma d’ayan side din ya kwanta.
Chapter 60 · 0% Book details