← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 146

Sashe 32

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wani irin kid’a ne me karfi yake tashi cikin wani d’aki meshegen kyau, kana ganin d’akin kasan d’akin macene sabida yadda aka ‘kawata d’akin da design pink colour , wani irin haske me kaloline yake haska d’akin, ga daddad’ar wa’kar da take tashi , lokaci zuwa lokaci zaka d’anji ihu kad’an na mace na tashi a cikin d’akin. Turo ‘kafar shiga cikin d’akin akai amma duk da haka wakar tashi take sosai ga kalolin da ya ‘kara ‘kawata d’akin sai faman haskawa yake ,wacce ta shigo wani d’an button ta danna take a wajan haske ya karad’e ko ina nacikin d’akin , lokaci d’aya fitulun da suke haska d’akin suka tsaya sai farar hasken da ya karad’e ko ina , a zuciye matashiyar budurwar da take jin wa’ka ta juyo cikin zafinrai � uban wanene zai shigo mun d’aki batare da izinina ba ?�, cewar matashiyar cikin daddad’an muryarta , kyakkyawar matashiyar budurwace da akalla a shekaru bazata haura 17years ba , Allah ya bata baiwar kyau duk da ba fara bace sosai Amma babu Wanda zai kalleta yace mata ‘baka dan skin dinta me shegen kyau ne da ko chocolate baza a kirata dashi ba sabida haskenta daya banbanta , d’ara d’aran idanuwanta masu d’auke da ba’kin kwalli ta zubawa matar da tashigo cikin d’akin , a zuciye ta ja dogon tsaki cikin d’an mitsitsin bakinta pink colour ,cikin kaskanci ta kalli matar da akallo d’aya da mutum zaiyi mata zaisan yar aiki ce � me nace miki? Uban me kike mun ma a d’aki da xaki shigo da ‘Kazantar jikinki cikin d’akina ?�, murmushi matar ta sakar mata ,duk da kasancewar ta mai aiki amma itama Allah ya bata baiwar kyau sihirtacce duk da shekarunta duk wanda ya ganta sai ya ‘kara kallanta sabida tsananin kyan da Allah ya bata , farace sosai duk da hijabin dake jikinta a gefe gefen fuskarta zaka ga wasu kwantattun gashi da ya ‘karawa fuskarta kyau � kiyi hakuri hajiya ce take nemanki�, dallah yimun shiru , cewar matashiyar budurwar tana katse ta � duk ranar dana ‘kara ganin kazamin kafarki cikin d’akina na lahira sai ya fiki jin dad’i haka Kawai bazaki zo ki shafa mun cuta ba irin taku ta talakawa , get out � ta daka mata tsawa ,wani guntun murmushi matar ta ‘kara saki tana sunkuyar da kai , kafun ta furta � kiyi hakuri ‘karamar hajiya � budurwar bata kuma cewa komai ba sai ‘kofar fita da ta nufa tana kakkare hancinta .
Tana fita ta ‘kara jan wani tsakin rai a ‘bace � gaskiya bazan iya ba , ko a ina momcy ta kwaso wannan ‘kazamar ,momcy tasan na tsani talaka bansan me yasa ta kwaso mun wannan kazamar ba , gabaki d’aya tazo ta cika mun d’aki da wari, haka kawai bazata zo ta shafamun warin jikin taba .� Tana kai ‘karshen zan centa ta d’akko turare ta feffesa a d’akin , jikinta sanye yake cikin ‘kananan kaya peach color da ya d’an kama jikinta , wani half cushion shoe ta saka na zaman gida ta fito daga cikin d’akin bayan rantsats tsiyar wayar ta iPhone 12 data data d’auko tana dannawa kunnanta sanye da wani pod na wa’ka . Cikin babban falon su da yaji kayan alatu ta nufa, ita kadai sai bin wakar da takeji take har ta ‘karasa ciki, tana shigowa matar da ta gani zauna kan manya manyan kujerun falon ta nufa da gudun ta duk da fuskar matar be fito ba , ta baya tayi hugging d’inta � momcy na�, murmushi ne ya Tashi me Sauti lokacin da matashiyar budurwar ta fuskanci matar da Hutu da dukiya ta zauna mata , ga jikinta da yake sanye dan manya super holland masu shegen tsad’a ga uban sarkar kwal da tayi ado Dashi amma duk da Haka tayi kyau ba kadan ba musamman yadda gold din yake kyalkyali. � my baby kin fito kenan ?� Dan tabe baki tayi a hankali ta furta � yes naji Ance kina kirana hope ba wani abun bane �, cewar budurwar da aka kira da baby � No baby bashi bane , I think am going out now , idan dadynki ya dawo kice masa na fita because bazan iya jira ya dawo ba kafun na fita , okay �, yanxu ma ta’be baki babyn tayi “kuma sabida wannan abun zaki kirani ina tsaka da jin wa’ka ta , and me yasa baki saka Eshaal ba sai ni zaki kira �, ko ajikin matar yadda baby tayi mata magana a gadarance cikin rashin kunya sai ma lallashinta da ta farayi � Haba baby na , kinsan banasan shabgata musamman idan ya had’a da daddynki shegiyarcan ta shiga ,kinsan ta da shegen munafinci�, remote baby ta d’auka � it’s okay naji, Amma ni yanxu yunwa nake ji, kisa ta dafa mun abinci dan banaso waccan ‘kazamar ta dunga mun girki,”wani dadi ne ya kama momcy baby sabida maganganun baby da ya faranta mata , � ko me kikeso haka za’ai my baby bari na kirata yanxu�, wani telephone momcy ta d’auka tare da dialing wasu number guda 3, ana d’aga wa cikin ta’be baki momcy ta furta � minti d’aya na baki ki zo ina nemanki a falo and idan kina tare da kazamar me aikinnan ki tabbata kin wanke jikinki karki sa mana cuta ni da baby�, tana kai ‘karshen zancenta ta kashe kiran. Ko minti biyu Ba’ayi ba , na soma jiyo takun ta kalli yana tun karo falon da su baby suke ciki, a hankali ta shigo cikin falourn , cikin daddad’an murya tayi sallama ,babu Wanda ya amsa mata tsakanin baby da momcy, itama budurwar da ta shigo bata damu da amsawar tasu ba dan ta saba da irin halinsu, farace itama sosai irin farin fulani ga tsantsan kyau da Allah ya bata iriin na fulani, jikinta sanye da doguwar ba’kar abaya tayi rolling da farin mayafi, yadda kanta yayi tudu zaka gane tana da gashin kai musamman yadda hakan ya nuna ta mayafinta , had’e rai momcy tayi lokacin dataga matashiyar budurwar itama baby wani dogon tsaki taja tana binta da kallon tsana , cike da gadara da izza tun kafin budurwar tayi magana Momcy ta dakatar da ita� bana bukatar jin komai daga bakinki, yanxu maza ki tashi kishiga kitchen ki dafawa baby abinda take san ci, and banazo ko wace kazama tayi mata aikin abincin saike �, girgiza kai kai Eshaal tayi tana bin baby dake hararar ta da kallo , � amma mom…� bata ‘kara sa zancen da take sanyi ba momcy ta d’auke face d’inta da mari ,� amma me ? Na saki abu kina cemun amma ? Amma d’in uwarki?zaki tsugunna ki tanbayeta me take so ko sai ranki ya ‘baci�, kwalla ce ta sakkowa Eshaal da Sauri ta goge ta tana durkusawar � me za’a dafa miki?�, cewar ta tana kallan baby, banza baby tayi mata tana latsa wayarta kamar bata san da wanzuwar wani ba a Wajan , sai da Eshaal ta maimaita kalmarta sau uku kafun baby ta d’ago fuska a ya mutse � ki tashi ki had’a mun rich friedrice da coslow sannan ki had’amun farfesun rago, nasa, da kuma na kaza , ko wanne daban daban ,sannan sai strawberry milkshake da banana milk shake da nake so,kallanta sosai Eshaal tayi jin abubuwan da baby ta lissafa Wanda tasan idan za’a kasheta ba lallaine taci abincin ba wahala kawai take san sakata � kin dai ji abunda ta lissafa, ki tashi ki bani waje � cewar momcy tana binta da wani kallan tsana, jiki a sanyaye Eshaal ta mi’ke jikinta duk a sanyaye hawayen da suke sakko mata ta share , yadda momcy da baby hatta dady da bayansa ra’barta suke mata abubuwa abun na tsaya mata a zuciya shiyasa kullum cikin adduar Allah yajikan ammeyta take ,duk lokacin da zatayi sallah sai tayi addua wa mahaifiyarta sabida ji take kamar bata da kowa a duniya, mutum d’aya ce take ‘ko’karin kwantar mata da hankali a duk lokacin da take cikin kunci ko tashiga maraicin uwa , AMMA ce kad’ai ke share mata hawayenta duk da yadda itama bata tsiraba Wajan baby da momcy kasancewarta yar aiki kuma a ‘kar’kashinsu. Tasan yanxu tana komawa Amma zatace zaka temaka mata , ita kuma batasan abunda zaisa Baby ta wulakanta ta shiyasa bata tsaya a ko ina ba sai kitchen , ita kadai sai tunanin ta inda zafa fara uban abincin da baby ta tula mata take .

🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

ABUJA
ADEMOLA ADETOKUMBO STREETS _!
Chapter 32 · 0% Book details