Sashe 55
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
da yawanci ba’a fiya zama a cikin layin ba , motar da Abla take ciki aka shigar cikin gidan sannan binta ta bawa yan matanta umarnin su shigar da Abla ciki, haka suka d’auketa kamar wata gawa sukai cikin gidan da ita , ko motsi Abla batayi kamar wata gawa. A waje kuwa wasu makudan kudi Binta shagala ta d’auko ta damkawa mutanan suna karba basu jira ba suka tashi motocinsu suka bar wajan, already tun acikin mota ta canza sim dinta, wata number takira kai tsaye bugu uku aka daga phone, cikin zakuwa ta furta � yanxu muka karaso cameeroon, zuwa gobe sai a turo motar da zata dauketa sabida idanuwan mutane� bansan me aka ce mata ba sai knodding kanta da ta sakeyi � toh ina jiran kudina kunsan bana wasa dashi�, Kitt ta kashe wayar tare da bin sahun su Abla. Cikin wani daki aka jefa Abla da ko motsi batayi suka kulleta, a hankali ta ware eyes dinta da Sukayi mugun ja tana bin kofar da kallo bayan idanuwanta batajın zata iya motsa jikinta, ta gefen side dinta har yanxu hawayene suke sakko mata, Shikenan baxata sake ganin Arwa ba? Sun kashe mata ita? A duniya babu wanda ya tava daukarta a matsayin ahalinta sai matar da zata iya kira mahaifiyarta ko ba koma a Wajanta ta taso sai Arwa da yanxu suka Rabata da ita , sun cuci rayuwarta, sun sa mata dafin da bazai taba goguwa ba a cikin ranta, me yayi saura? Me yayi saura yanxu ? Babu , sun ruguza mata komai na rayuwarta gabaki d’aya tsoro ko halin da zata shiga a yanxu ya fice daga ranta , zuciyarta ta bushe bata tsoron kome ze sake Samunta, tasan Allah yana sane da halin da suke ciki,shiyasan gaibu sannan ya fita sanin komai game da rayuwar ta , � La’ilaha illah Anta subhanaka inni kuntum minazzalimin, Ya Allah , ya Allah , wa’u fauwidhu amree ilallah , innallaha baseerun bil ibad, ya Allah� shine kadai abunda Abla take nanatawa cikin ranta . Tunda suka sata cikin dakin babu Wanda yazo ya duba halin da take ciki ko ya damu da sanin wani irin hali take ciki. Tayi kusan 1 hour kwance a yadda suka barta kafun cikin ikon Allah ta samu ta iya motsa hannayenta har tayi yunkurin tashi zaune , jirin da tafine ysa tayi saurin jingina jikinta da jikin bango, idanuwanta a bushe babu ko digon hawaye a kan fuskarta , zuciyarta ta bushe ta yadda ko hawayen batajin zata iya sai kukan zuci, kukan Zucin da Allah ne kadai yasan yadda take jin cikin ranta , haryanxu nunfashinta be gama saituwa ba musamman jirin da ta fiji dan ba karamin Shaka mata sukai ba har yanxu bata gama dawowa Daidai ba lokaci zuwa lokaci sai ta dunga zabura ko ta dunga dukan kanta kamar me kokarin zare wa . Karfe 5:30 pm aka bude kofar dakin da Abla take ciki, binta shagala ce ta shigo cikin wasu yan iskan kaya hannun ta dauke da ruwa da kuma bread , tun kafin ta karaso inda Abla take ta soma furta � da alama yunwa kikeji baby, ga bread nan da ruwa shiyafi dacewa dake amma karki damu ina samun biyan bukatata yau zansa a had’a miki babban liyafa yau kinji baby � ta karasa tana kokarin shafar fuskar Abla , duk da babu wani karfi a jikinta hakan be hana Abla shako wuyan binta shagala ba da har sai da ta saki kara da karfin gaske Abla ta damke gashin attached din da tayi , dukda yadda take jin ta ba kwari hakan ta daddage ta ware hannunta ta tsunkawa binta shagala mari me zafin gaske dama da hagu, ihu binta ta soma akan a zo a temaketa alba zata kashe ta , lokacin kuwa ba kowa a cikin gidan dan ta aikeso daga ita sai Abla da take kokarin Birkicewa gani take damace Allah ya bata sabida kashe mata Arwa da sukayi shiyasa ta daddage ta kara tsinkawa binta mari, sai faman kururuwa da neman agaji take akan Abla zata kashe ta ga zafin zamlar kırsan attachment d’inta da Alba tayi mata ga zafin Mari da Abla ta tsinka mata , dukda haka abla bata hakura ba ta daddage ta kwara kan binta a kasa sai ji kake kasssss sabida buguwar da yayi , iya jigatuwa binta ta jugatu duk da jikin da take dashi ta kasa kwatar kanta a hannun abla ita kanta bata san lokacin da kukan azaba ya kwace mata ba , ita kuka Abla kuka , � yadda kuka kashe ta Nima sai na kashe ku ba ku cancanci rayuwa ba , mugaye azzalumai Allah bazai barkuba � ido arufe Abla take ta faman surutai , binta kuwa da taji ba sarki sai Allah sai ta soma bawa Abla hakuri gabaki d’aya sai d’akin ya kacame da kukansu, lokacin da Abla ta kara gwara kan binta da bango a lokacin yan matan ta suka shigo d’akin da Sauri d’aya daga cikinsu ta nufi Abla gadan gadan, yadda zuciya ta zowa Abla har wuya bata san lokacin da ta sauke mata na ta kasan marin ba da iya karfinta da yasa sai da ta fadi, d’ayar ma Gadan gadan tabi kan Abla , itama Abla cafko kanta tayi ta buga da bango ga layin da take amma duk da haka bata kyalesu ba , d’aya bayan daya ta dunga bi tana tsunka musu mari, tun tanayin abu kamar a mafarki Abla sai ta koma kamar wata zararriya da bin hakki take marinsu, babu abunda suke sai faman bata hakuri da suke akan ta kyalesu amma ina Abla bata san ma sunayi ba burinta kawai ta nakasa yan iska.sai da abla ta faffasa musu baki kafun su samu su kwaci kansu hatta binta shagala sai janta yaranta sukai Sabida sumewar da tayi suna janta da kyar suna tsinewa Abla dan ba karamin jibguwa sukai ba.suna fita ta sulale a kasa ta kwanta, ba kuka take ba amma yadda kirjinta yake sama kamar zai fito sai ya baka tausayi dan hatta nunfashin dakyar take iya janyoshi.