Sashe 48
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Arwa ga Aneesa dan bazan iya saka ilham ba Sabida yar Dije kwalce kinsan kuma bala’inta itama cikakkiyar yar barikice kema kinsani�,murmushin gefen baki binta ta saki tana d’age ka fad’a� tun da baki Shirya ba ai shikenan �, zata tafi uwar karuwai tayi saurin dakatar da ita ganin ga samu ga rashi cikin saku wa ta furta � na amince amma taya za a fitar da ita ?yarinyar ba ‘karamin brain ne da ita ba �, ynxu kam binta kyal’kyale wa tayi da dariya kafun ta ciro wani farar powder a Leda tana nunawa uwar karuwai � duk kwakwalwarta da ilimin ta ai bata Kai wannan aiki ba ko?� Ta ‘kara tana d’aga coccaine din hannunta . Gabaki d’aya dariya sukai saki � shegiya binta baki da dama duk wani shu’umancina kin dameni, shiyasa nake san harika da irin ku �, cikin yanga binta take d’ad’d’age fuska da hura gajeren hanci ita a dole ana kod’ata . ********** ************ KANO 1:30pm kid’ane yake tashi a falon sosai sabida volume din murya da Baby ta ware sosai sai kace gidan shed’anu ga wani irin ‘kara da ya karad’e ko ina , baby ko ajikinta ko d’an kwali babu akanta sai gashin kanta da ta tufke jikinta sanye da ‘kananan kaya Riga da wando ga head phone d’inta da ta saka a kunne amma duk da haka sabida neman rigima da Eshaal ta ‘kara waye volume , ko mintuna 5 bata ‘kara ba tana rawa Eshaal ta shigo falourn rai a ‘bace , magana take wa baby amma kamar ma bata san tanayi ba shiyasa taji haushi ta kashe kid’an , azuciye baby ta tsaya daga rawar da take tana bin Eshaal da shigo falourn sanye da hijab da alama sallah zatayi ko take shirin yi � uban wa yace ki kashe mun kid’a ? Ke wace irin ballagazace wai ? Nace ki dena shiga rayuwa ta amma sabida maita sai kinshiga, karkiga mun had’a dad dake ki fita idona �, cewar baby, guntun tsaki Eshaal ta saki � ke kullum baby wai sai kin nemo abun rigima? Karki manta sallah fa akeyi , be kamata ai kisaka kid’a lokacin sallah ba , ko ke bana Tuna’nın kinyi sallahr, sannan idan dole sai kinji wa’kar sai ki kunnashi a d’akin ki mana ?�, a kufule baby ta kalleta � idan kece kika kar’barmun sallar karki karba , da nayi sallar da banyi ba ai ba kabarin mu d’aya ba , stupid kawai, wareey daga nan wajan �, ta karasa tana d’aukar remote , fusge remote din Eshaal tayi � wallahi bazaki kunna ba , kinsamu ana bin ki ta laluma amma ke sam bakısan annabi ya kafuva�, itama hannu baby ta saka zata karbi remote din Eshaal ta hanata, lokaci d’aya suka soma kokawa ran baby ba ‘karamun ‘baci yayi ba , shiyasa ta daddage ta gantsarawa Eshaal cizo a wuya da yasata sakin gigitaccen kara dan mugun cizo baby ta kai mata , karar da yasa momcy da ke waya a d’aki sai da taji amma ko motsawa batayi ba balantana ta fito ta duba abunda ke faruwa ,AMMA kuwa lokacin da Eshaal tasaki ‘karar tana cikin band’aki tana wanka, itama azuciye Eshaal ta cijeta da yafi wannan baby tayi mata , itama ‘karar ta saki dan sosai taji zafin cizan, a wannan karan karar baby da momcy ta jine yasa ta kashe wayar tare da barin dakinta Daidai lokacin da baby ta d’auki wani abun decoration ta kwalawa Eshaal , lokaci d’aya goshinta ya soma zubar da Jini , zata Shako baby momy ta shigo falon , cikin kukan shagwaba baby ta nuna mata cizan da Eshaal tayi mata , itama rai a’bace ta janyo wata bakar waya me kaurin gaske ko la a kari da fasa mata goshi da baby tayi batayi ba ta soma jibgar Eshaal da ba’kar wayar nan abunda da farar fata , jikinta duk yayi ja alamar duka, da Sauri Amma ta fito ko kaya bata saka ba sai dogon hijab data zura , yadda taga momy nan dukan eshaal ne yasa tashiga bata hakuri amma kamar zugata take , duk yadda Amma tayi abun yaci tura dole ta hakura musamman wanka mata mari da momy tayi , itama baby tsaki ta ja � wallahi na tsani munafurci, wannan mata dai muna fukace ke , inbanda munafurci uban me ya fito dake? Dama har dake aka had’a aka zanen, Mtsww � taja tsaki tare da daukar tanfatsetsiyar wayarta tai wuce warta daki, itama momy tana gama dukanta tai wuce warta ranta fess, da te makan Amma Eshaal ta koma d’aki sai kuka take , wani man zafi Amma ta dakko cike da tausayawa ta shafa mata kafun ta bar mata sauran, sai faman rarrashinta take tun tana kuka har ta dawo a jiyar zuciya a haka bacci ya d’auketa rai a’bace .