Sashe 20
Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A zaune ya tarar da prince lokacin uncle ya nufi bedroom d’insa � ina little ?� Cewar bobo,’kofar da ya nufa prince ya nuna masa � Tun d’azu yake nemanka har yayi fushi beci abunci ba “gashin kansa bobo ya shafa ,� and you kunci abinci?d’an sosa kansa prince yayi , bobo na ganin haka ya juya ya nufi dinning area , cikin wani unique plate yayi serving food aciki bayan ya rufe ya nufi ‘kofar da little ya shiga . Nan ma wata doguwar tafiya ce me d’auke da white tiles kafun ya karaso wasu dogayan ‘kofuna guda 5 dake Jere a wajan, Door d’in karshe ya nufa , yana bud’e door d’in na furta wow,sosai Wajan ya had’u gwanin ban sha’awa ba komai ne a wajan ba sai manya manyan Glass Tower masu shegen kyau kala kala , ga wasu irin colour fishes da suke yawo a cikin ko wana tower glass, babban glass aquarium d’in da yake farko wasu Mitsi mitsin Golden fish ne a ciki yan kanana kanana kalar golden da yawa aciki , daga cikin glass d’in har da wani grass carfet a ciki da wani babban dotse me ‘kofofi, sosai glass tower din yayi kyau musamman yadda golden fishes din suke ta motsi cikin ruwa. Daka gefen hagunsa ma wani babban Glass tower ne amma be kai girman na farko ba sabida babban shape d’in circle ne dashi daga inda kake kana iya ganin wasu irin kala kalan kifaye da suka sha banban da na farkon, suma cikinsu har da wasu design din shukoki da ‘kananan dutsuna suma kala kala , shima ‘kananan fishes ne a ciki kala hudu, Orfe fish, Golden Rudd, Red shiners , koi carp fish , ko wan kifi a ciki da kalar jikinsa suma sai faman mosti suke a ciki, haka bobo ya dunga ratsa manyan glass tower din fishes din har yazo kan Wanda yafi ko wanne had’uwa gabaki d’aya jikin bangon wajan glass tower ne cike da Rosy Red Minnows , wasu irin kifayene suma da farko idan ka kallesu zaka d’auka jikinsu ne me colours din sai ka matso kusa da glass din zaka ga ainahin transparent glass colour ne jikinsu sai kalolin da ke cikin fatar su, gabaki d’aya wajan gwanin ban sha’awa , ko ina ka wai ga zaka fishes na yawo cikin ruwa. ‘Karasa shigowa ciki bobo yayi kan wani unique table me zaman mutum hud’u ya zauna tare da ajje plates d’in hannunsa , � come out �, cewar bobo , daka wani jikin bayan glass tower Little ya Fito bayan ya gama barbad’a musu wasu powder me kama da abinci ganin yadda suke rububin zuwa wajan , wani medium sink bobo ya nuna masa da hannu, shima little Wajan ya ‘karasa tare da wanke hannunsa da wani hand wash me shegen ‘kamshi , plate d’in abinci bobo ya d’auko tare da d’aukar spoon , kamar wani ‘karamin yaro ya d’ebo abincin ya kai bakin Little dake kunbure kunbure , kadan ya bud’e bakin bobo ya tura masa French Toast d’in dake cikin fork d’insa , shima little d’aya fork d’in ya dauka tare da knife ya yanka waffles d’in gefe ya kai bakin bobo , ba musu ya bud’e masa bakinshima ya sa masa waffles d’in babu Wanda yayi magana har saida suka kammala cin breakfast d’in nasu � Now kaganni ai ko? Stop been so stubborn, naje na d’anyi wani aikine, be a good boy inna fita na dawo na tarar kayi wani laifi this time around zan hukunta ka , ok?�, curly hair d’inshi da ya sha gara little ya girgiza masa � yaya bobo , I have something for you, wait for me kaji?�, be jira cin amsar bobo ba ya fita daga wajan a guje , girgiza kai bobo yayi, a fili ya furta � Adil will always be Adil �, ko mintuna biyar be yiba ya dawo sai nishi yake, p-cap d’in ya fara mi’kawa bobo da ya zaro ido kamar ya ga wani babban gift har da saka wa a kansa , little box d’in da little ya ‘boye ya mi’kawa bobo,kallansa bobo yayi � for me ?�, murmushi Adil ya saki lokacin da bobo ya bud’e box d’in , with much surprise akan fuskarsa ya kalli unique design diamond bracelet d’in dake jikin ‘karamin box , kafun ya ‘kara maida kallansa kan Littel � for me ?� Curly hair dinsa little ya ‘kara jijjiga masa , har yanxu da mamaki a kan fuskar bobo ya ciro bracelet d’in da sai faman shinning yake , sai mutum ya kula sosai zaisan da suna a jiki, hugging d’insa bobo yayi � finally little ya zama big boy yanxu �, dariyar da ta ‘karawa little kyau ya saki da har saida dimples dinsa ya lotsa ,� let me help you �, cewar little , mikawa masa bracelet d’in bobo yayi da kansa ya saka masa , a tare suka ri’ke hannun juna kamar wasu friend suka fito daga cikin � THE DREAMER FISH ROOM �. Lokacin da Suka fito parlourn prince na zaune shida uncle ,kallansu uncle yayi kafin ya harari little � yanxu kaga yaya bobo d’in aiko?� Da Sauri little ya ‘karasa Wajan uncle din tare da hugging d’insa , � my uncle I missed you �, ture shi daga jikinsa uncle yayi � daga baya kenan� gabaki d’ayansu babu Wanda beyi dariya ba , a Gogon diamond d’inshi bobo ya kallan ganin almost 11 yasa ya nufi elevator , shaf shaf ya nufi part d’insa , ba zauna a ciki ba direct toilet ya nufa almost 2 minutes ya fito cikin wata ash bathrub har ‘kasa , door cikin gefen toilet d’in ya nufa almost 10 minutes kafun gabaki d’aya part d’in ya bad’e da kamshin ROJA , tun kafun ya futo sassanyan kamshin turaran Roja ya bad’e ko ina na cikin d’akin. Door d’in kofar da aka bud’ene yasa na mayar da hankali na kansa , fatabarakallahu Ah sanin kali’kin, tubarkallah Masha Allah, sanye bobo yake cikin wasu irin da kakken uniform d’in sojoji black colour , daga gefe gefen shoulder d’insa wasu golden stars ne guda hudu sai faman shining suke kwanin burgewa, daga jikin rigarsa a ‘bangaran hagu wasu abubuwane masu kaloli a wajan daga ‘kasan sa kuma wasu tanbura ne a wajan da bansan ko na menene ba. Daga side d’in damansa kuma wani tag ne a Wajan ‘kasan sa da harafin General A.M.A, a jiki, sosai uniform d’in yayi amsa kyau musamman damtsen hannunsa da ke sanye wani barge, daga gefe gefe wandan jikinsa ma wasu dogayan golden d’in line ne a both side d’in , ba ‘karamin haduwa yayi ba na bugawa a jarida , bai saka hular ba , sai curly hair d’insa da yake askewa fitowa sosai musamman gyara da ta samu, ra tsats tsen diamond watches d’insa ya kalla kafun ya Fito daga part d’insa cikin takun jarumta, yanxu ma ta elevator ya sakko, su little na ganinsa shi da prince , cikin sauri suke mi’ke suka sara masa ,dariyar abunda sukai uncle yayi kafin ya mayar da kallansa kan bobo da babu fara’a a kan fuskarsa,Kai tsaye inda suke bobo ya nufa � take care ! Yanxu ma kamar wasu sojoji suke amsa da yes sir , kanshi kawai ya Jinjina musu kafun ya nufi kofar futa . Suna ganin ya fita kowannansu ya zube kan kujera yana sauke a jiyar zuciya . A waje kuwa , wasu manyan lamborghini veneno masu shegen kyau gabaki d’aya tinted cars ne black colour, ga karatan sojoji ko wannansu cikin uniform d’insa, bobo na Fito wa cikin wani irin salo suka sara masa� salute sir �, tare da ‘kamewa, shima right hand d’insa yasa yayi salute , kafin cikin unique way Robert ya bud’e masa door , yana shiga ba’a bata lokaci ba jerun motocin da a’kalla zasu kai goma suka fita daga cikin gidan , Robert ne ya furta � sir �, dakatar dashi bobo yayi ta hanyar furta � BARRACK�.
✨✨✨✨✨✨
NIGERIA
ABUJA STATE _!
✨✨✨✨✨✨
NIGERIA
ABUJA STATE _!