← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 146

Sashe 89

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**** Ana idar da sallar magrib ko zaba little beyi ba yaje ya fito da Abla itama sanye take cikin wata doguwar riga maroon colour da ya wuce kwiwar kafarta kadan sai wani white wando da ta saka , sai wani farin shoe da little ya dakko mata , tayi rolling da mayafin kayan maroon , duk da ba kwalliya tayi ba sosai kayan sukayi mata kyau, gudun ma kar uncle ya dakatar dasu ko part d’insa basu shiga ba , yaya bobo ma yana part d’insa , suna fitowa da motoci hud’u zasu tafi , da’kyar Abla take tafiya sabida ganin sojojin gidan amma yau gabaki d’aya wad’an da zasu fita dasu suit ne a jikinsu shiyasa taji sau’kin Abun. Tunda Suka soma tafiya take kalle kalle musamman yadda ko ina yake da haske kamar ba dare ba , ko wana barin fata yana aikin gabansa gwanin ban sha’awa, sosai sukayi tafiya me Nisan gaske na kusan mintuna 15 kafin su ‘karaso Nora Gardner , babban shagone na mata da ake siyar da sababbun kayan sawa na mata designers masu shegen kyau da tsana , shiyasa wajan ya zama private bakowane yake iya siyan kayan wajan ba , face mask prince da little suka saka , kafin su fito tare da Abla da sai faman kalle kalle take , gabaki d’aya jikinta sai yayi sanyi duk da bata san dalilin zuwan nasu ba , Robert ne kawai ya bisu gabaki d’aya ragowar suka tsaya a ba’kin Wajan suna jiran fitowarsu, daga prince sai Little da Abla suka shiga Wajan sai kuma Robert da shima ya dakata suka shiga cikin wajan , da murna wata farar baturiya ta nufosu musamman ganin Abla , ita atunaninta Abla yar ganin ce Sabida yadda take da hasken fata me kyau , cikin French Little ya nuna Abla Sabida kada ta fuskanci me yake cewane yasa yayi anfani da French � madam ga sister na, kayan sawan da zasuyi mata kyau zaki d’auko mata da yawa amma ba Wanda zasu dameta ba , kamar na jikinta sai kuma English wears suma masu kyau , infact duk abunda xai yi mata kyau ki tafi da ita kizabar mata , bag , shoe , designers everything for a lady , ki d’auko mata su masu kyau� farar baturiyar nan tana jin haka har wani zaro ido take ganin lokaci d’aya za’ayi musu siyayya me yawan gaske, gabaki d’aya ta kasa magana, tana tsayan wata matar ta fito daga wani ‘kofa da Alama Itace me wajan , cikin Sauri ma’ai kaciyar nan ta je ta sanar mata , itama da Sauri ta ‘karaso Inda suke har ta washe musu ha’kora , da kanta ta ja Ablan dan taje Itace zata nemo mata abunda ya dace ganin lokaci d’aya zasuyi uban ciniki, kan wasu chairs masu shegen kyau su little suka zauna , Wajan sai ya kasance kamar Vip, ga me coffee da take tsaye idan suna bu’katar wani abun. Tunda Suka hau sama madam d’innan ta nufi VIP set da Abla , wasu irin shegen kaya shegen kyau ta dunga za’bar wa Abla tunda basu fad’i adadin kayan ba , shiyasa duk Wanda taga zai yi wa Abla kyau shi take d’auko mata ko ‘kirgawa batayi , Abla sai binta da ido take dan ita har yanxu bata gane me Sukazo yi ba , bayan dogayen designers din da ta d’ibarmata sai ta dawo d’auko mata ‘kananan kaya masu kyau, suna ajjesa, daga nan ‘bangaran inners suka nufa , kallo d’aya tayiwa Abla ta dunga fito mata da pants da bras masu shegen kyau gasu da yawan gaske , ita Abla har kunya ma abun ya bata ganin yadda take kallanta , daga nan ‘bangaran designers shoes and bag suka nufa , nan masu tsad’an ta dakko mata fashions , kuma yawanci hill shoes ta d’ebowa Abla sai shoes da ta saka mata , ga veils da ta d’auko mata , hatta fashion chains na mata da sar’ka da abun hannu gabaki d’aya sai da ta d’akko wa Abla , ba ‘karamin kaya ta d’ebowa Abla ba , sannan ta saka aka sassa ka musu a cikin jaka suka sakko Sabida gabaki d’aya tayi calculation d’in kud’in kayayyakin, ba ‘karamun ma’kudan kud’ad’e aka aka kashe wa kayan nan ba , suna sakkowa Aka fad’awa su little kud’i, Black card din Big Boss kawai ya saka da pin d’insa , suka zare ma’kudan kudaden da mutum sai ya girgiza amma da alama tsakanin prince da little babu Wanda ya damu da adadın kud’in. Kallanta matar tayi cikin turanci ta furt � gaskiya ked’in kyakkyawa ce , and kina da sa’a sabida kayan da yan uwanki suka siyo miki� ‘kura mata idanuwa Abla tayi kamar tana so ta gane me matar take so tace , ido d’aya little ya kashe mata suprice, lokacin da ake fitar da kayan , bakin Abla har rawa yake ta kasa magana sai nuna kayan da take da hannu , idanuwanta har sun kawo ‘kwalla , da Sauri little yaja hannunta suka fita � Haba don’t cry sister , just kayan sawar kine� cikin Sauri Abla ta fara girgiza masa kyau , gashi ta kasa bud’e baki tayi magana sai rawa da bakinta yake , lokaci d’aya kawai ta fashe da wani irin kuka , kuka take babu ‘ka’k’kautawa ganin abubuwan da suka siyo mata , abunda wani mahalu’ki be ta’ba yi mata ba a duniya , wai yau Itace ake nuna wa soyayya? Kamar a mafarki daman zata iya yin farin ciki a rayuwarta ? � abunda kawai take iya tunani kenan , kuka sosai take bana wasa ba , so take ta bud’i baki tayi magana amma ta kasa , harshenta yayi mata nauyi , bakinta bai isa ya nuna d’unbin godiyar da ke zuciyar ta ba , soyayyar su mara misaltuwane a cikin zuciyarta, wani irin soyayyarsu da kimarsune yake ratsa ko wana bargo na cikin zuciyarta , ganin ta’ki yin shirin ne kamar zai yi kuka shima ya furta � ki dena kuka mana , kin manta ke sister din muce ko so kike Nima nayi kuka ?� Da Sauri ta girgiza masa kai , ta bud’e baki zatayi musu Godiya amma ta kasa bazata iya ba, Allah ne kad’ai zai iya yi musu abunda sukayi mata , shi kad’aine zai iya saka musu, da kyar suka samu suka lallasheta tayi shiru , ko godiyar da take ‘ko’karin yi musu sun’ki bata damar hakan , gabaki d’aya basa suba time shiyasa har ‘karfe 8pm na dare ya wuce basu sani ba , gashi gabaki d’aya sun manta da zancan kaiwa simba Abinci. Har zasu dawo gida prince yasa suka ‘kara mi’ka babban mall d’in Hudson yards , shima wani irin babban waje ne na siyayya , Abla gabaki d’aya kasa d’ago kai ta kalli wajan tayi Sabida har wani zazza’bi zazzabi take ji kamar zai kamata sabida kukan da tayi ga idanuwanta da suka d’an kunbura , bayan sunyi parking Daidai zasu shiga cikin mall d’in Abla tayi karo da wata , ta jiyo zata bata ha’kuri matashiyar budurwar ta d’aga hannu zata mareta , cikin Sauri Little ya hankad’ata tayi baya saura kad’an ta fad’i kasa ma , ba kowa bace face Alice da tafito siyayya , batare da little ya kalli fuskarta ba yaja hannun Abla suka soma tafiya , wani din kallo suka dunga jefa wa tsakaninsu Abla da Alice , a karan farko wani irin kallan tsana ne sukayi wa junansu, Alice kuwa mamakin yadda aka turetane yasa ta kasa tashi ga manyan security da tagani tare dasu , ita kuma bata san a ganeta shiyasa ko security bata yadda sun biyota ba, amma a kallo na farko da tayi wa Abla taji wani irin tsanar ta ya shigar mata zuciya , ga wani ‘bacin rai da bugun zuciya da ta samu sabida tsananin kyan Abla da take hango wa , ta sani ko kusa bata da irin kyan yarinyar shiyasa tsanar Abla ya ‘kar shigar mata zuciya . Abla ma a kallo d’aya da tayi wa Alice taji wani tsanarta ya shigar mata zuciya dukda bata san dalili ba , a haka suka shiga cikin babban mall d’in, ‘ban garan kayan siyayya, dukda sunsan suna da su a gida haka little da prince suka dunga d’ibar kayan ciye ciye duk Sabida Abla suka siyowa kuma ga manyan ice cream suma da suka d’auko mata , chocolate , sweet da wasu abubuwan ma da bazasu lissafu ba , nan ma ba’karamun siyayya sukai mata ba dukda basu fito sunce ita suka siyowa ba Sabida kartayi musu kuka , ita dai binsu kawai take abaya , tana kallan yadda suke d’aukar Abu kamar basu san zafin kud’in ba ( Nace Abla toh daman taya zasu sani tunda da kudin yaya big boss suke ta anfani 👀🤭😹). Sai da Suka shiga cikin mota sannan prince ya d’auko wayansa , pass 9 , shine abunda ya nuna masa , besan lokacin da ya saki wani salatiba, a rud’e ya nunawa little time , shima lokaci d’aya ya saki salati , Abla kuwa gabaki d’aya bata fahimta ba shiyasa ta zuba musu manyan eyes d’inta da suke shinning sabida kukan da tayi, cikin Sauri little yace wa su Robert su ‘kara gudu , sai addua yake Allah yasa yaya big boss be dawo ba, har suka ‘karas adduar da Suke yi kenan, ana shigowa cikin gidan zuciyoyinsu tayi wani irin mugun harbawa a tare sabida ganin Anthony, tunda Suka ga Anthony da Victor to tabbas big boss ya dawo gida , ita kuma Abla bata san dalili ba , kawai taji wani irin bugawa da ‘kirjinta yayi kamar wacce tayi wani babban laifi, sai a lokacin kuma abincin da akace zata Tunga kaiwa ya fad’o mata arai, wani irin tsorone ya kamata, gabaki d’aya kamar Marasa gaskiya suka nufi cikin gidan su Robert kuma tuni sun shigar musu da kayayyanki siyayyar da sukayi me matu’kar yawa, suna shiga har wani jan Burki suke a tare ganin Big Boss zaune kan kujera yayi crossing legs d’insa da alama ya jima da dawowa Sabida farin wandan da yake jikinsa iya kwiwa sai faman shirt shara shara da take jikinsa , gashin kansa
Chapter 89 · 0% Book details