← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 146

Sashe 112

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

S____31💞
Hugging d’insa Bobo yayi sosai a jikinsa yana shafa bayansa � it’s okay ! Bar kukan haka , yanxu Dr zata ‘karaso ,� tun be ‘karasaba ba Dr din da Abla ta zauna a Wajan ta ta ‘karaso hannun ta d’auke da wani ‘karamin kit � Kagama ta ‘karaso let’s show her the room� gyad’a masa kai little yayi amma haryanxu bai dai na kukan ba , sai da suka rakata har ‘kofar d’akin Abla amma basu shiga ba suka barta ita kad’ai. Kama hannunsa bobo yayi zuwa bedroom d’insu , yana shiga yaga fitila a kashe, yana kunna wa kuma ya tarar da Prince ya kwanta ya lullu’be jikinsa , idan mutum be lura sosai ba sai ya d’auka bacci yake , shima little abunda yayi kenan, bed d’insa ya hau ya kwanta tare da lumshe idanuwansa , sosai face d’insa tayi fiyau babu murmushi ko fara’a a kanta , bakamar little da kowa ya sanshi me murmushi da dariya ba. Kallan direction d’insa Bobo yayi kafun ya mayar da kallansa kan prince , bece musu komai ba ya kashe musu light ya bar dum kamar kullum, shima ransa ba dad’i gabaki d’aya ko magana bayasan yi Sabida yadda ransa yake a Jagule.
Doctor tana shiga tamakon gaggawa ta bawa Abla fahimtar abunda ya sumar da ita , cikin ‘kan’kanin lokaci ta farka Sabida allurar da akai mata, da kyar take iya motsa jikinta sabida wani irin kasala da ya kamata , wasu drugs Dr ta bata da bayanın yadda zatayi anfani dasu, face d’inta tayi fiyau kamar ba ita ba , babu abunda bakinta ya iya furtawa sai � thank you � daga nan bata kuma cewa komai ba, ganin Dr d’in ta fita daga d’akın yasa taje ta ‘kara tsaftace jikinta tare da yin alwalar bacci ( mata please idan zamu kwanta mudunga yin alwala sabida ita Alwala babban tsarice ga dukkan Wanda yaso nufarmu da sharri , Mata muna sakaci lokacin Al’ada , lokacin da mace ya kamata ta ru’ke addua sosai musamman yin alwala yana da babban mahimmanci lokacin Al’ada , duk mutumin da yayi ‘ko’karin nufinka da sharri sai kaga Allah ya kubutar da kai ta inda bakayi zato ba , please mata mu lura ), tana fitowa Bed d’inta kawai ta hau sabida lokaci d’aya taji gabaki d’aya cikin nata ya dena yi mata ciwo gabaki d’aya , bata d’auki tsawan lokaci ba bacci me nauyi ya d’auketa sabida allurar da Dr tayi mata har da ta saka baccin tayi mata .
Dr tana fitowa ta had’u da bobo, fuskarta da murmushi ta furta � you don’t have to worry , ba wani abu bane babba , nayi mata allura nasan anymoment yanxu tayi bacci , and she need to rest for atleast good 2 days �, kansa kawai bobo ya jinjina mata � sure ! Thank you !”daga nan ya wuce part d’insa , itama ta fita Robert ya rakata har waje .

******* Big Boss
Ransa a’bace ya wuce cikin bedroom d’insa Daidai gaban mirror ya tsaya, kan sa a d’an sun kunye , gefe da gefe na gashin kansa sun rurrufe masa fuska, ransa yayi mugun ‘baci shiyasa ya kaiwa glass naushi, cikin ‘kan’kanin lokaci hannunsa ya fashe Jini bana wasa ba ya fara fito masa , amma ko kad’an be damu da hakan ba , sosai ransa yake ta farfasa, dukda yadda jine ke fita daga cikin hannunsa hakan besa ya tsaya kula dashi ba , a hankali ya bud’e eyes d’insa musamman tuno marin da yayiwa little , abunda be ta’ba faruwa ba a tsakaninsu , d’aya daga cikin drawers din ya bud’e tare da d’auko wani allura , Daidai jijiyar hannunsa ya saka wa allurar kafin ya lumshe eyes d’insa yana zama kan sofa, ga hannunsa da haryanxu jinin da yake zuba bai tsaya ba . � Nasan ko me kakeyi kana yin sane Sabida su , but please you have to calm down, nasan basu cancanci ku yafe musu ba , but atleast lokaci yayi yanxu, 22years isn’t a joke”cewar uncle da yake shigowa d’akin , bud’e rinannun idanuwansa Big Boss yayi ya zubawa best uncle d’insa , � I hate it when someone talk about so called them ! I hate it� yadda ya fad’a a gajarce da ‘bacin rai mutum zai san har cikin zuciyarsa a ‘bace yake , murmushi uncle yayi masa “Nasan ranka a’bace yake har yanxu, amma ya kamata kasani, ko ba dan kai ba , atleast for Little�, Kyawawan lips dinsa na ‘kasa Big boss ya d’an tauna da har saida lips d’insa suka fashe, be kuma tanka wa uncle ba sai ma lumshe eyes dinsa da yayi , Sabida yadda yaji kansa na sara masa. Murmushi uncle ya saki kad’an yasan halin Big Boss sarai kamar yunwar cikinsa , ya san yanxu yana ‘kara magana amaimakon abun yayi sauki sai ma worst da zai ‘karayi, mai da kallansa yayi kan hannunsa da ya nuna shedar fashewa Sabida glass din da ya daka me shegen kwari ne , cikin tausasa murya uncle ya furta � take care of your self, good night � da haka ya juya ya bad’ar d’akın ba tare da damuwa da rashin tankawa da Big boss be yi ba . A Daidai ‘kofar falonsa na farko suka kusan cin karo da Bobo yana kallansa ya jinjina masa kai ganin shima face d’in bobo babu wani fara’a akanta sosai , Duk cikin su Big boss ya fi kowannansu zuciya dan da gasken gasken ya ci sunan masu sunansa , shima uncle be tanka masa ba ya furta � wannan face din da ka ‘ki saki ba magana zan yi maka ba , take care of your brother , good night�, a hankali Bobo ya furta � Good night uncle � daga haka Bobo ya nufi cikin bedroom d’in Big Boss shi kuma uncle ya bar part d’in.
Bakinsa d’auke da sallama ya tura ‘kofar d’akın, a tsaye ya tarar da Big boss hannunsa d’aya ya d’anyi dressing dinsa , yana ganin Bobo ya d’an ta’be baki zai cike cikin dressing room d’insa , cikin tsokana Bobo ya furta � yanxu tafiy zakayi kabarni ? Bayan kasan wajan ka nazo ?� Batare da ya kallesa ba Big Boss ya furta � Get lost ! You headache � ynxu kam murmushi Bobo yayi � Ni ne ma ciwan kan ? Nifa lallashin ka nazo yi , haka Kawai ka tsinkawa little d’ina mari , ka saka bawan Allah cikin damuwa…� dakatar Dashi Big boss yayi ta hanyar furta � kaima baka fi ‘karfin marin ba ai� yana kai ‘karshen zancansa ya shine dressing room d’insa . ‘Dan girgiza kansa Bobo yayi cikin d’aga murya sosai yadda Big Boss zai jisa ya furta � Babu Inda zani, yau a cikin d’akin nan zan kwana ..”be kulle bakinsa ba yaji kamar ana ta’ba kofar alamar xai bud’e , cikin Sauri Bobo ya gudu yana murmushi ‘kasa ‘kasa .

****2:00am Big Boss ne zaune kan wasu kujeru masu shegen kyau yadda yanayin Wajan yake mutum zai fi kiran sa da Wajan sha’katawa dan sosai yanayin tsarin Wajan ya had’u musamman yadda yake d’auke da wasu kujeru guda masu shegen kyau, system ce kawai akan medium glass table d’in gabansa , sai ra tsats tsiyar wayar sa da ke gefen side d’insa . Cikin kwarewa Big boss yake operating d’in ta , yadda ya zuba mata narkakkun eyes dinsa sai ya ‘kara yiwa fuskarshi kyau, musamman yadda hasken system d’in ya ‘kara hasko da tsananin kyan sa . Jikinsa sanye yake cikin wasu fararan kayan pajamas masu shegen kyau da santsi, ga ba’kin lallausan gashin kansa da ya nannad’e a bayansa.
Shigowar Bobo wajan ne yasa ya d’an d’ago da idanuwansa , sau d’aya ya kallesa ya mayar da kallansa kan system d’in gabansa . Shima Bobo ‘karasa shigowa yayi hannunsa d’auke da 2 cups of coffee sai faman turiri suke, a kusa da system d’in Big boss ya ajje d’aya , d’ayan kuma ya ri’ke a hannunsa , babu Wanda ya tanka a cikin su sai coffee d’insu da suke sha , sai da bobo ya tabbatar Big
boss ya gama aikin nasa sannan ya zauna a kujerar da take facing d’in Big Boss , � we’re sorry! A dena fushi da mu� sai kuma ya d’an saki wani murmushi kad’an saman la’b’ban sa � wannan ne karo na farko da naga little yana san abu da gasken gasken with all his heart, yasan duk abunda yake so ko be fad’a ba za kayi masa , but this time around he just need your support, we all know his conditions, ya kwanta cikin damuwa , you too , yarinyar da yake matu’kar d’auka sister dinsa , I, uncle , prince , banasan ganin ku haka , it’s hurt me so mentally �. Yana kai ‘Karshen maganarsa ya kalli Big Boss da yake danna wayansa hankali kwance kamar ba dashi Bobo yake magana ba , A hankali ya mi’ke cikin cool voice d’insa ya furta � Good night � daga haka be kuma cewa komai ba ya bar part d’in Big Boss gabaki d’aya , sai a lokacin Big boss ya d’an d’ago da eyes dinsa ya kalli hanyar da Bobo ya fita kafin ya ‘kara mayar da kallansa kan wayarsa da yake operating, ya d’au kusan 1 hour tukunna ya tashi daga kan kujerar da yake , ya nufi cikin master room d’insa . Bashi ya Fito ba sai Wajan around 3:20am, tundaga kan part d’in uncle , Bobo , da su little gabaki d’aya saida ya duba lapiyar su musamman yadda yaga little ya kwanta a takure , ga guntun hawayen da ya bushe akan face d’insa , be jima ba ya nufi part d’insa sabida yadda kansa yake sara masa.
Chapter 112 · 0% Book details