← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 146

Sashe 137

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

**** MONDAY
Yau ya kasan ce Monday , da wuri Abla ta shirya cikin uniform d’inta, tana fitowa gabaki d’aya su Little sun tanadar mata breakfast d’inta , ita kad’ai taci banda su sannan suka had’a mata wani box shine na kayan za’ki, yau basu bita makarantar ba , tana fitowa madam sarah ta kar’bi school bag d’inta , Abla zata hanata Madam sarah tayi saurin bud’e mata ‘kofa , tazo zata karfi chocolate box d’in hannunta Abla tayi saurin dakatar da ita , a haka motocin su suka bar cikin gidan , cikin sa’a kuwa bata had’u da Big Boss ba , hakan ba karamun dad’i yayi mata ba kuwa.
Tana shiga school ta tarar dasu Fanan a class duk da yawanci kad’an ne wanda suke ciki. Hugging d’in juna sukai gabaki d’aya su ukun, kafun Abla ta samu seat ta zauna , � kin kusa fara cin dukan makara fa � murmushi Abla ta sakar wa fanan da tayi maganar � amma kece zaki yi dukan ko ?� Ido d’aya Fanan ta kashe mata kawai , � Ni kuma gaskiya sai dai naciki tara babu wani duka � , hannu Abla ta mi’ka mata � oya give me five � itama Eshaal ta d’ago hannun ta da niyar su tafa sai taga Abla tayi saurin janye hannun ta tana dariya , d’an hararar ta Eshaal tayi � wallahi Allah dai ya hana mugunta � wani gwalan Abla tayi mata tana furta � Oho dai � . Baby ce ta shigo cikin class d’in yadda take so calm yau sai ta bawa kowa mamaki , ga face d’in ta da mutum ya kalla yasan tana cikin damuwa, a seat d’in su ta zauna tare da kifa kanta , kallan Eshaal , Fanan tayi � Me aka yiwa Baby ? Tun ran friday naga sauyi a face d’in ta gabaki d’aya batasan yiwa kowa magana, bata cewa a fita yawo yanzu ko music bana gani tana sawa , idan nace ta shirya mu fita yawo sai tace No�, ‘karamun murmushin Eshaal tayi mata � Fanan nima bansan meke damun taba , tun ran Thursday take a haka , ko abinci bata ci sai taji yunwa ta isheta , duk lokacin da zan farka sai injita tana kuka , i try to asked her but tace mun bakomai �, shiru sukai gabaki d’ayan su , fanan zata kuma magana teacher ya shigo class d’in, fasa fad’an abunda take so ta fad’a tayi tare da komawa seat d’inta . Har teachers suka shigo suka fita Baby bata cewa kowa komai ba , itama Eshaal time to time tana kallan Baby, haka kawai taji bata san ganin ta cikin wannan mood d’in, ta fi san ganin ta a ‘yar rigimarta.
A na fita break yawan ci class suka fice kamar had’in baki yayi saura su hud’u , Abla , Fanan, Eshaal, sai Baby da ta sunkuyar da kanta . Kamar zasu wuce sai Eshaal ta nufi inda take , cikin taushin murya ta furta “Baby ?� Shiru Baby tayi mata batare da ta amsa ba , a karo na biyu Eshaal ta ‘kara furta � Baby?� Uhm kawai Baby tace mata � Me zaki ce na taho miki dashi ?� Cewar Eshaal , a hankali Baby ta furta � Nothing Just go � kallan juna Fanan da Eshaal sukai , sabida basu ta’ba ganin Baby cikin wannan condition d’in ba , alama Fanan tayi wa Abla ko zata yi mata magana , kanta ta jinjina mata gabaki d’aya suka dawo seat d’in , a hankali Abla ta furta � Baby ?� ‘Karamun tsaki Baby tayi zata tashi tabar wajan Abla ta dawo da ita , ta bud’e baki zata yi magana itama Abla cikin fad’a fad’a ta furta � shout up , me ke damun kine ?Tun d’azu ana so ayi miki magana kina yi wa mutane wula…� bata ‘karasa ba Baby ta fashe da kuka tana rufe face d’in ta , gabaki d’aya jikin sune yayi sanyi ganin yadda take kuka, cikin sanyin murya Abla ta furta � kiyi hakuri banayi haka dan kiji haushi naba �, kukan face d’in ta Baby ta shara tana kallan su da itanuwanta da sukayi jajawur har sun fara kunbura sabida kukan da tayi , a hankali ta furta � Ni ba kuyi mun komai ba , just go and leave me alone �, hannunta Abla ta kama cikin tausasa murya � kinsan me ? � cewar Abla, girgiza mata kai Baby tayi tana ‘kara share hawayenta , ya’ke kad’an Abla tayi sabida abunda zata fad’a � Nima ina da Sister kamar ki , Sunan ta Arwa � sai kuma tayi shiru , gabaki d’aya idanuwa suka zuba mata , a hankali ta furta � itama batajin magana kamar , ko me yake damun ta bazata bud’e baki tayi magana ba sai dai tayi ta kuka , tun ina lallashin ta, har na soma yi mata fad’a , amma kin san ita tana da sau’kin kai bakamar keba , idan na tanbayeta abu tana fad’a mun, kema ko bazaki fad’awa kowa damuwar ki ba , ki dunga ro’kan Allah ya sassauta miki abunda ke ranki zaki ji dad’i kinji?� A maimakon Baby ta amsa mata sai jefo mata mata tanbayar � Tana ina ?� Kwalla ce ta so tarar wa Abla cikin sauri ta goge tana ‘kara ‘ka’karo murmudhi akan face d’inta � Ta mutu, Arwa ta mutu , ta tafi ta barni� gabaki d’aya sai suka zuba mata idanuwa cikin su kuwa har da Baby da take goge eyes d’in ta , kamar zatayi kuka ta soma magana � Kusan kwana hud’u kenan ina yin wasu mafarkai, wasu mutane mace da namiji suna ta ambatan sunana , ko wannan su yana mi’ko mun hannu akan na cece sa , gefe d’aya kuma kamar suna mun fad’a , musamman muryar na mijin da yake cewa ni ba yarinyar kirki bace , na canza halina ko kuna babu shi babu ni,bansan ko su wanene ba , amma kusan kullum sai nayi mafarkinsu , duk lokacin da suka mi’komun hannun dan na cece su sai naga wasu irin gizo gizo ba ‘ka’ke , jikin su duk jini suna tunkaro inda nake , kullum nayi mafarkin nan sai nayi kuka musamman yadda gizo gizon suke tsoratar dani sai naji kamar suna inda nake, duk lokacin da na kulle idanuwana muryar mutanan nan nake ji, duk da bansan ko su wanene ba amma sai nake jina jima da zan dauwama a inda suke , ina san ganin su ko sau d’aya ne , zuciya ta tana mun ciwo�, ta ‘karasa tana fashewa wani saban kukan . Wani iri Abla taji cikin zuciyarta ‘kafarta kamar ana mata tafiyar tsutsa , lokaci d’aya mafarkin da tayi itama ya fad’o mata , bata san dalili ba , haka kawai taji zuciyar ta na bugawa , kukan Baby ne yasa ta kawar da nata tunanin, suma face d’in su Eshaal duk ya canza kamar zasuyi kukan , murmushi Abla ta sakar mata , � ki dunga yawai ta addua , mafarki ba gaskiya bane kinji? Duk lokacin da zaki kwanta bacci ki tabbata kinyi Alwala sannan ki saka addua insha Allah zaki dena mafarkin � hawayenta Baby ta share tana jinjina mata kai � Na gode �, zaro ido Eshaal da Fanan sukai ganin yau Baby tana yin godiya , ganin yadda suke kallanta ne yasa ta banka musu harara, gabaki d’aya kuma sai suka saka dariya , seat d’inta Abla ta koma ta d’auko chocolate box d’in ta , � Nasan yanzu za’a dawo class , lets just have this chocolates� Kallan Eshaal, Baby tayi a hankali ta furta � kiyi hakuri!�, a tare gabaki d’aya suka had’a baki Wajan furta � Awwwn..� cike da tsokana Fanan tazo dai dai kan Baby ,� ya Allah idan aljanune suka saka Baby ta shiryu Allah yasa su ‘kara saka ta , ta shiryu idan taki shiryuwa kuma su lakad’a mata duka ,� yanxu ma gabaki d’ayanzu sukai a hankali Baby ta furta � Am sorry Eshaal , duk abubuwan da nayi miki a baya , idan banyi miki ba bana jin dad’i a raina sai inji kamar zan zauce shiyasa bana jin dad’in idan ban miki ba � Murmushi Eshaal tayi mata kafun ta furta � zan yafe miki with just one condition � shiru sukai gabaki d’aya su suna jiran abunda Eshaal zata fad’a � har sai kin nemi yafiyar AMMA�, kanta Baby ta jinjina mata � yes I have that intention�. Ko mintu 3 basu ‘kara ba aka dawo daka break shiyasa kowa ya nufi seat d’insa , a haka teachers suka cigaba da shigowa har zuwa time d’in short break, yanzu ma basu fita ba a class suka zauna su hud’un , yadda suke hira suna dariya kwanin burgewa lokaci zuwa zuwa lokaci sai Baby ta kalli Abla , har Abla ta lura da ita, cikin tsokana tsokana Abla ta furta � Yan mata ko na miki kyau ne ?� Murmushi Baby tayi mata tana girgiza mata kai , batare da damuwa ba ta furta � I just feel having talking to you � sosai Abla ta sakar mata murmushi , � Nima haka , I feel the same way � da haka suka cigaba da hirarsu. Ko da aka tashi sai da Baby tasa Abla ta bata number d’inta , amma Abla tace bata haddace ba, shiyasa Ita Baby ta rubuta mata tare da fad’a mata idan ta koma gida tayi mata magana . A haka suka Abla ta nufi inda su zata sami su Sarah , suma su Fanan sukai mata sallama suka tafi. Bata san dalili ba , she just enjoyed the day with gurls , taji dad’in kasan cewa da su ko ba komai sun rage mata kewa , har ta ‘karasa gida kuma tana Tuna’nın mafarkin Baby.
Tundaga wannan lokaci wani irin ‘kawance ya shiga tsakanin su , ko ina zasuje a school suna tare da juna su hud’u, in basu da school kuma zasu hau group d’in da Fanan ta bud’e musu , sosai wani irin ‘kawance ya ‘kullu a tsakaninsu. Cikin tsawan lokacin nan kuwa gabaki d’aya Abla ta fita har kar Big Boss , ko had’uwa dashi batasan yi shiyasa da ta Daidai lokacin dawowar sa ko shigowarsa gida zata gudu d’akin, sai ya zama kamar wasa ‘buya take dashi, gabaki d’aya duk hanyar da zata had’asu ta toshe ta gabaki d’ayan ta . Har zuwa yanzu kuma a makaranta bata had’uwa da su Bad Boys , tun bayan Alkawarin wula’kanta ta da yace zai yi bata ‘kara ganin su ba , ita gabaki d’aya ta manta dasu ma .
Chapter 137 · 0% Book details