← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 146

Sashe 75

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ya dad’e zaune akan sofa yana operating system d’in gabansa da alama wani aikin yake yi sabida yadda ya bawa abun mahimmanci sosai , sai around 1am ya kashe system d’insa gabaki d’aya ko phone d’insa be d’auka ba ya fito daga cikin d’akin, kamar yadda suka saba shida bobo saida ya nufi part d’in kowa ya duba lifiyarsu kafun ya dawo nashi part d’in, sosai idanuwansa suka soma red baccin da beyi d’azuba ga ciwan kai da yake sosai, 1:30am Daidai lokacin da ya kalli agogon d’akin shiyasa kai tsaye batare da ya zauna ba ya nufi Toilet d’insa , mintuna 10 kacal ne ya fito dashi daga toilet ga hannunsa da face d’insa da take da damshin ruwa alamar alwala yayi, Daidai wata shinfid’ad’d’iyar farar dadduma me laushin gaske ya nufa tare da kabbara sallah, ya jima yana nafilfilun da ya saba har wajan karfe 2:30am na dare , shikad’ai sai faman lumshe idanuwansa yake harya koma kan sofa d’insa yana lumshe eyes d’insa musamman yadda ya jingina da jikin sofan, sai da ya d’auki kusan 5 minutes a haka kafun ya janyo wayarsa da ya ajje kan center yana dannawa , har ‘karfe 4:30am Big boss be kwanta ba sai ma shiryawa da ya sake yi kamar kullum cikin white d’in kaya riga da wando sai ‘bakar sumar gashinsa da take ta d’aukan ’kamshi da ‘kyalli , ta ko ina daddad’an turaransa ne yake tashi had’e da sanyin Ac, tsagar girarsa sosai ta fito a face d’insa musamman yadda girar fuskarsa take a cike , hatta red lips dinsa sosai ya ‘kara turuwa , yadda yake lumshe sexy eyes d’insa sai ya burgeka, phone d’insa kawai ya d’auka yanufi down stairs lokacin da ake kiran sallah , babu kowa a falourn , maida kallansa yayi kan agogon falourn batare da ya zauna ba , bobo ne ya fara fitowa shima sanye da brown din Riga sai black d’in wando da yake jikinsa , fuskarsa cike da murmushi ya furta � Big Boss � shima Big boss face d’insa ya d’ago kad’an tare da lumshe masa sexy eyes d’insa daga nan be ‘kara cewa komai ba , bobo yana zama uncle ya Fito shima hannunsa da d’an ’karamin charbi, shima a Wannan karan Big boss be kulasuba sai d‘an lumshe eyes d’insa da yayi masa , shima uncle cike da tsokana ya lumshe masa nashi idanuwan, bakinsa big boss ya ta’be kad’an yana d’auke kansa , � uncle sannu da fitowa � cewar bobo , amaimakon uncle ya amsa masa sai nuna masa direction d’in Big Boss da yayi cikin ‘kasa ‘kasa da murya ya furta � Yau yan mulkinne suka motsa?”d’an kallan direction din big boss yayi kafin ya saki murmushi kawai , a karo na biyu Big Boss ya ‘kara kallan agogon falourn, ganin an tayar da sallar asuba, sai soma tafiya Prince da little suka ‘karaso wajan cikin sauri sai faman haki little yake yi shikad’an , d’an kallansa big boss yayi kad’an tare da d’auke eyes dinsa ya soma tafiya , suma gabaki d’aya bin bayansa sukai zuwa masallacin cikin gidan .
Ana idar da sallah babu Wanda ya kalla cikinsu ya wuce part d’insa , bin bayansa da kallo little yayi har ya wuce , kamo hannunsa bobo yayi suka soma tafiya ganin yadda mood d’insa ya canza � kafiya neman magana little ,kasan baze kulakaba yanxu, ya gaji ka bari ya huta first �, kansa little ya jinjina masa kafun yayi masa narai narai da ido shigen abunda bobo yayi wa big boss � yaya bobo yau ka bamu Hutu banda training din nan kaji?� Yes please� prince yayi saurin fad’a shima , lokaci d’aya bobo ya saka hannu ya tallemusu ‘keya , � kun shirya yau darata Kenan shiyasa kuka biyoni? Toh babu ruwana kunsan hanyar d’akinsa ai kuje ku fad’a masa� cewar bobo , � Haba yayan mu nakanmu kaga yanxu yaya big boss bacci zaiyi please please yayan mu kaji?� Cewar little , shima prince a hankali ya furta � dan Allah kaji yayan mu rabun ranmu, kaji?� Girgiza musu kai yayi kafun ya furta � okay karku cikani da surutu� little har da wani dariya ya saki kafin ya furta � we promised� suna shiga cikin falourn ko zama basuyi ba suka gudu part d’insu � Allah ya shiryeku� cewar bobo shima ya nufi part d’insa .
Chapter 75 · 0% Book details