← Book details Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 146

Sashe 124

Ibtissam Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Tana sakkowa down stairs ta tarar da Little da Prince har sun shirya mata break fast d’inta , cikin d’an ya’ke Abla ta furta � Yaya prince ina kwana ? Yaya little ina kwana ?� Yadda Little yaga tana magana cikin cool voice ya furta � Bazaki fasa zuwa makarantar nan ba kuwa ? Are you okay ?� Murmushi Abla ta sakar masa kad’an � I can manage , muna da speech yau ne � kansa ya Jin kina mata kamar yace ta hakura sai kuma yayi shiru , dan dole suka sa ta ci abinci duk da yadda tace musu a ‘koshe take , da zasu tafi makaranta ma bata had’u da su Bobo ba , har suka kama hanyar idanuwan ta a rufe suke bata san lokacin da aka ‘karaso ba saida Little ya d’an ta’ba ta , � please nace ki dena damuwar nan kinji ?� Kanta ta jinjina masa yanzu ma , wani black face mask ya mi’ko mata � zaki iya sawa a face din ki in kina so � d’an ‘karamun ajiyar zuciya Abla ta saki ka d’an ko ba komai face mask d’in zai kare mata face d’inta . Kamar kullum waving sukai wa juna suka tayar da motar suka tafi ita kuma ta nufi class d’insu . Tunda ta shigo ake binta da kallo ga wani ‘kus’kus da suke yi suna nunata , wasu zafafan hawaye taji suna ‘ko’karin sakko mata tayi saurin mayar dasu , harta ‘karasa seat d’inta babu Wanda ta kalla , tana zama Eshaal ta ri’ke mata hannunta � kiyi hakuri nasan sharri akai miki amma Allah zai saka miki kinji ?just be you , okay ?� Kanta Abla ta jinjina mata ko bakomai ta samu wadda ta yadda da ita � Nagode � cewar Abla , itama fanan seat dinta tazo , ita da Eshaal suna so ta sake kamar da , amma zazzafan zazza’bin da take ji ya hana tayi magana sai dai ta jinjina musu kai ko kuma ta furta “eh ko ah ah � shine kad’an abunda bakinta yake iya furtawa , gashi ko karatun abunda zatayi a speech bata karanta ba Sabida abunda ya faru da ita jiya. Ba’a d’au 2 minutes ba Baby ta shigo cikin class d’in, Daidai seat din da su Abla suke ta nufa , da Sauri Eshaal ta had’e hannayen ta alamar ro’ko, hararar ta Baby tayi tana kallan Abla, a bazata ta fusge mask d’in Abla cikin Sauri Abla ta sunkuyar da kanta ‘kasa , karo na farko da Baby taji babu dad’i dan anyiwa mutum abu, � ‘boye fuskar ki da kike bashi zai hana mutum ya yadda da abunda aka gani ba , ko ma su wanene sukai miki Haka raunin ki suke so kamar yadda kike ‘ko’karin nuna wa yanzu, bance sai kin yadda da maganganu na ba , kwanda ki fito ki nuna wa ko wana d’an iska daidai kike dashi , ta hakan ne zaki iya kwatar kanki a hannun kowa � tana kai ‘karshen maganarta ta juya , d’an ’karamin murmushi ne ya fitowa Abla ,� Na gode � shine abunda ta iya furtawa Baby , kanta Baby ta jinjina mata kafin ta harari su Eshaal da suka saki baki suna kallanta , sosai suke kallanta da tsantsan mamaki , karo na farko da Baby ta fad’i maganar arziki, shiyasa cikin Sauri fanan ta koma Seat d’inta . Har lokacin kuma ba’a dena gulmar Abla ba , ga zazza’bin da yake ‘ko’karin cin ‘karfin ta , duk yadda Eshaal da fanan sukayi da ita akan suje clinic ta ‘ki yadda. Har 9am suna class babu teacher din da ya shigo sabida speech din da za’ayi na seniors, wani irin fargaba Abla take ji a ‘kasan zuciyar ta ,babu abunda take sai adduar da ta zo bakinta. 9:40am aka bu’kaci duka students suje babban filin hall din da za’ayi program din , duk yadda Eshaal tayi da ita suje Abla ta kasa zuwa , zuciyarta ba dad’i da kyar ta hakura ganin time na tafiya suka nufi hall din , duk Wanda ya ganta sai su fara magana kasa kasa ko su dunga nuna ta , Daidai zasu shiga hall din suka tarar da Mr jabcon a tsaye sai faman murmushi yake wa Abla, a bakin ‘kofar ya tsaya ta yadda dole sai sun ra’bashi tukunna , kallan da yake bun Abla da shine ya ‘kara tunzurata, Daidai zata shiga cikin hall d’in yayi ‘ko’karin rike mata kwankwaso, bata damu da d’aliban da suke wuce ba wa , ta d’aga hannunta da iya karfinta , ta tsinka masa mari, tare da tofa masa miyau tayi wucewar ta . Wannan abunda tayi masa ne ya ‘kara tun zura jabcon, shi kad’ai sai jijjiga kansa yake yana ‘kwafa , wayar sa da ta d’anyi ringing ya d’auka, banyi me aka ce masa ba sai wata shegiyar dariya da ya saki lokacin da yake komawa gefe , � kamar yadda aka shirya plan , komai yana kan shiri nan da ‘yan mintuna kad’an aikin ki zai kammalu kamar yadda kike bu’kata� yanxu ma banji me aka ce masa ba sai wata shegiyar dariya da ya ‘kara saki kafun ya furta � zan turo miki da account din yanzu � sai d’iff ya kashe wayar yana shiga cikin hall d’in.
Chapter 124 · 0% Book details