← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 162

Sashe 95

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Safwan na dawowa gida ya shiga part dinshi , a har gitse ya fito knowing that Inna ta shiga part dinshi, part din Inna ya nufa looking very angry asiya dake zaune falo na hangoshi daga nesa tayi saurin mikewa ta shiga bedroom dinta gabanta na faduwa, banging Kofar yayi ya shiga looking so angry,
"Me ya kaiki bangarena?.." Shine tambayan da yayiwa Inna dake zaune Tana mazurai da idanuwa Don yana shiga duk wannan shirin datayi na in ya dawo zata tambayeshi ya wargaje, kawai ji tayi Tasha jinin jikinta sabida tashin hankali,
"Me ya kaiki bangarena?.." Ya sake tambayan ta looking super duper angry
"Wai...Wai...waya fada maka na shiga bangaren ka?.." Ta tambayeshi sounding so scared kaman ba Dan da ta durkusa ta Haifa bane, wannan love and respect din is gone, sai tsoro da shakka, nunata yayi da yatsa daga inda take zaune yana cewa
"Daga yau sau yau....kar ki kuskura ki Kira shiga bangarena...shiyasa na baki wajen ki daban...wajena daban...in inaso ki shiga inda nake waje daya za samar mana...Don haka ki zauna inda na ajiye ki..." Yafada idanuwanshi rufe ruf Sannna yana nunata da finger kaman zai mareta, yasan in har ya bude idanwau she will definitely run away Don he's so angry and he hates her with passion, Inna dake zaune batasan lokacin da ta fara hawaye ba, she cant believe danta né ke magana haka yana nunata da yatsa kaman zai mareta, daga idanuwa tayi full of tears tace
"Safwan tunda abun ya kawo kazo ka tsaya Kaina Kana yi min ihu bar maka gida zanyi...daman ba kan titi ka dauko ni ba ..." Tafada voice dinta na cracking sabida yanda take hawaye, tsoki safwan yaja yasan she's crying dukda he's eyes are still closed, ,
"Ai Inna nidake mutu ka raba..,duk inda na saka kafa muna tare dake...Wai kin mance Abunda kike cemin?... Kina kirana da sunan matsiyaci...kina cewa kashin talauci gareni kaman mahaifina...kince yanda ubana ya mutu cikin talauci Nima haka zan mutu...sai Yanzu nayi kudi saboda ke kice zaki bar gidan?... Ai you're day dreaming Wallahi...we're in this together...ni dake takalmin kaza ne...babu Mai rabamu sai mutuwa..." Yafada idanuwanshi lumshe amma tears are rolling,
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun...safwan ban fadi hakan Don ka shiga wani mugun Abu saboda arziki ba..." Bata karasa ba yace
"Inna mugun Abu me nayi saboda kudi?.." Ya tambayeta yanason yasan what she knows because he can't open he's eyes to examine her, shuru Inna tayi Tana kuka, shima hawaye yake amma he's face is as strong as ignite rock, asiya na labe Tana sauraron abinda suke cewa,
"Wallahi in baki bar wajen ba sai na ballaki..." Yafada yana daga Kai zuwa bakin Kofar da asiya ke labe, da sauri ta koma baya hannunta kan bakinta sai kuka take, duk yan cult suna da one ability or the other amma na safwan is so clear sabida anger dake cinshi, he's always angry can only pretend to be happy considering the situation amma when ever he looses it bai da kyauwun gani,
"Inna tambayanki nake..nace wane mugun Abu nake ?."ya sake tambayan ta sounding so hot, cikin kuka Inna tace
"Safwan da ganin kudin da ke dakinka ba na halal bane...." Tafada cikin matsanacin kuka, dariya ya saki tare dacewa
"She have the guts to complain, ..Wai ban gane ba na halal bane?..kin taba zaunar Dani kin bani shawara a matsayinki na uwata?...kin taba ce min Dana kar Kayi kaza kar Kayi kaza?.. Sai Yanzu zaki zauna kiyi magana kaman uwar kirki?... Think again.." Inna Kara volume din kukanta tayi Tana cewa
"Safwan ni kake cewa ba uwar kirki ba?.. Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun..."ta fada  cikin matsanacin kuka, baki ya tabe Sannan yace
"Oho..Nidai nace kar ki Kara shi har min part...kuma babu inda zaki...kudi né ke zauna kici ki koshi...kaman yanda kike bukata..ai lokacin da nake kawo kadan baki godewa..tou Yanzu ga Mai yawa nan...eat to your satisfaction...." Yafada yana hawaye, sai lokacin ya bude Ido tare da juyawa
"Safwan...Yanzu kana nufi nice silan fadawanka mugun Abu?.." Tafada cikin wata irin kukan da duk da will not bear to see he's mother crying like that amma safwan ko a jikinshi, bai juyo gareta ba yace
"Kar ki kuskura ki Kara cewa Ina mugun Abu...Nadia fada maki..." Yana kaiwa nan sai ya bar part dinta, nashi part din ya koma sai huci yake zuciyar shi sai kuna take, before he thinks yana da control over he's anger amma he's wrong, he can easily get so furious and when he gets furious sai yaji kaman ya shake mutum kawai,
Har yamma bai Kara fita ba, yana gidan kwace reflecting on he's life, wajen 5:30 yayi wanka ya fita cikin English wears, Dukda he's in bad mood bai manta da 2 million dinshi ba, yana zuwa cikin gari yayi shopping fruits da Kayan ci, ya sayi Kayan da he won't need to go out, wayarshi tayi ringing yana fiddowa yaga wannan matar dazun, tsoki yaja ya maida wayar aljihu ya cigaba da Abunda yake. Yana gamawa ya saka a bayan mota ya nufi gida lokacin duk an gama sallah mgrub.
Chapter 95 · 0% Book details