← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 162

Sashe 85

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mahaifiyar rabia ce. Tsaye Tana salati,
"Wallahi rabia ciki gareta...ciki gareta Wallahi..." Tafada cikin tsananin tashin hankali yayinda rabia Tana durkushe compound rike da wata yar bag Tana amai, yanda take aman tamkar hancjinta zai fita yasa mahaifiyar ta kura mata Ido, daman ta fito compound né da niyyar zuwa hospital a bata poisonous poison ta kashe kanta, Tana fita kamshin abinda ake soyawa kitchen ya sata  sakin amai wajen har mutanen gida suka fito, hannu mom dinta ta Dora akai ta dinga kuka kaman ba gobe, wannan maganar ciki ya kusa kashe alhaji Ibrahim, yasan he's not a good person but he don't deserve this, shi kanshi kuka ya dinga yi a inda yake kwance yana sauraron abinda ake cewa, mahaifiyar rabia kallon ta tayi tace
"Na yafeki duniya da lahira...ki nemi wata uwa bani ba,,," tafada cikin matsanacin kuka wannan maganar yasa rabia mikewa da sauran karfinta tayi waje da gudu Tana kuka, wasu yan unguwar kallonta suke not knowing abinda ya sameta, a daidaita ta tsaida ta hau ta fada mashi sunan hospital da zai kaita, har suka isa bata Diana kuka ba, Tana isa ta bude bag dinta ta biya sai lokacin ta tuna bata dauki wayarta ba, gani take Yanzu she don't even need a phone tunda she's about to die. Cikin kuka ta shiga office din Doctor luckily bai dade da shigowa ba, kallonta yayi yaji ta bashi tausayi he still remembers her saboda daga baya he hates himself for not collecting her number Don yayi contacting dinta yaji ya suka kare da saurayin dayayi mata cikin. Da sauri rabia tayi kneeling gabanshi da idanuwanta da suka koma kaman ba nata ba tace
"Dan Allah..Dan..annabi...ka bani wani..Abu insha in mutu..." Tafada sounding so fed up with life, mikewa yayi tsaye tare dacewa
"Stand up..ki zauna..." Ya umarceta kaman zaiyi kuka, most doctors basu da tausayi amma wannan is nice, idanuwanshi sun sauya kaman ba that guy with pure white eyes ba, cikin kuka ta girgiza mashi Kai,
"Aa Dan Allah..,kawai ka taimaki rayuwata...uwata ta tsine min...nayi sanadiyar cutar da ubana..I have nothing to live for anymore..." Tafada cikin kuka,
"Just seat down..." Yafada mata calmly, ahankali ta Mike ta zauna
"Pls kiyi shuru..kome ya samu bawa rubuce yake..now tell me have you tell him about the pregnancy?.." Ya tambayeta, cikin kuka ta daga  mashi Kai,
"Me yace,,."
"He said..in zubda,,,kar in kara yi mashi maganar cikin..." Ta amsa mashi atakaice still crying,
"Oh god...now fadamin...what's the story behind your relationship dashi..." Doctor ya tambayeta, cikin kuka ta fada mashi yanda suka hadu da safwan da yanda ya yaudareta ta gano mom dinshi da sauran su, babu abinda Doctor keyi sai girgiza Kai, he's so sad about the innocent girls story,
"Kiyi shuru pls..." Yafada cikin sanyinmurya, rabia batayi shuru ba ta cigaba da kukan ta,
"Ki dauki abinda ya same ki as kaddara..,you're a good person and Allah will see you through...bazaki zubar da cikin ba...Sannan you won't commit suicide...everything will be alright..." Yafada kaman yana magana da kanwarshi,
"aa..so nake in mutu..,am hopeless..." Bai Bari ta karasa ba yace
"You're not...you're a good person...kinyi laifi kuma kinsan kinyi so you're not hopeless...naga yanmata da dama da zasu zo suna cin chewing gum zasuce Doctor pls abortion zaka yi min...kinga basuyi nadama ba..amma ke kinyi daman..and  Insha Allah komai zai wuce..." Kallonshi rabia ta dingayi Tana hawaye, sai da ya gama tace
"Nawa ya kare..,I don't want to live anymore...bani da kowa Yanzu...kawai mutuwa nakeso..., tafada mashi cikin kuka,
"Listen ko baki da kowa you have me...ban taba Jin inason taimaka kowa kaman ke ba...they're somethings that is bad but feels good..Don haka zan taimaka maki..zan baki shelter...zan baki food har Allah ya raba ki da Abunda ke cikin ki lafiya..." Rabia girgiza Kai ta dingayi Tana ganin is another way to use her,
"Aa.,banaso...kawai I want to die..." Ta fada mashi,
"Am serious...I will help you..." Yafada calmly,
"aa Nidai ban so...banason taimakon namiji..namiji have ruin me...kawai mutuwa nakeso... "
"Listen ni ba mugu bane..kawai nasan in har na barki and you harm yourself Allah will not forgive me because Ina da daman taimakawa amma naki..Don haka Allah kadai yasan dalilin komai...da akwai hospital da dama a cikin gari amma Allah ya kawo ki nan Sannan ni kuma cikin duk patients da nakeyi banga wacce ta bani tausayi kaman ke ba..nasan in har Allah ya bani ikon kula dake har kika haihu ba karamin lada zan samu ba..Sannan zan roki Allah ya Kai ladan ga mahaifiyata data rigani gidan gaskiya...Don haka pls give me the chance to do this...I really want to do it...ban taba Jin Ina shaawar yin Abu kaman wannan ba" ya fada mata, rabia hada Kai tayi da table din gabanta Tana kuka, she's so speechless sabida he sounds so truthful, maganar da yayi yasa ta danji sauki cikin ranta, bayan kaman minti daya tace
"But Ai gidanku bazaa yarda ka zauna Dani ba.." Bata karasa ba yace
"Don't worry about that..ba gidan mu zan kaiki ba....Ina da gida inda in Allah ya yarda zan zauna da iyalaina...chan zan kaiki...In Allah ya yarda kafin a Kai kudin néman aurena a sa biki ayi komai kin haihu..."
"In na haihu what will happen to me...kan titi zan koma da abinda na haifa?.." Ta tambayeshi still crying,
"Don't worry about that.?.insha Allah they will be a way out of it..." Ya fada mata Sannan ya Kara dacewa
"Sunana Doctor salim bello ...nice meeting you...,rabia..." Yafada yana wearing a smile.
"Yanzu dai zansa a kawo maki abinci...Sannan zanje kasuwa in San sayi wasu abubuwan da zaki bukata...babu Halin inje dake sabida dad Dina zai iya samun labari...Don haka ki shiga nan ciki..da akwai resting chair ki kwanta ki huta kafin a kawo maki abunci...ba Lallai in dawo da wuri ba saboda my dad called me to meet him..Don haka just relax, if you need anything ask the receptionist..." Yafada mata sounding so friendly, zama tayi Tana kallonshi da yanda yake magana, sai taji ya burgeta, duk yanda mutanen cikin duniya ta lalace da akwai few people with the heart of daimond, they want to shine in the life of others, Doctor salim is the first son of Alhaji bello mahaifiyar shi was the first wife na alhaji bello who lost her life during giving birth to him, shi kadai mahaifiyar shi ta haifa, bayan rasuwarta aka auro mahaifiyar su mufida wacce ta kula dashi tamkar ita ta haifeshi, in ba Wanda yasan family din sosai ba you won't know ba ita ta haifeshi ba, yana da aure da yaranshi biyu, he's like he's father when it comes to he's generosity, daman a lion never begets a sheep, yanda halin ubanshi yake shima haka yake. Lokacin da yaga rabia for the first time she reminds him of mufida, saboda kusan age dinsu daya, kawai he pitied her so much that he promised himself if har Allah ya kaddara zai taimaka mata she will sure come back and when she does he's going to help her, it's an act of charity for him and luckily she came back, yana da gidaje da yawa a cikin garin Kano and have decided ya bata daya ta zauna har ranar da Allah yasa tayi aure, dalilin dayasa ya fada mata he's not married is Don ta samu kwanciyar hankali. Ya rabbi ka bawa duk Mai Hali yiwa na kasa dashi. Because shine na chan, life is vanity upon vanity, (I love you so much my anty...your generosity yafi na kowa that I have ever come across. Allah ya baki ikon ida nufinki akan masu karfin Hali..."

Inna kam tunda taga wannan abun mamaki ta dinga aduar gari ya waye Don ta tari safwan da wannan maganar, amma the following day tun da asuba karar fit an da mota ya tashesu, wannan abun ya yiwa Inna ciwo sosai, kawai gani take safwan ya gama rainata,
"Fasikanci fa...a gabana safwan yake kawo mace ...suyi fasikanci..Kai wannan yaron da abun mamaki yake.." Tafada cike da Jin haushi, asiya kam bata cewa komai sai tunanin Abunda yasa safwan ya Chanza haka kawai take, Tasan ko kadan safwan ba haka yake ba duk Wanda yasan safwan yasan he has Changed so much, he's change is everywhere saboda attitude dinshi da komai ya sauya, ko kadan ba'a taba tunanin safwan zai iya kawo matar banza har gida Don lokacin in ya samu kudi zaiyi masu Kayan sallah bai yarda ayi masu dinki Mai matse jiki Sannan bai yarda su saka gyale, ko cikin gida Bai Bari su zauna babu dankwali amma yau wannan safwan din né Mai dauko matar banza har cikin gidanshi.
"Inna lillahi wa'ina ilaihi rajiun.?.! Ta fada Tana sakin ajiyan zuciya., Inna kallon ta tayi taja tsoki tare da kauda Kai
"Inna yaya safwan yana bukatar adua...Inna mu tashi tsaye muyi mashi adua..." Tafada hawaye na fita daga idonta, harara Inna ta watsa  mata Tana cewa
"Kina ganin mutum ya zAma dan iska kina maganar adua?.. Kin Taba ganin inda adua ya sauya halin mutum?.. " Bata karasa ba asiya tace
"Eh Inna..babu abinda adua bai sauyawa?...kawai muyi mashi adua...nasan komai zaiyi daidai..." Tafada Tana kuka,
"Allah dai ya maidashi lafiya...zai gane Ai.." Tafada atakaice.
Chapter 85 · 0% Book details