← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 142 OF 162

Sashe 142

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Idanuwan Mamanmu waje tana kallon habib, already idanuwan habib dake shigowa gidan sun ciko da hawaye, yana tafiya a hankali zuwa wajen mamanmu dake dukawa tana ajiye yaron dake hannunta, duk su fatina da sisters din habib dake compound basu gane habib ne ba saboda change dake tattare dashi yayi yawa, babu Mai taba cewa wannan slim habib ne tsaye haka har da Dan tumbi da silky skin,
"modibbo... "shine abinda ya fita daga bakin mamanmu, duk zaro idanuwa sukayi suna kallonshi,
"mamanmu... "yafada yana fashewa da kuka sannan yana fadawa jikinta, haba before you know it duk sisters dinshi sun fada jikinshi kaman zasu kadashi tare da mamanmu da yake rike dashi, har lokacin mamanmu b'ata dawo daidai ba, idanuwanta waje tana kallon habib, ta kalli hannun shi ta kalli jikinshi, she's looking so surprised, habib MA kallonta yake yana murmushi amma yana hawaye, Fatima kasa tashi tayi daga inda take zaune saboda wannan bai Kama da yaya modibbo, wannan yafi karfin ajinta, he looks so hot and classy,
"mamanmu... "ya sake fad'a yana kallon mamanmu da ta kasa daidaita idanuwanta tare da rufe bakin ka,
"kaine modibbo... "tafada voice dinta na rawa, da sauri ya daga mata Kai,
'"nine habib dinki... Nine mamanmu.. Danki ne... "yafada idanuwanshi dauke da hawaye bakinshi kuma dauke da murmushi,
"habib kaine Dan Allah ko mafarji nake... "ta fad'a cike da shock, da sauri yake daga mata kai yana cewa
"Mamanmu nine... "yafada hawaye cike a idonshi, mamanmu dafa chest dinta tayi ta kuma saurin maida hannunta kan habib, habib bai kallon kowa sai mahaifiyar shi, he wonders ya akayi ya zauna babu ita all this while, yasan she have been through a lot because he's her backbone,
"ban San zan tardaki Ba... Mamanmu bansan zan sake ganinka ba..."yafada cikin kuka, abinka da matAn kauye da gudu fatima ta shiga daki saboda fargaban ganin masoyinta, kafin kace me gidan ya cika da mutane wayanda sukaji habibu daya haukace ya dawo da katuwar mota, abban fatima was as shock as mamanmu Don tsaye yayi ya harde hannu a chest dinshi, sisters dinshi chukuikuyeshi sukayi har kayan dake jikinshi sukayi dirty, abban Fatima Kama mashi hannu yayi ya fita dashi waje mamanmu kam har lokacin kaman ba habib take kallo ba, bin bayansu tayi tana lekawa Don dai ta tabbatar shine, motar dake tsaye ta kalla taga wani zaune a gaba, komawa ciki tayi duk ta rasa inda zata saka kanta, sujud tayi nan waje ta Kai minti shabiyar kan ta kasa, babu abinda take fadawa Allah sai yaba mashi da gode mashi daya maido mata danta in one piece, little habib kam sai wasan shi kawai yake baj wani damu da abunda ke faruwa, Fatima na shigewa daki ta fashe da kuka, Allah kadai yasan yanda take ji, she's so happy that tears of joy flows freely. Habib na waje yana bawa maza da suka taru tare da abban Fatima labarin abinda ya faru, bai wani San while he was mad ba amma ya basu labarin da alhaji bello ya bashi lokacin da ya bugeshi, da kuma sauran labarin yanda akayi ya Kai inda yake yanzu, wasu har da kuka jin labarin shi, ko kadan bai fad'a masu dalilin haukacewar shi ba, at least he's friends might be involved. Ya kusa hour guda waje sannan ya shiga ciki, dakin mamanmu dake zaune gefe daya yashiga, kusa daita ya zauna itama tace ya bashi labarin abubuwan da suka faru har isuwa yau, zai bude baki yayi magana little gabi yashigo, kallon mamaki habib yayi mashi, he was thinking kilan kanwarshi daya tayi aure ta haifi da Mai kaman dashi bayan rabuwar su, Don yaga the little him a idon yaron,
"mamanmu.... Wannan yaronfa.." ya tanbayeta looking at the adorable child daya haye kafar mamanmu, murmushi mamanmu ta saki sannan tace
"danka ne... "idanuwa habib ya zaro not believing he's ears a
Kallon yaron dake kafar mamanmu yayi yace
"mamanmu dana ne?.. "ya tambayeta voice dinshi na cracking, dariya mamanmu tayi idanuwanta cike da kwalla, yaron kam ko a jikinshi yana zaune kan kafar mamanmu sai wasa yake da wata har baby dake hannunshi, hannu habib ya mika mashi sai ta makale mashi kafada alaman bai zuwa, habib bai iya furta irin dadin dayake ji, kawai he's feeling something That all he's life bai taba jin irin shi ba, gani yake he's fulfilled, total satisfaction is what he's getting, hannun yaron ya Kama yaro ya zame ya kama Mamanmu gam kaman zaa tafi dashi,
"mamanmu nine Mai da?.. "ya fad'a hawaye na sake gangaro mashi, murmushi kawai mamanmu take,
"mamanmu ina Zara... "ya tambayeta
"tana dakinta.. "bai bari ta gama magana ba ya Mike da sauri yana cewa
"mamanmu yi hakuri.. Bari in dawo... "yafada yana ficewa daga dakin, dariya mamanmu tayi cike fa farinciki mara misaltuwa,
"abban ne... "tafadawa yaron dake hannunta, shuru yayi yana kallon bakinta. Kaman walkiya habib ya shiga dakin, fatima najin ya bude curtains tayi saurin rufe face dinta, tsayawa yayi yana kallon dakin, nothing changed, Just like yesterday,
"habibty... "ya kirata cikin lafazi Mai faranta ran Mai sauraro,
" habibty na...nayi kewarki.... "yafada yana takowa zuwa gabanta, hannunta dake kan face dinta ya rike ya cirosu ya ga face dinta sharkaf da hawaye, dagata sama yayi yana jujjuyawa daita, sai fad'a mata how much he loved and miss her kawai yake, sannan yana mata godiya haifar mashi da,
"amaryata.... "ya rada mata a kunnenta tayi saurin boye face dinta
"daman ban moreki ba... "ya sake rada mata yana kissing wuyanta,
"yanzu sabuwar rayuwa zamu fara... Ni dake... "yafada mata in a very horny voice,
"ki shirya da yamma zamu tafi cikin brini... "ya fad'a mata. Sunfi minti talatin tare sannan ya fita ya koma wajen mamanmu, already ta fito ta hura wuta ta dora mashi abinci, kusa da inda take tana zuba Maggi atukunya yazo ya samu wata yar karamar kujera ya zauna nan kusa daita ya fara b'ata labarin abinda ya faru tun haduwarsu da Mai saa, mamanmu na dafa abinci tana sauraron shi, har bai boye mata komai ba, kirji mamanmu ta dafa cikin tashin hankali tace
"modibbo ranar da safwan ya zo nan.. Kallon daya nayi mashi naji tsigar jikina na tashi... Inna lillahi waina ilaihi rajiun... "tafada cikin hawaye
"mamanmu da yazo Kinga alaman kudi tattare dashi?,, " habib ya tambayeta saboda he's dying to hear how life have been with them, kawai baison yaji ance sun shiga, dukda he sees the domination in them lokacin da aka basu wannan abun suka sha, sannan the last time daya gansu is at the hotel inda suka sauka a anambra. Cikin kuka mamanmu tace
"lokacin daya zo.. Duk. Ya sauya... Kaman bashi ba... Har tsoro ya bani dukda ban San takamemmen abinda yake yi ba... Kallo daya nayi mashi naga tsigan jikina ya tashi...kudi ya dauko Mai uban yawa ya bamu.. Amma cikin ikon Allah bamu amsa ba"tafada cikin matsanacin kuka, shima habib kuka Kawai yake, wani irin bakin ciki yake ji har cikin zuciyar shi
"Mamanmu Mai saa ya cutar damu... Adua ce kawai ya kubuta Dani... Yanzu ban San ya zanyi da zancensu safwan da usman ba... "yafada yana kuka kawai he's thinking he's childhood friends sun zama masu cin naman mutane,
"modibbo shiriya ta ce.. Duk Wanda Allah ya shirya ya shiryu.. Duk kuma Wanda Allah yasa ta tabe babu Mai kubutar dashi... Kawai adua zakayi masu amma Sam ban yafe kaje inda suke ba... Nasan in na San kana rayu suna iya kokarin kasheka.. Irin wannan mutanen basu barin duk Wanda yasan sirrinsu da rai... Dan Allah ka fita harkarsu... Tsakanin dasu adua kawai zakayi masu.. In suna da rabon shiriya Allah yasa su dawo Kan hanya maidaidaiciya... "mamanmu tafada tana hawaye, kuka sosai habib yake,
"Allah yaisa Mai saa... Allah ya hadaka da balain duniya da lahira... Yanzu mamanmu babu taimakon da zaayi masu?..haka zan dane hannuna in bar abokaina su tabe?.. "yafada crying very loud, he can't believe this is happening, he can't believe shi yayi arzikita hanyar halal amma abokan shi sunyi ta hanyar Haram,
"tsakaninka dasu sai adua.. Shi kadai zaka dingayi masu... Ka dinga yi masu sadaka..amma gaskiya ban yarda kaje kusa da inda kake ba... Kanaganin so sukayi ka mutu amma Allah ya tsareka.. Nasan ko zuwan da safwan yayi gidan nan Don su San halin da kake ciki ne... Kawai ka fita harkarsu... Wayan nan yanzu ba abokanka da ka sani bane su.. "mamanmu tafada feeling so hurt from the inside Don dukkansu yaran data rainane, yanda ta San yarantar danta haka ta San nasu. Habib kam kukan da yake ya kasu kashi kashi yana kukan farin cikin dawowa cikin family sannan yana kukan rabuwa da abokanshi, bayan yasha kuka ya gaji ya daga weak eyes dinshi ya kalli mamanmu tare dacewa
"mamanmu... Ku shirya zuwa da yamma mu bar garin nan... Gidan dana fad'a maki an bani... Yana da girma sosai... Duk mu koma ciki... "yafada mata, ahankali ta girgiza mashi Kai tare dacewa
"tunda Allah yasa ka dawo garemu lafiya modibbo ka dauki matarka kuje kuyi zaman aure yanda ya kamata... Yarinyar tayi hakuri sosai.. Tunda habibullah ya Kai wata biyar ake zuwa neman aurenta amma ko sauraronsu batayi...ni kaina dana gaji sai na nace tayi aure Taki.. Don haka ka tafi daita ita kadai mu muna nan..."
"haba Mamanmu.. Ya zaayi in barki nan...nidai gaskiya gabaki dayan mu mutafi birni... Kinga wajen da girma sosai Don dakuna sunfi goma... "bai k'arasa ba tace
"aa... Bazan iya zama da sirikata gida daya ba saboda gudun bacin rana... "da sauri yace
"amma mamanmu AI nan MA tare muke dake... "
"saboda kauye ne.. Sannan kusan kowa na nan haka suke zaune da surukansu...Don haka ka tafi da fatima saidai zaku barmin habibullah... "tafada mashi,
"mamanmu ban iya barinki nan garin... Kawai zan samu wani gidan a gari sai ku zauna...amma gaskiya ban iya barinku kauye in tafi birni ku Kuna nan.. Bayan duk wahala da kukasha bayan rabuwarmu..ko Fatima ban tafiya daita sai na sama maku inda zaku zauna... "Kai mamanmu ta girgiza mashi sannan tace
"bamu sha wahala ba... "nan ta bashi labarin yanda suka dinga managing da rayuwar su ta kara dacewa
"ka tafi daita... Kar kayi tunanin raina zai baci...da akwai hakkin ta a kanka..tunda Allah yasa ka dawo lafiya garemu sai ka dauki matarka ku tafi.. Ko kadan kar ka samu damuwa Don wannan kauyen ya zame mana gida... "mamanmu tafada mashi, shuru yayi for a moment sannan yace
"mamanmu fatima ta haihu da kanta nan gida ko asibiti,.. "nan ta fad'a mashi irin wahalal data sha, yana jin ance aiki akayi mata ya Dan saki murmushi already he's thinking dirty abinka da Wanda ya dade babu mace. Yana zaune a gindin murhu har mamanmu ta gama dafa abinci, cikin kwano aka zuba aka kaiwa driver dake kwance bayan mota. Habib abinci yaci sosai because he misses the food of he's mother, suna tare har sukayi magrub, da kyar mamanmu tayi forcing habib ya tafi da Fatima, Don he meant what he said na cewa bai tafiya da fatima sai ya sama masu inda zasu zauna sannan ya tafi da fatima amma Ganin mamanmu Taki yarda dole ya tafi daita Don kar tayi fushi dashi. Da kuka fatima tashiga mota kaman wata amarya ba komai takewa tsoro ba sai wannan azaba datasha a darensu na farko, suna zuwa cikin birni wajen karfe goma na dare yasa driver ya tsaya a wani meat joint ya saya da abun sha sannan yasa driver ya kaisu gidanshi, daman da akwai maigadi da alhaji bello yasa akayi hiring wai Don kar ayi sata gidan tunda an zuba kaya kuma babu kowa, hannunshi cikin nata suka shiga ciki, fatima kasa boye kauyancinta tayi saboda abubuwan rayuwa data gani. The rest of the night was full of pleasure for habib and agony for fatima Don ko na farkon batasha azaba irin wannan ba, it's like opening something new all over again,.
Chapter 142 · 0% Book details