← Book details Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 143 OF 162

Sashe 143

Sirrin Wasu Gayun Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Mufida kam tun safe alhaji ya fada mata da mahaifiyar ta habib ya tuna da rayuwar shi, har da mata, kuka kawai ya rage batayi ba but she was dying, saida mahaifin ta yafita ta tashi ta shiga ciki ta dinga kuka saboda bakin ciki, for the First time she wanted something and could not have it, kome take so tana samu amma this once she loved something she could not have and it hurts her badly.

Dr yana fita ya kama hanyar gidansu rabia da yaran, babu abinda kakeji sai gwarancinsu da suke bayan mota, bayan sun isa Unguwar Dr yayi parking kofar gidansu rabia ya fito ya dauki yara biyu sai. Mai raino ya dauki sauran biyu suka shiga gidan, yau the gate is opened Don haka basu tsaya knocking ba, compound din babu kowa sai wasu yara biyu, sallama Dr yyi da karfi suka fito, wannan yaran da suka gani yasa duk sukayi tsaye baki bude suna kallon ikon Allah, ajiye su Dr yayi ya umarci nanny ta ajiye na hannunsu ta ajiyesu sannan yafara cewa
"sunana Dr salim bello... Shekara kusan biyu da suka wuce wata yarinya tazo asibiti na neman maganin da zata kashe kanta da abinda ke cikinta saboda bakincikin abinda ta aikata... Yanda wannan yarinyar ta nuna nadama ga abinda ta aikata yasa na bata wajen zama maimakon in bari ta kashe kanta, Wanda ya haliccemu ma yana kaunar Wanda yayi laifi ya nuna nadamansa. ..."dan tsayawa yayi tare da sakin dan murmushi yana kallon Muhammad daya dauki wata yar Leda daga kasa yana wasa daita kasancewan yanzu gidan ba kaman da ba, daman da Mai gida ko Mai arziki ya mutu komai nasa sai ya watse so use your wealth wisely Don mutuwa bata knocking, in kayi abinda Kai kadai zakayi benefiting when you die even those that hate you in the family will still try to claim some of your wealth.
"ku kalli wannan halittun.. Kuna ganin da akwai Wanda yaisa hana wannan yaran zuwa duniya ko ta halin kaka ne?..."Dr yayi adding, duk shuru sukayi mahaifiyar rabia ta fashe da Silent cry Wanda bai da kara sai hawaye.
"wane irin hukunci kuke ganin zaayi maku da ita inhar tayi nasara kashe yaran nan... Ku dauki abinda ya samu rabia as kaddara Don kowa MA yana iya fadawa kuma yanda muka dauki kaddara shows how Strong our iman is... Na dade ina aikin likita kuma naga mutane da dama amma ban taba ganin Wanda ya shiga tashin hankali kaman rabia ba...har yau bata bar kukan abinda ya sameta ba.... Kaddara ce ta riga fata.. Dan Allah koda kuwa bazaku amshi rabia ta zauna gidan nan ba ku yafe mata... Kuyi hakuri da abinda ya fada mata... " Dr ya k'arasa maganar cikin sanyimurya, kuka sosai mahaifiyar ta da duk wata babba na cikin gidan suke, yan yaran gidan kam har sun fara wasa da yaran,
"Inna lillahi waina ilaihi rajiun... "mahaifiyar rabia ta fad'a cikin matsanacin kuka, dukawa tayi ta dauki daya daga cikin healthy children din tana kallon beautiful face dinta, tasan tayi Babban kuskure da bata duba kaddara ba har ta dinga yi mata baki, tana tsine mata, kallon yarinyar hannunta dake kaman ita tayi molding kanta kawai take, tasan ko yaya yaro yazo duniya indai mutum Mai hankali ne he or she shouldn't discriminate, Don kaddara na iya fadawa kowa,
"yanzu rabia ta haifi wannan yaran?.."wata matar ubansu tafad'a cikin kuka itama, cikin murmushi Dr yace
"aiki akayi nata aka fiddo su biyar sai daya ya koma... "Dr ya amsa mata sounding so happy and excited, he feels so fulfilled,
"yanzu Kai kadai kayi wahala daita har ta haihu?.."wata ta sake tanbayan shi,
"aa.. Da akwai masu kula daita... "ya sake amsawa,
"Allah ya biyaka... Allah ya saka maka da alkhairi... Lallai mu mun nuna karancin imaninmu da muka tura namu waje.. A wannan zamanin ma duk laifin da ya zatayi baa bari kunne biyu suji balle ayi surutu.. Iyaye boyewa suke amma mu bamuyi hakan ba rabon zaku hadu da rabia... Allah kadai yasan dalilin hadaku amma bamu da bakin gode maka saidai muce Allah yayi maka fiye da yanda kayi mana... Kacewa rabia duk mun yafe mata ta dawo gida... " babban matar mahaifin ta ta k'arasa jawabin ta, idanuwanshi ya lumshe tare da sakin ajiyan zuciya, mahaifiyar rabia ko magana bata iyayi saboda kuka, ta rasa yanda zatayi daina kuka amma thinking that her daughter ta dauki cikin yan biyar babu dangin uwa balle na uba da zasu kula daita makes her want to cry from morning to night, kawai tana tunanin ya wahalal cikin da daya yake balle yara hudu. Durkusawa Dr yayi yana masu godiya kaman shine yayi laifi aka yafe mashi, yaran biyu ya dauka wata yarinya cikin kannen rabia tayi saurin cewa
"Dan Allah ka bar mana su... Sai anty ta taho kawai... "murmushi Dr ya saki before saying
"gaskiya kuyi hakuri... Basu shirya zuwa ba tukun... Zan maidosu tare da mahaifiyar su... Bayan sunyi wa alhaji sallama... "
"wane alhji kuma... "wata ta tanbayeshi,
"mahaifina.. Alhaji bello tanimu... "jin sunan Wanda aka kira yasa duk suka zaro idanuwa, they can believe they're together with the son of prominent man in kano State,

Thanks57💚💛💜🧡❤
Sirrin wasu gayun
💚💜🧡💛❤💙

®Zuwairat (ummumaryam)

5⃣7⃣

Duk baki suka bude suna kallon shi saboda sunan wanda ya kira as he's biological father, babu Wanda bai San bello tanimu ba inda asalin Dan kano ne,  kowa suna jin sunan saboda yanda yakeyi da taimakon mutane,
"Allah Mai iko... Wannan babban alamari ne...wato ta sanadin rabia zamu hadu da ire iren ku?..muna Jin alkhairi da kukewa mutane amma bamu tabbatar ku mutanen arziki bane sai yau... In ba mutanen arziki ba wa zai amshi yarinyar da tayi cikin shege ya b'ata kulawa da masu yi mata hidima har ta haihu ya cigaba da kulawa da abinda ta haifa?... Lallai wannan kadai yaisa ya nuna mana cewa rabia ba Mai laifi bace... Don duk Mai mugun hali bai haduwa da mutanen arziki sai mutanen banza irinsa... Babu abinda zamu ce maka sai dai muce rabbi ya biyaka..."uwar gjdan alhaji Ibrahim ta fad'a cikin hawaye,  Dr kam har yayi danasanin fada masu koshi waye,  yanda suka zuba mashi ido da kuma yanda suke magana makes him shy,  duk sai adua suke mashi banda mahaifiyar rabia that could not talk because of cry,baby dake hannunta sai kallon ta kawai take tana gwaranci,  yaran suka amsa suka fita,har bakin mota aka raka su ana mashi godiya,  mota ya tada ya bar wajen cike da farinciki, he don't know how he will break this to rabia,  yasan zatayi murna sosai,  he's so happy but in ya tuna da yaran yasan he will miss them sosai as bazai samu ganinsu kaman yanzu ba,  sun zame mashi tamkar other family that he sees during the day and he's family at night,  kawai bai wani abu da rabia but yasan he have feelings for her as in ya tsallake rana daya bai ganta ba kaman yayi wata,  kawai ta zama tamkar real family that he misses her every day, ajiyan zuciya ya saki yana tuki, haka suka isa gidan rabia ta nemi sanin inda suka je yace shan iska ya kaisu.  He wants to tell her inda sukaje amma yana ganin it's late, kuma yana son yafadawa alhaji abinda ke wakana.
Chapter 143 · 0% Book details